Chapter Two

4.3K 293 17
                                    




Seda ya d'auki tsawon lokacin da ya wuce tsammanin mutum sannan yace, "Ga magunan naki, ina kyautata zaton kin iya karatu za kuma ki iya gane dosage d-" bata basa dama ya k'arisa fad'in abinda yake da niyya ba ta katse shi "Mallam ba seka zageni ba am not an illiterate."

"Serve you well" ya fad'a ba tare da nuna damuwa ba "Then kina iya tashi in kaiki gida."

"Nagode kar ka damu I can bring myself home" taga alaman d'an rainin wayo ne shi to ya kwantar da bokatin hankalinsa, kar yace don ya ganta a haka zey raina mata wayo dan kuwa ita ba jahila bace saboda tayi karatun ta na secondary ba kuma a kowani gajan government school ba. No private school ne me kyau wanda ake kira da Ruby springfield college wanda ya kasance one of the best schools in Maiduguri.

"What gibberish are you saying?" Ya tambayeta a takaice. "See kar ki 6ata min lokaci, kar kiga don tun d'azun ina danne zuciya na ina binki a hankali ki d'au hakan ba a bakin komi ba. Ina da muhimman abubuwa a gaba na wanda sukafi tsayuwa anan ina rok'anki to take you home, now get up" ya buk'aceta cike da tsiwa sede ko motsawa Amal batayi ba. "Are you deaf?"

"I said to leave me alone!" Ta buga mai tsawan itama "Ka kama ka jawo min asara ina zaman zama na zaka wani kama kace min in tashi ka kaini gida? Me kakeson in cewa Mami bayan duk cafanin dana yo mata ka ta6ar6arar min dasu kabarni da babu? Don Allah ka barni kayi tafiyanka."

"In ke baki san abunda ya kamata ba toh ni na sani a cewarki bazan biya ki asaran dana janyo miki bane? I'm aware of all that and zan mayar miki da komi kawai ni ki tashi in kaiki gida na bawa iyayenki hak'uri na fita hak'k'inki, I have other important things to attend to" ya sanar da ita. Kaman wacce bazata motsa ba se kuma ta shiga miqewa a hankali wanda a garin hakan ta kusa fad'i kasancewar k'afar nata da ta kasa takashi. Da sauri Afzal ya tarota, ganin bey saketa ba har yanzun kuma baida niyyan yin hakan ta shiga jan hannunta sai dai ta kasa.

"Don't fight it" yace da ita "Muje" bata sake yunk'urin k'watan kanta ba har suka kai haraban asibitin inda yayi parking motarsa. Sanyata yayi a kujeran gaba sannan ya zagaya ya shiga shima tare da tada motar. A circular road inda ya kad'etan suka koma inda ya buk'ace ta da ta rubuta masa list na abubuwan datayi rashin nasu. Ba gardama ta amshi paper da biron ta lisafo komi harda kud'ad'e da amount nasu. Abu d'ad'd'aiku ne be samu ba wanda yamata alk'awarin bata kud'in idan ya kaita gida. A farko yaso su jesu kasuwan domin ta siyo amman tuna besan kan kasuwan ba sabida bai ta6a shiga ba seya fasa. A karo na biyu kuwa yayi tunanin ko zasu shiga su biyu tayi leading nasu but referring to her wounded leg yaga wuya kawai hakan zai bata so se yayi sticking to first decision d'in kawai: na miyar mata da kud'in. Kwatancen gidansu ya buk'ace ta da tayi mar wanda tayi ba tare da gardama ba. Chan cikin Jiddari suka shige. Tunda Afzal yake be ta6a shiga kwamacalan unguwa ba kaman wannan se yau, yasan war haka motansa ya fita daga kamanninsa ya dawo wani abun na daban saboda potholes da kwatamin daya rink'a shiga. Sun kai wani junction ta buk'ace sa daya tsaya.

"Ina ne gidan naku?" Abinda ya fara tambayarta kenan.

"Mota baya iya shiga layin zan k'arisa daga nan nagode."

"Acewarki kawo ki kawai nayi saboda inada ra'ayin hakan? Am here to apologize to your parents and tsaya ba sekin karya min handle na mota ba" ya buk'ace ta ganin tun d'azun take k'ok'arin bud'ewa amman ta kasa. Fitowa yayi ya zagaya sannan ya bud'e mata k'ofar tare da miqa mata hannunsa. A cewarta gabad'aya nufi yake da ta sanya nata aciki saboda ya taimaka ya fito da ita daga motan sede wani hanzari ba gudu ba tana gwada yunk'urin sa hannunta cikin nasa kawai taga yaja hannun nasa baya da sauri yana me kad'a mata kai "Tray d'in zaki miqa min" ya sanar da ita. Wani irin kunya kaman ta tone k'asa tasa kanta aciki ta jiyo amman wallahi seta rama ba shakka da gangan ya mata hakan don ya kunyatar da ita. "Kar ka damu ina da hannu I can manage" ta fad'a rai a murtik'e tare da murgud'a mai baki. Murmusawa yayi yaja gefe tare da crossing arms nasa a faffad'ar k'irjinsa yana me kallonta. Yasani sarai bazata iya fitowa ba harta sai ya taimaka mata toh why don't he enjoy the moment?

Rana D'aya Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz