Chapter Thirty-Seven

2.8K 217 21
                                    



"Ina securities?" Daddy ya tambaya "Nawa ne kud'in bailing nata?"

"Ranka shi dad'e ai baze yiwu kayi bailing nata ba saboda 'yarka is accused of an imprisonable offense wanda hukuma take tsoron saketa gudun kar ta sake tafka wannan laifi dan haka kotu ya nemi a ajiyeta under close supervision idan har ba wai wanda yayi filing case akantan bane ya buk'aci a saketa that is idan yaja baya da case d'in" d'aya daga cikin securities d'in yayi masa bayani.

"Alhj Amin dan Allah kayi wa Afzal magana yayi hak'uri duk nan mun san Nazeefah bata kyauta ba amma yayi hak'uri yaja baya da filing case d'innan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar komin munin halin Nazeefah bazan so ta k'are a gidan yari ba kuma tabbas idan Afzal ya kai k'aranta kotu tunda tana da laifi chan zasu kaita, ni bazanyi fighting against Afzal ba saboda shike kan gaskiya. Amma dan Allah ba dan ni ko ita ba kayi wa Afzal magana yayi hak'uri, kai kad'ai keda ikon hanasa aikata hakan please." Hannu Abba ya dafe a kafad'ansa "Karka damu Alhj Abdallah zanyi masa magana in shaa Allahu za a sake Nazeefah."

"Nagode nagode sosai."

"Toh bari mu wuce Hjy Mariam mu tafi ko?" nan sukayi sallama suka fice. Har anan kuka Mummy keyi.

"Yanzu mey riban wannan abin kunyan da kikayi mana kika kuma yi wa kanki Nazeefah? Ki gaya mun mey riban hakan? Kiga yadda Daddy'nki ke rok'an Abban Afzal kaman mey maula yanzu hakan ya miki kyau?"

"Mummy dan Allah kiyi hak'uri, Daddy I'm sorry" ta amsa cikin sautin kuka.

"Wace wacan?" Mummy ta tambayeta tana nuni da Safiyya.

'"Yar aikin Amal ce."

"Mey tayi ita kuma?"

"Mummy please forgive me."

"Ki bud'e bakinki kiyi magana ana tambayanki!" Daddy ya tsawata mata.

"Daddy dan Allah kayi hak'uri wallahi sharrin shaid'an ne."

"Am asking you for the last time idan har baki amsa tambayan da Mummy'nki tayi miki ba wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Zame hannu na zanyi acikin wannan al'amari Afzal yayi duk abinda yaga dama da ke tunda ke kince bakida hankali."

"Daddy wannan itace 'yar aikin Amal Safiyya wacce nayi amfani da ita na fidda Amal daga d'akinta."

"Kika fidda Amal daga d'akinta?" Mummy ta tambaya da d'umbun mamaki. "Kina nufin kinsa Afzal ya saki Amal?"

"Be saketa ba yaji tayi."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Nazeefah! Is this how evil you've become? A iya shekarunki kike wannan mak'irci? har kinsan ki raba aure ki shiga tsakanin miji da mata? Wallahi ba tarbiyyan dana baki ba kenan Allah ma shaidana ne" ta k'are maganan tana neman fara sabon kuka. "Duk kalan wa'azi da nasihan da nake yi miki ashe shiga kunneki kawai yake ta dama yana fita ta hagu ashe a wajen kike ajiye mun magana na, wallahi ba abun in ja miki Allah ya isa ba."

"A'a Hjy Surayya kiyi hak'uri duk bey kai ga haka ba" Daddy yace da ita yayin da Khaleefah ya cigaba da bata hak'uri yana shafa bayanta a hankali. Shi kansa mamakin halin 'yar uwarsa yake.

"Mey da mey kika rink'a sanya yarinyar nan yi haka har kika sa Amal tayi yaji iyyeh?" Tisata Mummy tayi a gaba seda ta irga dukkan abubuwan da ta aikata "Wallahi Alhj idan har baka bari an hukunta taba an yanka mata watanni ko shekaru a gidan yari ba uba kage ga 'yar nan ba, ni da kaina zan kira Afzal in k'arfafa masa guiwa in shaa Allah sekin biya abinda kikayi wa baiwar Allahn nan, har kisa mijinta ya zargeta? Zargui fa Nazeefah! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

"Mummy dan Allah kar kiyi mun haka Daddy na tuba dan Allah karka saurari Mummy."

"Kin bani kunya Nazeefah, na d'au kinyi hankali dagaske har nake alfahari da hakan ashe halin nan naki na nan har yanzu, yaudara na da Mummynki kawai kikayi kika nuna mana kin shiryu, wallahi ban ta6a tsammanin hakan daga gareki amma bazan biye miki ba, Hajiya Surayya kiyi hak'uri hanun mutum baya ri6ewa ya yasar komin mey Nazeefah tayi har yanzu a matsayin 'yarmu take hakan baze ta6a canzuwa ba. Kuma ko kema fad'a kawai kike baza kiso ace an kai 'yarki gidan yari ba hak'uri ya zama dole dama acikin 'ya'yanka dole akwai wanda ze gagareka saidai mu a matsayin mu na iyaye muyi hak'uri mu cigaba da yi musu fatan shiriya."

Rana D'aya Where stories live. Discover now