Chapter Fourty-Six

2.8K 189 43
                                    






Washegari...
Hayaniyan da Daddy ya jiyo a kitchen ne ya sanyasa fitowa daga d'aki inda yake kwance. Mami ya tarar tsaye gun sink ko mey takeyi oho.

"Jamee na mey kuma kike yi?" Ya tambayeta tsaye daga bakin k'ofan.

"Oh Alhj!" Ta juyo a d'an razane "Har ka tashi ne?"

"K'aran kwanukanki suka tadani" ya sanar da ita.

"Ayya yi hak'uri inzo in mayar da kai baccin ne ko zaka koma da kanka?"

"Ko d'aya tambaya nake mey kikeyi?"

"Oh! Doya nake ferewa Abba kasan bey karya ba."

"Inji wa? Ai da kin tambaya, tare aka siyo mana breakfast d'in nasa mey gadi ya kai masa nasa se inde zaki site nasa ku gaisa."

"Allah sarki nagode."

"Jimin matan nan fa godiyan mey kuma kike mun? Dan na ciyar da Abban mu? Taho mu koma d'aki" ya k'are had'e da mik'a mata hannunsa murmushi cike da kunya ta saki sannan ta mayar da kayan aikin ta k'ariso ta mik'a hannunta ta sanya acikin nasa, janta yayi izuwa d'akinsu had'e da zaunar da ita kan gado. Cikin wardrobe nasu ya nufa ya d'auko wani package sannan ya dawo ya zauna a gefenta.

"Hungo" ya mik'a mata.

"Mey wannan?" Tayi saurin tambaya.

"Kede bud'e ki ga" ba tare da yin gardama ba ta amsa ta bud'e d'an kunne ta tarar aciki k'waya d'aya. "Ko na waye wannan Alhj?"

"Bazaki iya tunawa ba?"

"A'a gaskiya" ta amsa tana kad'a kai amsa yayi daga hannunta yace, "Kin tuna rana na uku dana fara d'auko ki daga makaranta muna tsaye a k'ark'ashin makeken bishiyan chan muna hira muna shan rakke chan kika ta6a kunnenki kikaji ba d'an kunne? Muka ta nema amma muka rasa?"

Murmushi take sosai cike da mamakin yadda akayi har yau Daddy be mance da wannan rana ba bayan ita da ba don ya tuna mata yanzu ba ta riga ta mance da shi shaf. "Toh ai bayan dana raka ki gida na dawo na cigaba da nema ashe ma ba a wajen ya fad'i ba tun a bakin makarantar ku ya fad'i."

"Shine ka adana har yau Alhj?"

"Kamar yadda na adana soyayyarki a cikin zuciyata na tsawon shekaru ashirin da biyu." Ya amsa nan take.

Mamaki ne ya mamaye Mami gabd'aya ta rasa na cewa chan ta kira sunansa inda ya amsa a take "Alhj idan har kana so na haka toh meyasa ka gujeni? Na fahimci kayi mun abinda kayi ne saboda ka rama abinda Umma tayi maka amma meyasa ka kujeni? Meyasa ka daina d'aukan wayana?"

"Duk da hakan ma be kamata inyi miki abinda nayi miki ba Jamee amma a lokacin shaid'an ya riga ya rinjayeni I'm terribly sorry."

"Komai ya riga ya wuce Alhj ka daina neman tuba na."

"Nagode Allah yayi miki albarka."

"Ameen Alhj baka amsa min tambayan danayi maka ba."

"Kinsan wani sa'in mutum baya sanin muhimmancin abinda yake da shi se idan ya rasa, da fari nak'i in amince da cikin Amal nawa ne saboda tsoro da nake kar in 6ata wa mahaifina suna acikin gari, kowa ya sani mahaifina sanannen malami ne ba k'aramin zubar masa da mutunci zanyi ba idan har na amince da cikin cewa nawa ne. Tsoro ne yasa na gujeki Jamee, na d'au bayan da nayi nesa daga gareki zan iya mancewa dake, na d'au yin hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali ashe sam ba haka bane. Tun bayan da nayi cutting off conact dake da duk wani nawa rayuwata ta dame, acikin k'unci nake kwanciya in tashi har seda Allah ya shigo mun da Surayya cikin rayuwata, wacce ta yaye mun duk wani bak'in ciki nawa take kuma bala'in tuna mun da ke ta kowani 6angare. Duk da hakan saide idan ban kwanta ba Jamee senayi mafarkin ki, lokacin da na fara neman layinki kuma se yayita cemun switched off."

Rana D'aya Where stories live. Discover now