Chapter Twenty-Seven

3K 216 28
                                    


   Murmusawa ya tsaya yi yayinda yake k'are wa surar jikinta kallo, lallai Allah yayi halitta anan gata 'yar siririya amma fad'i gareta ta k'asa. Na d'an lokaci ya karanci tana da aniyar janye hijabin nata ne dake rataye jikin sink ta sanya, kafin ta aikace hakan yasa hannu ya janye.

  Wai meyasa Yaya yake mata haka ne? A hankali take jin footsteps nasa suna doso ta, har6awa zuciyanta ya shiga yi yayinda k'afafunta suka shiga yin kakkarwa na sosai. A dai-dai saitin bayanta ya tsaya, hannu ya aza a kan bayanta a hankali yana tafiya sama, idanunta ta rufe gam yayinda wani irin sparks suka soma bin jikinta. Ji tayi ya tsaya chak se kuma taji yana shafa mata gashin kai, ribbon nata data nannad'e gashinta ajiki taji ya kama yana k'ok'arin sincewa. Kafin tayi wata k'wak'k'warar motsi taji ya since nan gashin nata data nannad'e jiki ya shiga warwaruwa. Da mamaki ya tsaya yana kallon irin tsawon gashin nata, har tsakiyan bayanta ya sauk'a yana lilo lub-lub yana shek'i. Har anan Amal bata juya ta kallesa ba se faman kakkarwa take, a hankali taji ya shiga takawa kuma, idanta ta rufe gam lokacinda ta gansa tsaye a gabanta, k'irjinta ta shiga karewa fiye dana d'azu yayinda takeji kaman tasa kuka dan kunya. Yafi minti d'aya tsaye a gabanta yana kallonta yana mey mamakin how fragile and delicate she is, hannu ya d'aga a hankali ya aza akan kafad'arta yana bin hannunta da wani irin shafa, se mamakin laushin jiki irin nata yake sekace auduga. Na sosai jikin Amal ya d'au wuta da irin abinda yakeyi mata. Ganin bata da niyyan bud'e ido ta kallesa ya kirata cikin sanyayyar murya.

  "Lily?" Shiru tamai "Lily k-" katse sa tayi ta hanyan rungumarsa, hannayenta ta zagaye gagam ta rik'esa a jikinta yadda ko kykkyawan motsi baze iyayi ba yayinda ta datse idanunta.

  "Goodness Lily" ya kira sunanta yana k'ok'arin raba jikin nasu sede ina ya kasa dan wani irin damk'an da tayi masa.
   "Lily I can't even breathe let me go" yadda kuka san da iska yake magana haka ta mayar dashi ta kuma k'i sakin nasa ita a dole bata son ya kalle mata surar jiki kuma hakan ne kawai take ganin mafita. Ganin fa bata da niyyan sakesa ya shiga jasu waje a hankali, k'ank'amewa tayi a jikinsa har suka k'arasa izuwa bakin gadon nasu.

  "Toh sakeni haka ki kwanta" nan ma kota motsa. "Lily da ke fa nake magana" ba suratan da beyi ba amma tak'i sakesa wane gum haka ta manne mai ajiki, haka ba yadda ya iya ya shiga sauk'a k'asa da ita har suka juye akan gadon sede tak'i sake sa har yanzun. "Lily yi hak'uri ki sakeni in kashe mana wutan kinji?" nan ma shiru duk kalan suratan da yatayi hakan besa ta sakesa ba haka a tak'ure manne da juna suka kwanta har bacci 6arawo ya d'auketa. Bayan da Afzal ya tabbata baccin nata yayi nauyi ya shiga raba ta daga jikinsa sede ina tak'i barin hakan se faman sake shigewa jikinsa take. Wai acikin baccin ma? Ya tambayi kansa. Haka sukayi baccin wahala ranan barin ma Afzal da ko nishi me kyau baya iya yi.

  Asuban fari alarm nasa ya shiga ringing, da ya ce ze motsa dan kashewa se Amal ta sake kankamesa haka alarm d'in ya tayi har izuwa lokacinda ya tayar da ita daga baccin itama.

  "Yi hak'uri ki sakeni muyi niyyan sallah kinji?" Dan albarkacin sallah kawai ta sakesa wanda da wuri ta juya mai baya ta shiga kare k'irjinta da pillow murmusawa yayi ya mik'e had'e da mik'ar da k'asusuwansa da suka murmurk'ushe, hijabin nata ya ja daga gefe ya wulla mata "Hungo sa abinki" ya sanar da ita chan ciki-ciki yace, "A hankali zaki sake da ni" bata 6ata lokaci ba ta amsa ta sanya murmushi kawai yayi ya k'arisa bayin bayan ya watsa ruwa yayi alwala ya buk'aceta da ta tashi tayi niyya itama. Yana kallonta ta shige cikin bayin da hijabin nata kafin ta fito har ya shimfid'a musu sallaya ya sanya jallabiyansa shima. Wardrobe nata ta k'arasa ta d'au zani d'aya ta d'aura sannan ya jasu sallan bayan sun idar sun kammala Azhkar nasu ta gaishesa a hankali cikin siririyar muryarta.

  "Good morning Yaya."

  "Ba suna na ba kenan don haka bazan amsa ba" ya ce mata da mamaki ta d'ago kai tana kallonsa cike da neman k'arin bayani.

Rana D'aya Where stories live. Discover now