Chapter Fourty-Three

2.6K 220 81
                                    


"Ya Salaam! I don't know! I really don't know Ummi amma bazan iya jure rashinsu duka ba because I love them both ko za6i akace inyi bazan iya ba."

"Rabuwa da d'ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani."

"Bazan iya ba Ummi gara ni in mutu da in rasa d'aya daga cikinsu."
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauk'e yayinda take tausaya wa d'an nata tabbas yana cikin tsaka mey wuya "Yanzu ka kwantar da hankalinka ka koma gida d'in kaje ka samu Amal tunda bata jin dad'i gobe in shaa Allahu zan shigo."

"Allah kaimu" ya amsa.

"Yauwa nace su Mami fa ka sanar dasu?"

"Banyi ba tukuna but I'll."

"Ya kamata."

"Ummi tsoro nake kar suce zasu rabani da Amal."

"Baza suyi hakan ba in shaa Allah, kaide ka kwantar da hankalinka ka kuma sa a ranka cewa komin meya faru shine mafi alkhairi a gareka."

"Thank you Ummi bari in koma."

"Muje in raka ka."

"A'a ba amfani yi zaman ki" nan ya fice ya nufi motansa inda ya zauna ciki yana tunani, gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i. Wayansa ya zaro daga aljihu ya sake trying layin Nazeefah luckily seya shiga sede yana soma ringing aka katse cike da hanzari ya sake gwadawa wanda nan ma aka kuma katsewa. Kansa ne ya d'aure yana cikin nazari sega sak'o nan ta tura mai;

_I'm sorry I can't pick up your call, don't worry we're all fine._
Take yayi replying nata da;
_Alhamdulillah then, where are you at?_
Cikin minti d'aya reply nata ya iso
_Mummy ta kama mana d'aki a hotel zamuyi magana gobe goodnight._

Ajiyan zuciya ya sauk'e atleast they're safe, ko bey tambaya ba yasan Mummy ce ta hanata sanar dashi inda suke saboda gudun kar Daddy yayi saurin ganosu. Oh Allah!
Key yasa ya kunna motan ya dawo gida. Har anan bacci Amal ke, kayan jikinsa ya rage sannan ya duba ledan ruwan nata yaga da ragowa, gadon ya haye ya sameta inda ya kwanta a gefenta had'e da aza kanta a k'irjinsa wanda a sanadin hakan ta farka.

"Shhh go back to sleep it's just me" ya sanar da ita yana shafa bayanta a hakan har ta sake komawa baccin. Shi kam se tuna abinda Ummi ta fad'a masa yake _Rabuwa da d'ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani._

Wajajen tara da rabi ya farka bayan yayi alwala yayi sallah ya zarce kitchen ya kad'a wa Amal kununta sannan ya dawo ya shiga tayar da ita. Taimaka mata yayi ta wanke bakinta sannan ya bata kunun da kansa bayan nan ya 6allo mata magunanta ta had'iye.

"Wa zaka kira?" Amal data k'ura masa ido ta tambaya ganin ya d'ago wayansa.

"Ummi, tace in kin tashi in had'aku ta gaisheki da jiki" bata sake cewa komai ba har se lokacinda Afzal ya had'asu suka gaisa. "Mami fa yaushe zaka kira su?"

"Zan kira su Amal amma ba yanzu ba."

"Se yaushe Yaya?"

"Meyasa kika k'osa in kirasu Lily? Didn't we talked about this?"

"Yaya I'm sorry I jus-"

"Ya isa please you're sick don't stress yourself. Zaki watsa ruwa?" Kai ta kad'a masa zalla sannan ya mik'e ya ciro mata kayan baccinta ya taimaka mata tasa. Bayan ta kwanta ya d'aura mata sabon ledan drip d'in sannan suka kwanta. Washegari kaman yadda Ummi tayi alk'awari tazo ta gidansu da breakfast mey kyau da kuma kunun Amal da ta dama mata cikin flask. Har cikin d'aki ta shigo suka gaisa da Amal sannan suka dawo parlour ita da Afzal.

Rana D'aya Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon