Chapter Fourteen

2.5K 305 58
                                    


Tuk'in ganganci Afzal ke wane wanda ke shirin afka hatsari da gan-gan, ikon Allah ne kawai ya kaisa gida nan ma da yayi parking ya fito ko ta kan motan beyi ba bale ya zara key har ya rufe k'ofar, a wangale ya barota ya k'ariso ciki. Yana bankad'e k'ofan ciki se ga Nazeefah a shirye tsaf da alama ma fita take shirin yi.

"Yauwa Afzal zani suna ina buk'atan 5k" ta tambayesa ba tare da ta karanci halin da yake ciki ba, don 6acin rai Afzal ko kallonta beyi ba bale ma ya amsata, yazo wuceta kenan ta kira sunansa "Afzal magana fa nake."

"Nace bani da shi!" ya sanar da ita a tsawa ce. Ranta ne ya mugun 6aci dan rainin hankali banzan 5k ne ze tsaya yana mata walak'anci akai? Ai ba wai ta rasa 5k d'in bane itama kawai de don tana neman k'ari ne, ma ba laifinsa bane ita ta tambaya. "Wallahi kama kanka izinin ma na fasa tambaya" tace dashi yana cikin tafiyar.

"Karki tambayan kuma dan Allah in kin fitan karki sake tako k'afarki gidan nan aikin banza kawai" yana kaiwa nan ya wuce d'akinsa bang! Taji yayi banging k'ofar kad'an ya rage bata ci tuntu6e ba don yadda ta firgita.

Anya kuwa lafiya? ta tambayi kanta. K'arisawa waje tayi garin fito da motarta daga parking lot taga k'ofan motan Afzal a bud'e, lek'awan da zatayi taga motar ma a kunne ya barta nan ne ta tabbatar da cewa lallai-lallai something went wrong somewhere. Key'n ta zara ta kashe motan ta dawo ciki ta ajiye mai sannan tayi ficewarta.

Tun shigansa ciki ya fad'a kan gado ya kwanta can anjima ya mik'e ya shiga zagaya d'akin yayi nan yayi chan ba tunanin da be yi ba akan Amal da wannan mutumin da yaga tayi saving lambansa as 'LOML❤️🔐', gabad'aya ya rasa meke masa dad'i. Hannunsa da ya d'aga kawai yakai jikin bango, blow ya rink'a kai wa bangon yadda kuka san baya jin zafin a jikinsa, kafin ace me hannun nasa duk ya faffashe yana yoyon jini, ana cikin haka ne wayansa dake aljihunsa ya soma ruri, be damu ya cie bale ma ya duba wa ke kira ba se a karo na biyu. Ganin Amal ke kira kawai yaji zuciyansa ya sake 6aci yayin da ya shiga tafasa yana masa wani irin k'ona wurgi yayi da wayar seda ta rugurguje a k'asa (Allah sarki iphone 7) sauk'a har k'asa yayi yana wani irin kakkarwa. Mutum na iya rantsewa aljanu ne suke aiki a kansa. Idonsa ya rufe gam bud'ewan da zeyi sega hawaye na tsiyaya. Yau ran maza ya 6aci! Yafi minti goma durk'ushe a wajen, jini se tsiyaya yake daga hannun nasa, a takaice de yayi staining kan tiles d'in gabad'aya. Daga bisani ya mik'e ya shiga bayi ya bud'e tap tare da sa hannunsa k'ark'ashin running water d'in. Kun de san yadda sabon ciwo ke rad'ad'i idan ruwa ya ta6a toh k'una da rad'ad'in da zuciyan Afzal keyi masa kwatankwacin hakan ne. Bayan da ya wanke ciwon ne ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa sannan ya fito yayi dressing hannun nasa ya mik'e a kan gado.

Ta fannin Amal kuwa hauka ne kawai batayi ba layin nasa ta cigaba da kira ammana inaa se switched off yake ta cemata, private number'nsa da take kira shima switched off ke cewa dake layin a kashe ne. Gabad'aya ta rasa me ke mata dad'i, ashe da tun farko ta sanar da Afzal d'in batun Ya Abdul, a ganinta da abubuwa bazasu cha6e haka ba dan kuwa ita ko da wasa bata kawo a ranta wai kishinta Afzal yake ba, a nata tunanin ta d'au kawai he's being over protective of her ne as her big bro. Ta d'au wai haushi Afzal yaji saboda bata sanar dashi kan cewa wani ya nemeta ba har sun daidaita, little did she know shi kansa Afzal d'in sonta yake. Har dare yayi har washegari bata fasa kiran layin nasa amman inaa se switched off yake ce mata, bayan data tashi daga school yau ta biya ta office nasa sede da mamaki securities suka ce mata ai be fito aiki ba yau kwata-kwata akan bey ji dad'in jikinsa ba. Wani sabon tashin hankalin ta fad'a, mey ke damun sa? Shin jikin yayi tsanani ne kokuwa? An rik'eshi a asibiti ne kokuwa yana jinya a gida? She needs to find out. Sede kamar yadda bata san gidansa ba haka kuma bata san gidansu ba balantana taje gun Ummi taji meke faruwa. Office nasu Sultan ta wuce chan ma ta tarar baya nan wai sun wuce meeting, zama tayi kusan na awa tana jiran dawowansa amman shiru dan haka kawai ta hak'ura ta komo gida. Tana isa gida ta watsa ruwa tad'an huta chan ta d'ago wayarta ta sake gwada numban Afzal luckily private line nasan ya shiga sede har ya tsinke be d'aga ba, a karo na biyu data gwada kuwa se yake ce mata number cannot be reached ko meye dalili? Ashe blocking contact natan Afzal yayi yasa a call divert yadda baza ta ta6a iya samunsa ba.

Rana D'aya Where stories live. Discover now