🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆 15 🎆🎆🎆🎆🎆🎆🎆
Nayi mata sannu da zuwa ta amsa yaran suka gaishe ni na amsa, ta tambayeni bai farfado ba haryanzu nace eh, "wadanan ya'ya na ne, wanan shine babba kamal, sai zahra, khamis da Ahmad, autata sunanta azeeza, ban taho da ita ba na barta da baban su don tayi barci kafin na dawo" nace "gasu kyawawa kaman maman su, sunayen nasu ma masu dadi" sukace sun gode. Muka dan taba hira kadan sai ta mun saida safe, tana fita kamar da awa daya ya farka, na kira likita ya dubashi sanan ya rage gudun ruwan dake jikinshi ya fice. Muka narka abinci mai ji da rai sanan muka kwanta, washe gari sai gasu su duka harda mai gidanta mai suna Alh Tahir, shima din dai jaje ya mun sanan ya hada kan yaran suka koma gida da matar shi, safe rana dare haka aka dinga ka wo mana lafiyayyun abinci, jafar dake jinya tuni ya soma habbaka jiki ballantana ni uwar gayya. A ranar da za'a salamemu a ranar na tuna ashe bamu da wajen zuwa na roketa alfarmar ko me aiki ta daukeni ta tambayeni ina dangina kamar yanda na saba fada haka na gaya mata akan banida kowa fitowa nayi neman abinda zan taimaka wa rayuwata dana yarona amma wanan karon baiyi tasiri ba don ce mun tayi bata yarda ba ni idan banida dangi to yaron fa? Ai baza'a rasa wanda ya sanmu ba. Naga dai babu sarki sai Allah sai na fayyace mata komi, ta tausaya ma rayuwar da muka tsinci kanmu kuma tamun alkawarin zata taimake ni saidai nima nayi mata alkawarin babu cuta ko munafurci tsakanin mu na amince sanan muka wuce gidanta.
Wato nayi rayuwa mai cike da so, kulawa, martabawa , yanci da dai sauran su marasa lissafuwa. Sun kaunace ni tamkar wata kanwar su, babu wanda zai ganni yace ni bare ce, munyi clean n fresh da dana. Aka hadashi da aziza a class daya kasancewar itace sa'ar shi nikuma aka nemar mun admssn a jami'a ko damuwa da tsadar basu mayi ba. A ranar kasa ma magana nayi sai hawaye tsabar farinciki daya cika ni, daba don su ba da na dade da cire rai da jami'a saidai rayuwata ta kare a matsayin matsayin mai aiki.
BAYAN SHEKARU BIYAR
Na gama makarantana da bautar kasa a lokacin kuma jafar ke kokarin kammala rubuta common entrance na fita daga primary. A ranar dana dawo kowa a gidan murna yayita tayani, su zahra aka makalkaleni duk wai sunyi kewata, basuyi karya ba domin nima nayi mugun sabo dasu. A cikin satin aunty zuhuriyya ta soma shirye shiryen small family party din data hada mun na kammala makaranta, nayi nayi ta fasa ta ki wai saboda tanada kudi a kije a banki gwara ta kashe wa marasa shi akan yayi ta zama a cikin acctn doing nothing. Dama yanda mukayi dasu shine muddin danginta suka tambayeni daga ina nace ni yaruwar Alh tahir ne shima idan danginshi suka tambaya na juya zancen shiyasa kowa ke mun kallon yar dangi basu san babu dangantakar iya ba balle na uba. Ranar taro yazo yanuwa da abokan arziki suka zo tayani murna, anci an sha mai kyau sanan na karba gifts dayawa harda mukullin mota wani abokinshi ya bani a matsayin tashi gudumawar. Fadin farincikin dake raina a ranar baya misaltuwa. Na lura da kanwar Alh tahir data saka mun ido, duk inda nake tana nan, fatanta taji ta ina ne na zama yar'uwar zuhura domin shakuwar dake tsakanin su yasa tasan kowanne yaruwarta da ta isheni sai nace daga kauye ne na taho shiyasa bata barni ba. Data ga ban bata gamshashiyar amsa ba sai taje wajen zuhuriyya neman amsa, ta dakatar da ita tace kar ta damu ita da kanta zata zo ta sameta a guest house din su tayi mata bayani dalla dalla, sai ta amince. Washe gari da misalin karfe sha dayan rana ta fito da niyyar tafiya taga hajaran,tayi mun bayanin abunda zan dafa har ina zolayanta. Mun rabu cikin raha da annashuwa domin bana gajiya da zama kusa da ita, a kodayaushe bata da burin daya wuce ta sakani farinciki dani da dana. Da ta iso sai tayi parking a waje ta sauko domin bata zo da niyyar zama ba, ta turo gate din kenan ta hango motar mijinta, cikin mamaki ta karaso amma sanin cewa bai san zata zo ba shiyasa ta fasa bi ta falo ta zagaya ta kofar kitchen domin ta surprising dinsu duka, tana cikin taku na ukun da zai sadata da falon ta jiyo maganganun su saboda kofan daya sada kitchen da falon a bude yake "ina mutukar tausayin zaliha wlh hajara, ga yaronta so young yana bukatar wanda yasan mutumcin su saboda ya maintaining din martaban su n there's no one dat can fit dat space sai ni tahir so pls inaso ki bani taki goyon bayan".
YOU ARE READING
Kakkarfar Alaka
RomanceIts about a girl who went through a lot to get to where she is in life. She grew up without a father and also got abused at the place she worked and was left with an unwanted pregnancy which the owner didn't want to take responsible for.