Chapter Thirteen

2.5K 278 57
                                    

BY MIEMIEBEE
PAGE 13


Da mamaki ta k'arasa ciki ta watsa ruwa taci abinci, dab bayan sallan Maghrib ta gwada kiran Afzal sede kamar yadda ta k'udurta a ranta haka mutuminku yak'i d'aukan wayan, sau biyu take kiransa ta regular line nasa amman yak'i d'agawa, private line nasa ta kira next. nan ma yak'i d'agawa dagangan dan kuwa wayan na a gefensa yana mik'e kan gado sede ya kalla ya cigaba da zura wa ceiling ido. Sak'o ta tura masa ta text message tana basa hak'uri nan ma yak'i reply bayan ya karanta. Duk da haka bata kariya ba, ta bisa whatsapp ta tura masa messages bil adad tana basa hak'uri tana kuka duk seya karanta ya kuma k'i reply abinda yafi ci mata rai kenan. Taya har ze karanta amman baze bata reply ba? Yau ina zata sa kanta? Assignments nata data d'ibo zatayi ma taji baza ta iya ba tsan-tsan tashin hankali.

Dab tazo kwanciya wajajen k'arfe goma na dare ta sake kiran lamban nasa sai da still Afzal yak'i d'agawa, ganin ba mahalicci se Allah kawai ta tofe addu'o'inta ta kwanta abinta duk da cewan ba baccin take ji ba, gabad'aya hankalinta yana kan halin da Afzal ke ciki. Ita da tasan hakan ze biyo baya wallahi da bata shiga motan Ya Abdul d'in bama tun farko.

Washegari lectures nata na safe na k'arewa tama driver'nta waya ya dawo da ita gida. Aldeb da zo6o me dad'in gaske ta d'au lokacinta ta had'a ta zuba masa a silver flasks nasa sannan ta tanadar wa Papi da Mami nasu a gefe. Wanka ta sakeyi ta canza kaya tasa matching color hijab ta feffeshe da turare sannan driver ya sauk'eta a office nasu Afzal. Tun da ta ga motansa a fake hankalinta ya d'an kwanta. Tana isa bakin office nasan a sama tayi knocking inda ya amsa da "Come in" a hankali ta bud'e ta shiga. Sosai mutuminku yayi murna da kuma mamakin ganinta amman ya dake a gun yana wani mozewa, kansa ya kawar tamkar ba mutum neba ya shigo office d'in had'e da cigaba da aikin dake gabansa. Ajiyar zuciya ta sauk'e ta k'arisa ciki ta zauna kan kujerar da ta saba zama a kai kullum tare da yin shiru.

Ganin be da niyyan yi mata magana na kusan tsawon minti biyu kawai se ta gaishesa "Yaya good afternoon" Yadda kuka san da kurma take magana haka yayi mata, ko kai be d'aga ba balle ya kalleta se rubuce-rubucen sa kawai yake.

"Yaya gaisuwan nawa ma bazaka amsa ba?" Ta tambayesa cikin kamala a hankali tamkar wacce take shirin yin kuka. "Yaya so kake ne ciwon zuciya ya kamani in mutu? Dan Allah kayi hak'uri" har anan be ce mata komi ba.
"Yaya I'm sorry, I'm so sorry" ta fad'a had'e da rik'e kunnuwanta yayinda idanunta suka soma cikowa da hawaye.

"Yaya yanzu se nayi kukan zaka mun magana?" Yanzu kam har hawayen sun soma d'iga sede har anan Afzal yak'i koda d'aga kai ne ya kalleta.

"Toh shikenan" tayi maganan tana share hawayenta "Bari in koma inda na fito tunda ko d'aga kai bazaka iyayi ba ka kalleni" ta ja hanci "Ga Aldeb da zo6o nan na kawo maka, I'm still saying sorry" tana kaiwa nan ta mik'e, bata kai ga taka k'afarta ba Afzal ya mik'a hannu ya rik'e hijabinta, chak ta tsaya gun ba tare da tace komi ba se faman kukanta take a hankali.

"Don't go" yace da ita a hankali dad'i sosai taji amman ta fake itama "Ni ka sake mun hijabi."

"Nace ki tsaya" ya nanata cikin tattausar murya. Juyowa tayi tana kallonsa yayinda hawaye ke d'igowa sama-sama daga idanunta. "Bayan tun jiya ina baka hak'uri kak'i kulani bale ka hak'ura ni ka sakeni inyi tafiya ta dama tun ba yau ba na gano ba ka sona."

"I'm sorry toh zauna kin ji?" Ya ce da ita a hankali.

"Nifa tafiya ta zanyi ka sakeni kurum."

"Lily nace ki zauna."

"Toh haka akeyi ne?" Ta tambayesa had'e da turo d'an bakinta. "Ko baccin kirki na kasa yi jiya, I called and texted you severally sarai kana gani kak'i responding d'ina, Wallahi if only ka san yadda hankali na ya..." ba se kawai ta rushe mishi da kuka ba. Yana tayi shiru tayi shiru kar ta tara masa jama'a amman inaa tak'i jinsa, se kukarta take harda me sauti. A haka ne har PA'n Afzal ta lek'o take tambayan ko lafiya. "Lafiya Blessing don't mind her kukan banza take" yace da PA'n sannan ya samu ta ja musu k'ofan ta fice.

Rana D'aya Where stories live. Discover now