Chapter Fourty-One

2.9K 228 62
                                    




Cike da jin dad'i da rawan jiki ta d'auko akwatin ta ajiye kan gado sannan ta shiga fiddo da kayakinta daga wardrobe tana jerasu aciki, taci rabin aikin Mummy tayi knocking bisa k'ofan d'akin. "Come in" ta amsa sannan ta bud'e ta shiga.

"Ya da shirya akwati haka ina zuwa?" Ta soma da tambaya.

"Mummy Ya Afzal yace gobe zezo ya mayar dani d'akina" ta sanar da ita cike da jin dad'i.

"Kai haba!" Mummy ta tambayeta unbelievably tana mey tayata murna.

"Wallahi ai tun last two weeks yaso mayar dani amman bakwa nan yace in hak'ura sekun dawo."

"Allah sarki Afzal, toh Alhamdulillah yayi kyau sosai Allah kaimu."

"Ameen Mummy" ta amsa delightedly.

"Kiga duk kalan rashin hankalin da kika tafka hakan be hanasa yafe miki ba har yake shirin mayar dake d'akinki. Sekiyi ma kanki fad'a Nazeefah ki kiyaye 6ata masa rai, kuyi zaman lafiya da 'yar uwarki ba abinda hakan ze ragar miki."

"Hakane Mummy in shaa Allahu komai ya wuce har gida zanje in samu Amal in bata hak'uri."

"Masha Allah, Allah baku zaman lafiya duka."

"Ameen Mummy."

"Toh kinata hanzari haka ko gobe bazaki had'a kayakin bane?"

"Toh Mummy in kuma da safe zezo fah? Ai gara nayi na gama yanzu tunda ba abinda nakeyi."

"Toh ki sauk'o muci abinci dinner is ready."

"A'a nikam zan sauk'o daga baya sena gama had'a kayakin nawa tukuna."

"Toh barin sanar da Daddy'nku."

"Yauwa do please thank you" nan Mummy ta fice ta ja mata k'ofar. Bayan sun gama cin abincin tayi gyaran murya, "Alhj?" Ta kira Daddy.

"Na'am Hjy Surayya."

"Errm batun Nazeefah ne daman, Afzal yace gobe zezo ya mayar da ita d'akinta." Dummm! Zuciyan Daddy ya buga ko motsi ya kasa yi.

"Alhj lafiya?" Mummy data karanci yanayin da ya fad'a nan take tayi saurin tambaya.

"Lafiya ba komai."

"Nace Afzal ze zo bikon Nazeefah gobe."

"Bazata koma masa ba" ya fad'a zalla. Da mamaki Mummy ta tsaya kallonsa "Dalili Alhj?"

"Nace bazata koma ba zuwa zeyi ya bata takardanta zamansu ya k'are."

Mummy ta kasa amincewa da abinda kunnuwanta ke jiye mata da mamaki tace "Alhj ka ko san me kake fad'i? Har mun samu yaron nan ze mayar da ita d'akinta kake cewa bazata koma ba? Ko kai zaman 'yarnan a gidan nan haka na maka dad'i ne? Ko so kake ka mayar da 'yar taka bazawara?"

"Nide na fad'a miki kije ki sameta kice mata ba inda zata" yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi d'akinsa. Kai Mummy ta kewayo tana kallon Khaleefah da shima ya tsaya kallonta da d'umbun mamaki d'auke a fuskokinsu. Daga bisani ta mik'e ta je ta samu Nazeefah a d'aki, lokacin har ta gama had'a kayakin nata tana cikin tattare jakukkunanta da takalma.

"Nazeefah wani abun ya had'aki da Daddy'nku ne?" Mummy ta tambayeta bayan ta zauna bakin gado.

"A'a wani abu ne?"

"Gashi ina mishi maganan gobe Afzal zezo ya d'aukeki yana cewa ba inda zaki."

"Ba inda zani kuma?" Nazeefah tayi exclaiming cike da k'in yarda.

Rana D'aya Where stories live. Discover now