🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆. 25 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
A ss2 aka sakani, a cikin lokaci kalilin soyayya ta kullu tsanina da wata yarinya mai suna maryam, hakika na sota, na kaunaceta da dukkan zuciyata harda gangar jikina,hankalinmu baya kwanciya muddin bamu ga juna ba idan nine na dinga sintirin zuwa gidan su muddin kuma itace tarewa takeyi a kofar dakina har lokacin dana dawo. Inda nayi rashin sa'a shine sabbin abokai danayi a wajen domin idan ban manta ba mu biyu ne kadai musulmai sauran duk kabilu ne daga mazan har matan amma nayi kokarin killace kaina har na gama service dina a ranar da mukayi musu bankwana a assembly suma ne kadai maryam batayi ba hankalinta ya kai koluluwar tashi tace ita yar kauye ce ni kuma dan birni kar na tafi na barta da mikin sona a zuciyarta naje na samu wayayyiya yar masu dashi na mance da ita, nayita lallashinta ina kwantar mata da hankali akan maganar aurena da ita babu fashi zan koma ne mu dai daita da mahaifina azo a nema mun aurenta, ko a dakin maigadi ne zan iya tarewa a wajen muddin da da ita zanyi rayuwata dukda ma nafi karfin haka. A daren ranar akayi taror duka youths din suka hada party da rabon kaddara zai afku shiyasa ina zaman zamana a dakina na mike na tafi,bansani ba kaddara ke jana,ashe wasu la'anannun sun druging drinks din da maganin sha'awa ban sani ba na kwankwadi nawa nayi hanyar gida. Da kyar na iya driving na iso gida na tarar da ita a kofar dakina kamar yanda ta saba da dan kwanon abincin data saba kawo mun ta buga tagumi tana jirana. Ganin yanda naketa hada uban zufa gashi lokacin damina ya sawo kai ana samun iska a gombe shiyasa ta sha jinin jikinta tayi saurin taroni "abbakar lafiya kuwa?" innaaa...... Banga ta amshi ba nayi saurin wuceta na bude kofa na fada daki cikin sauri itama ta biyoni.
Wanan shine karon farko data taba shiga cikin dakina domin koda ta kawo abinci bata sameni ba a wajen take bari washe gari ta dawo kwasar kwanuka watakila tayi tunanin kar na tafi ban mata bankwana bane shiyasa ta zauna jirana. Na dinga hada gumi gashi babu wuta bare na kunna fanka na cire kayan jikina na haura kan katifan dakin inata faman musu musu hanayena a tsakanin cinyoyina sai kace mai jin sanyi ji nake kamar zan mutu idan ban aikata abunda kwakwalwata ke faman ayyano mun ba. Ta shigo juyin duniya akan nayi magana amma naki domin niyyata ta gaji kokuma taji haushi ta tafi amma sai ta mike kafa a dakin ta dinga mun kuka tana fifitani da maffici "abubakar dan Allah ka daure ka tashi muje koda chemist din iro ne ka karbi magani kaga abokan aikinka dukkansu basa nan babu wanda zan iya kirawo wa gashi dare yayi" na daka mata tsawa akan ta tashi ta tafi kawai i'll be fyn amma tsawar shi akan ya tsoratata saima ta sake matsowa kusa dani tana taba jikina taji ya dau zafi sautin kukanta ya karu tace "abbakar kayi wa Allah ka mike na taimaka maka zuwa wajen mai magani" cikin nishi sama sama nace "bana bukatan magani a cikin halin da nake ciki kusancinki dani ma kara mun ciwon yakeyi ki taimaka kawai ki tafi kada ki saka ni aikata abunda daga ni har ke zamuyi nadama" har a yanzu ina kallon yanayinta a lokacin, ina kaunarta shiyasa bazan iya mata abunda zuciyata ke ingizani nayi ba amma ya na iya dole ta matsa mun akan na fada mata nikuma na fada mata da tunanin muddin taji zata gudu da kafafunta saboda abun tsorone ga wadanda aka shafa musu fatiha ma bare wadanda are yet to amma sai bata dau shawarata ba a takaice ita ta bani jikinta da kanta a cewarta tanada maganin ciwona bazata zauna tana kallona ina wahala ba. Saida kome ya gama wakana na watsake na fahimci abunda ya faru, nayi kuka har na gode Allah nayi Allah wadar da mugayen abokai saboda su suka ja min amma ita ko a jikinta watakila harda karancin addinin musulunci da take fama dashine ban sani ba saboda nadamar data nuna dan kadanne a tunaninta tunda ta cece masoyinta ta gama komi. Tun daga ranar da abun ya faru har ranar dana bar garin na haramta mata zuwa koda kofar gidana, na tafi da kewarta a cikin zuciyata. Tun dana koma kusan kowanne rana sai na buga wa kawunta waya idan ya dawo daga kasuwa da dare saboda batada waya sai dashi take sadarwa......
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.