Kakkarfar Alaka Part 17

141 10 2
                                    


              🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 17 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Gidan da mama take aiki sai naga ya chanja daga kammaninshi na da ya dawo daban alamun cewa ya daina samun irin kulawar da yake samu a zamanin chan. Nayi parkin na bar jj a mota yana barci na wuce cikin gidan da zumar idan mamana bata ciki nayi U turn izuwa kauye. Na hangota tanata shanyan kaya, a hankali na kira sunanta ta juyo tana kallona peg din hanunta ya fadi a kasan na dauke na makala wa rigan sanan na rungumota dukkan mu muka fasa kuka duk na kewa don rabon mu da juna kusan shekaru tara tun tafiyana kt aiki. Na riko hannayenta duk sun dukunkune saboda azabar aiki, hawaye ya sauko mun a zuciyata nace da yardan Allah tayi bankwana da wanan aiki tace "sodari am, a don na? ashe da rabon zan ganki. Yanzu dai nasan da maganganu a bakin ki saboda haka ki shiga muje ki huta sai muyi" nace "mama dana na mota na a waje bari na dauko shi" na fita na saba shi a kafada, jafar akwai nauyin barci ba laifi idan ya gaji. Tace "idan muka shiga ki basu hakuri kawai akan aurenki anyi shi da gaggawa shiyasa ba'a gaiyyace su ba yanzu kuma mijin ya rasu kina jina ko" na gyada kai sanan muka nufa ciki. Kamar yanda mukayi da mama haka na musu bayani suka mun ta'aziyya sanan muka wuce daki,na kwantar da jj sanan na shigo da sauran kayyakin mu ciki. Nayi wanka nayi sallah na dumama cikina, na wuce kitchen taya mama aiki, a takaice dai sai bayan isha muka samu kanmu da zama har muyi hira. Na bayyana mata kalubalen dana fuskanta a rayuwata, mukayi kukanmu muka share tace Allah na nan kum Allah ya albarkace aunty na Zuhuriyya. Nace "mama na lura gidan nan ya dawo wani kala kala me ya zamu maigidan?" "hmm...... Karayar arziki ne ya sameshi kika gansu haka, hauwa mijinta ne ya sakota saboda kazanta rahiina da yazid kuma babu kudin makaranta buga buga kawai yake fita yi sanan su san nayi" na jinjina kai sanan nace "ikon Allah, kudi me zamaninsa. Allah ya bashi wanda ya fi na da" "amiin". A cikin sati biyu na gama fafutukar neman gida na siya dan madaidaici muka tare dani da dana. A hankali a hankali har na cika gidan da kayyayakin amfani, yayi kyau daidai kudinsa sanan na koma daukan mamana don babu yanda ina ji ina gani zan barta a wahala bayan inada sanadin warakar shi. Muna kan hada kayyyakin ta ta ce mun alhajin na neman aron miliyan hudu don ya kara da sauran kudaden wajensa zai soma wani business dashi kuma yana hangen success ssai a harkan. Na amince zan bashi amma da sharadin zai biyani bayan wata shida ya amince sanan na ara mishi muka wuce da mamana, na samo mata masu aiki har biyu batada abunyi daga barci sai kallo. Kafin wata shida har ya biyani kudina harda extra profit ai kuwa shikenan hanya ta bude mun Allah ya saka ma kudaden albarka, na koma kauye na kwaso kawunai nan na dawo dasu birni kowanne na bashi jarin kanshi banda Abdallah dake zaune damu don na nema mishi jami'a domin shima nce yayi ya soma teaching. Alhmdlh! Allah ya cika mun burina na cire dangina daga kangin talauci mun zamo mawadatta, wannan shine farko da kuma tsakiyan labarin rayuwata babu wanda yasan karshe sai Allah. Na mallaki dukiya da kuma ababen shakatawar rayuwa wato bani da matsala sai na aure saboda bakin fentin dake bibiyar rayuwata. Ina tsoron aure duk da na jarraba sau biyu soyayyar bata kai koinna ba yake watsewa saboda binciken daya zama tilas a addinance kafin kayi aure. Nikan nawa fanni biyu ne, idan ta fannin zamana shegiya ma'ana mara uba bai hanani ba ta fannin haihuwan shege wato ja'afar sai ya kawo cikas shiyasa na yafe na bar wa Allah zabi akaina. Madallah! Ban yarda kowa ya karanta ba saboda sirrinane so be warned!!!!:.............

A nan umar ya ajiye nannauyan ajiyar zuciya ya rungume takardar a kirjin shi yana mai tuno fuskarta a ranar daya hadu da ita, the way she was smilling mutum zai rantse da Allah akan bata taba fuskantar wani kalubale ba a rayuwarta amma wanan takardan ya fayyace komi. Yayi murmushi shi kadai yasan abunda yake ayyanawa a ranshi sanan ya duba agogo karfe biyun dare "lallai na dade ina karatun littafin nan"...

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now