Kakkarfar Alaka Part 13

138 7 0
                                    


🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 13 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Na rasa inda zansa raina ga da'na yunwa na cinshi yanata min ihu don ba ci yayi ssai ba a wajen alhj kasancewar na hanashi ci a wajen baki, ya janyo kayanmu zuwa wajen dakali muka zauna na cire skul bag dinshi daga bayanshi na soma lalube ko zan ga dan biscuit idan ya rage na bashi naji damin kudi a ciki a razane na cirosu, rafar dari biyar biyar ne guda biyu sabbi dal, bakina har rawa yake nace "jj uban wa ya baka wadannan abubuwan cikin jaka?" yana kallon motocin dake wucewa yace "dazu da muke cin abinci ne uncle ya saka mun a ciki" cikin fushi nace "wai ni ban hanaka karban kudi a wajen mutane ba ko kunen kashi ne da kai?" ya juyo yana kallona "mama wlh ce mun yayi sweets ne dana ce mishi akwai nauyi, ai sweets ne ba kudi ba ko ba haka kika ce ba?" naja dogon tsaki kaman na rufe shi da duka amma kodashike ba laifinshi bane tunda yaro ne kuma gaskiyan shi daya ce kudi kadai na hana. Nace "daga yau koda ma dutse ne ba sweet kadai ba koma menene kada ka kuskura ka karba idan ba wai taimako zakayi ba kanajina?" ya gyada kai "mama yi hakuri bazan sake ba" dama bori ne nace "na hakura" amma a raina fa farin ciki nayi don koba komi na samu na kudin mota dana abinci. Tarar mai napep nayi na loda mishi kayan mu sai shagon abincin maman sa'a. Maman sa'a wata dattijuwa ce da muka hadu da ita a wajen siyayyan kayan abinci kasancewar ni hajiya ke yawan aika don gaskiyana da rashi sace sace da bana mata kaman sauran, akwai yarda ssai a tsakanin mu, mun kulla zumunci ssai da ita da yarta wacce bata wuce sa'ata ba don wasu lokutan idan ina free nakan kai masu ziyara mu dan taba hira sanan na dawo bakin aikina. Ta karbe ni hannu biyu bayan na mata bayanin abunda ya faru tace babu damuwa na dawo gidanta da zama na cigaba da mata aiki zata dinga biyana, wanan shine sanadiyyar komawata shagon maman sa'a.


Muna zaune lafiya kalau da ita da yarta sa'a hatta jj saida yafi jin dadin nan da chan saboda yawan kai shi yawo da sa'a ta keyi sanan sun mayar damu more like family rather than a mere house maid sanan har makarantara boko na saka shi mai kudi saisa saisa. Kasancewar kaddarar da namiji na bibiyata shiyasa nan ma saida aka samu mishkila. Wani saurayin sa'a mai suna abdul wanda take mutukar so tunda ya kyallara ido ya ganni shikenan Allah kasheshi wa yake so banda ni, nayi nayi ya rabu dani ama atafur ya nuna bai ma san wanan zancen ba. Ranar wata asabar ina cikin aiki naji kwankwasar kofa, kasancewar langa langa ce ta waje. Na sako hijabina nafito tsakar gida ina cewa waye amma shiru sai na bude kofar na fito, ya jingina da gaban motar ya kura mun ido, ganin shi danayi sai naji wani tukukin bakin ciki ya tokareni a zuci nace "lafiya?" yayi wani mayaudarin murmushi yace "ita ta jawo haka, dama sa'a nazo nema amma tunda na ganki tama zo gidan sauki kamar yanda hausawa sukace faduwa yazo daidai da zama" na harare shi "to sa'a bata nan sunje kasuwa da mamanta sai ka kirata a waya ta sanar da kai lokacin da zata dawo" na juya zan koma sai naji ya janyoni, nayi saurin tunkudeshi ina mayar da numfashi don a rayuwata tun abunda baban amir ya mun na tsani ko tabani ne namiji yayi domin dukkansu kallon mayaudara nake musu. Na bude baki zanyi magana amma sai ya rigani "kajiki don Allah wata cus dake, don kawai mutum yace yana sonki shi zai baki damar yi mishi wulakanci, wai an gaya miki wani kyau ne dake. So nake ki amince mun na chanja miki rayuwarki ki ga so tsantsa" nayi kwafa "lallai kam so tsantsa na tabbata da irin wadanan mayaudaran kalaman kayi amfani wajen shawo kan yar'uwata to saurara kaji da kyau, wlh ina yi wa sa'a so daya tal shiyasa baza'a iya hada baki dani a cuce ta ba. Shin kama san soyayyar da take maka kuwa kake so ka ci amanar ta ribar me zaka ci" yayi tsaki "ni bar mun maganar wanchan dan Allah inada irin ki me zan nema a wajenta,a dama manejin ta nake kan irin ku suzo, naganki sai na kyale?. Gata wata lutiya babu kyaun gani sai kace pumpkin sanan........." ban bari ya kara sa mun wadanan mugayen kalaman ba na dauke shi da kyakyawar mari, yayi saurin dafe kunci don na tabbata marin ta shige shi ssai gashi kuma na mishi bazata, ina shirin kara mishi wani muddin ya cigaba da wadanan kalaman kawai sai ga sa'a da mamanta ashe marin dana waska mishi akan idanunsu, ganin su shiyasa ya hakura amma na tabbata da cewa a zuciyarshi yana da niyyar ramawa.

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now