Kakkarfar Alaka Part 3

190 12 1
                                    


                     🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 03 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆

Cikin sauri ta shigo ta nufi kitchen inda maman take, ya daga murya "keh! Ki tabbata kin dauraye wadannan hannayen nakin tass sanan ki dauko mun abincin, muddin ba haka ba to kuwa zaki cinye shi" mami ta leko "sai shegen kyankyamin tsiya, bazata daurayen ba. Da uban waye ya hanaka ci a lokacin da kowa ke ci, umar so kake ulcer ya kamaka ko?" yana haurawa yace "mami kar ki damu ba ire iren mu ulcer ke kamawa ba so worry not mother" ya haye dakinsa. Yayi wanka ya sauya kayan jikinshi ya hau darduma ya gabatar da sallan azahar,farida ta shigo da sallama ta ajiye tray din abincin akan reading table dinshi ta koma ta ciro goran faro daga fridge din dakinshi da glass cup akan fridge din ta share da towel din dake ninke a gefen ta ajiye mishi sanan tace "yaya ga abincin ka, less i forget ya habib yazo nemanka dazu yace idan ka dawo ka kira shi wai akwai magana mai muhimmanci da zakuyi" "shikenan naji zan kira shi" ya gama ci ya kirawota a land line tazo ta kwashe kwanukan ta fice dasu, sai a lokacin idanun sa suka kai kan takardan daya shigo dasu dazu. Ya dauko shi ya hau kan gado ya jingina da pillow, yana jujjuya takardan a hannu "na bude ko kar na bude? Idan ban bude ba ai bazan sami news din ko ita wacece ba so i just hav 2 saida ta yafe ni" yayi bismillah sanan ya bude first page din ya fara karantawa kaman haka ; Sunana Zaleeha Abubakar Moddibo. Ni haifaffiyar bafulatanar garin gombe ce cikin hukumar dikku, bansan mahaifina ba hasalima a bakin jama'an kauye naji ko wanene shi. A takaice dai ni wata abace wacce jama'a suke kira "shegiya" kasancewar mahaifina tunda ya ma uwata ciki ya gudu ya barta kuma tsoron Allah sai ya hanata cireni ta zabi ta fuskance kalubale daga wajen jama'a akan ta kashe rai ta hadu da tsananin fushin ubangiji. Akwai ranar da na taba tambayarta shin da wa nake kama? Tace komai dina na mahaifina ne kasancewar shima bafulatani ne,tun daga lokacin na tsani fuskata domin bana kaunar duk abunda zai danganta ni dashi, na tsane shi tsana mai tsanani saboda kin auren uwata dayayi yayi mata ciki ya gudu ya barni da fuskantar kyamar jama'a..... Ina rayuwa ne da kakata da ya'anta uku. Baffa sulaiman shine babba don shi yana da mata da ya'ya biyu, shike jan ragamar ci da shan gidan mu, sai mahaifiyata Maryam wacce aka fi sani da mairo, tana aiki a chan cikin birnin gombe a matsayin mai aiki a gidan wani Alhaji mai arziki. Tunda ta haifeni bayan ta yayeni saboda yamadidi da ake da ita ko waec bata rubuta ba ta gudu birni a matsayin mai aiki shiyasa babu wata shakuwa tsakanina da ita, takan zo sau uku ko hudu a shekara shima idan ta samu sarari ne don a cewarta bata kaunar kauyenmu tunda sunanta ya gama baci. Ita take biya mun kudin makaranta da kuma suturar mu daga ni har kawunai na da kakata. Na uku shine kawu Yakubu wanda yake nce dinshi a college sai auta Abdallah, shikam sa'a na ne domin ajinmu daya dashi, shine kawuna abokina sanan yayan don banida kowa sai shi......

Kakkarfar AlakaWhere stories live. Discover now