🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 07 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Alhaji Isa Abduljalal Zanna da matarshi haj Harira haifaffun garin maiduguri ne, aikine ya kawo su garin katsina da zama. Ummu Rumana wacce aka fi sani da rumaisa itace ya' ta farko, tana aure a garin canada da yayanta hudu sai Abduljalal(Adnan) wanda ke likitan dabbobi wato vetinary doctor, sai Umar dake aikin custom, sai Yuzarsif da Mu'azzañ dake final year da kuma 300lvl dinsu a ABU kasancewar babu wani shekaru tsakaninsu sai Farida dake Ss3 da kuma auta Hanifa wacce ke ss1. Ahmad da ne ga kanwar mami wacce ta rasu ta bar shi shine ta dauko shi ta mayar dashi hanunta a halin yanzu yana primary 5, wanan shine takaitacen tarihin umar. Bai tashi dawowa ba sai bayan sallan mangrib, direct massalaci ya wuce don yasan adnan da daddy duk suna wajen, bayan an idar suka rankayo gida tare. Yana shirin haurawa dakinshi mami ta kwalla mishi kira "sauko nan, yi maza ka sauko kar ka kuskura ka karasa wanan dakin domin nasan muddin ka shiga kai da abinci sai gobe da rana" dukkansu a falon suka soma dariyar shi ya dan hada rai don yau no space for fun a zuciyar shi, tunanin zaliha ya mamaye jini da bargon shi yace "mami ki bari ayi isha mana sai kace wani karamin yaro" "eh din naki na barin, naga alamun baka san ciwon kanka ba, tun da kai baka son kanka ni ina kan sonka so maza sauko tun kafin raina ya baci ka hau kujerar nan ka zauna" ganin ba wasa a fuskarta ta hada fuska tamau shiyasa bai sake musu ba ya wuce straight dining table ya zauna yana gunguni sai kace karamin yaro, dukkansu har abba dariyar dramer dinsu suka dinga yi. Haka sauran suka zo suka sameshi akan table din, farida ta zubawa kowa abunda yake son ci kowa ya soma cin lafiyayen abincin mamin su. Ganin shirun umar yayi yawa sai adnan ya zugure shi da kafa kasancewar tare suke a gefe daya "bro ya akayine kayi shiru haka?" hanifa tace "yaya adnan kenan, ai shi yaya umar a kodayaushe a shiru yake ai, kai kafi kowa sani" Adnan yace "nasani amma shirun nashi na yau yafi na kullum ga abincinshi ma sai wasa da chokali yake ko rabi baiyi ba mu kuma mun kusan kammalawa, ko mami ce?" mamin tace "ai idan ma nice to kuwa ya dinga shiru kenan a dining har ranar da zaiyi aure ya tafi ya bar mun gida don ni nasan ciwon kanshi tunda shi bai sani ba. Alhaji kayi wa yaron nan fada, ni nayi nayi har na gaji abun ya faskara so yake ya janyo wa kanshi cutar ulcer ya sakamu a damuwa bayan dukkanmu anan hatta kai dakake kasuwanci baka dashi" murmushi abban yayi yace "umar kaga yau mami ta kawo kararka rabon da naji hakan tun kanada shekaru shida a duniya so ya kamata ka kikaye wa lafiyar cikinka, don dukkanmu a nan muna sonka bazamu so abunda zai cuce ka ba hope u get me" ya jinjina kanshi"naji abba, zanyi kokarin kiyayewa in shaa Allah, kinji mamina" mamin tace "ahap sau nawa kake mun tuban muzurun" "dagaske mami wanan fa its for real zanyi kokarin faranta miki rai kamar yanda na saba, kinsan ba'a jin kanmu ko mamina" "dadin baki ko? To naji amma ka tabbata ka cinye abincin kwanon nan tass ko kadan kada ka rage sanan na tabbatar da maganar ka, ehe" dukkansu harda shi suka dara yace ''Mami! Mami! Hmmmm" ya karasa sauran a zuciya ''mami rikici''. Saida ya kankare abincin kwanon sanan ta barshi ya tashi daga kan dining din suka wuce massalaci sukayi sallar isha sanan kowa ya wuce shashin shi. Dale gado ya sakeyi ya cigaba labarinshi daga inda ya tsaya..........
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.