Chapter Ten

2.8K 189 46
                                    


Points har 225, damn! Sosai yaji dad'i ya kuma yi alfahari da ita yana me kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Layin Mami ya kira take, kasancewar itace ke kusa da wayan yasa ta d'aga, bayan sun gaisa ta kaiwa Amal wayar tun kan ya buk'aci hakan.

"Assalamu alaikum Yaya ina yini?" Ta fad'a lokacin da ta amshi wayan daga hannun Mami tana mey azawa a kunnenta.

"Wa'alaikumus salam Lily, ya kike?" Ya amsa.

"Alhamdulillah ya gida ya Nazeefah kuma?"

"Lafiya Alhamdulillah."

"Toh masha Allah."

"Hmm" ya numfasa had'e da yin shiru, hakan yasa Amal tambayar ko lafiya.

"Results naku ne ya fito" ya sanar da ita cikin wani irin salon daya sa Amal yanke hukuncin ta ma riga ta fad'i exams d'inne.
"Innalillahi!" ta furta yayinda zuciyarta ta buga.
"Ban ci ba ko?" Ta tambayesa a hankali bayan d'an lokutan data d'auka.

"Toh gashi nan de-" ai bata basa daman k'arisa abinda yayi niyya ba ta katse wayar. Ba shiri ta fad'a bayi ta d'auro alwala, tana cikin shimfid'a sallaya wayan ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira wani tsinkewar zuciyarta ta kuma yi ba shakka ta fad'i d'inne in ba haka ba da tun da ya kira ze sanar da Mami. Nata ya k'are yau, shin ina zata sa kanta? Da wani idon zata sake kallon Afzal?? Hmm har ta hango tokari da habaicin da Mami zata yi mata idan ta gano ta fad'i jarabawar nan. Sanya wayan tayi a silent sannan ta shiga kawo nafilfilu.

Ta 6angaren Afzal daya san rud'ewa irin na Amal kuwa da gan-gan yayi hakan dama ba don komi ba se don yayi dariya kamar yadda yakeyi yanzu, har picturing fuskanta yadda ta rud'e yake a kansa. Two more missed calls ya k'ara mata har anan bata d'aga ba don haka ya tura mata sak'o;

'Lily pick up that phone.' Dai-dai lokacin da take sallame sallan sak'on yake shigowa batayi ta kai ba seda ta gama tofe addu'o'inta sannan ta lek'a screen d'in. Bata kai ga bud'ewa ba se ga call nasa n shigowa ta sani muddin bata d'auka ba ransa ze 6aci, ba don tana so ba ta d'aga had'e da yin shiru. Shima shirun yayi don kanta ta soma magana.

"Yaya don Allah kayi hak'uri" jin yadda ta rud'e shiko ya canza ra'ayinsa na sanar da ita aslin batun ya soma da cewa, "Lily meya faru?"

"Tell me Yaya na fad'i ko?" Ta tambayesa cike da tsoro.

"Your results..." se kuma yayi shiru.

"Yaya don Allah kayi hak'uri wallahi ni kaina ban san ya akayi na fad'i ba please don't tell Mami."

"Am so disappointed in you Lily shin duk abubuwan dana koya miki daman ba ganesu kike ba kokuwa amfani da computer d'inne baki iya ba?"

"Wallahi ni kaina ban sani ba amman kayi hak'uri don Allah."

"Nide nayi asaran biyan kud'in jamb."

"Please kayi hak'uri" ta furta a hankali yayin da takejin haushin kanta.

"Yanzu Lily ki rasa nawa zaki ci se 225?"

"Na shiga uku 225!" ta nanata a rud'e tsabagen yadda ta rikice hankalinta be ma bata taci ba se chan abin ya buga mata kai "225 fa kace Yaya?"

Rana D'aya Where stories live. Discover now