Chapter Fourty-Four

2.7K 226 53
                                    


"Ummi no, ba ita bace."

"Then wacece, Nazeefah?"

"Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi."

"Ni yanzu ka rud'a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a rai kokuwa ita zaka saka?"

"Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal."

"Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi."

"Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?"

"Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i."

"I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad'ai ya bata wuya a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad'in aurena kuma na kama na k'ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba Ummi and now da abunda zan sak'a mata kenan bayan duk wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more time please ki taimakeni Ummi."

"Hak'urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da wuya Nazeefah ta kar6i bak'on lamarin nan da hannu bibbiyu kaman yadda ka fad'a amma as time progresses zata gano cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad'aya kuma ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k'arya ne. Duk kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do what's right Allah na tare da kai."

"Thank you Ummi" da haka ya katse wayan yayinda kalamun Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad'aya baze iya sauwak'e mata ba. Dama seda ta fad'a mishi cewa tasan Amal ze d'auka akanta saboda baya sonta se Amal se gashi kuma Amal d'in ze d'auka yanzu. Sede ba don baya son ta bane kaman yadda ta fad'a se don Amal ce za6in da Allah yayi masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi. Tsoronsa d'aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan 'yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa sa da ya d'au d'aya yabar d'aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey kyawun halatayya irin tata ba. She's just different.

Mik'ewa yayi a hankali yabar d'akin ya nufi nasu inda Amal ke kwance a kan gado se tunani take. Har ya k'arisa kan gadon bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.

"Rania?" Da mamaki cike da tsoro ta mik'e zaune tana kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah 'yan uwa ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik'a mata hannunsa da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga k'arshe seta mik'a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik'ar da ita tsaye akan k'afafunta. Na matuk'a kanta ya d'aure yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal ya rungumeta a jikinsa.

Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k'are, ta sani Nazeefah ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi k'arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him. No matter how hard she tried not to show how terrified she felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci Afzal ya d'agota daga jikinsa da k'yar dan yadda ta kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata "Please don't cry Rania."

Rana D'aya Where stories live. Discover now