Chapter Twenty-Eight

3.4K 220 34
                                    


Wayansa ya d'ago yayi texting nata _I'll be going out, I won't take long_ bayan minti d'aya sega reply nata _Allah kare seka dawo._

Wani sak'on ya sake tura mata,
_Won't you miss me?_ murmusawa tayi ta sake tura masa reply _Ko kad'an ma._

Dariya ya saki ya sake texting nata _😫😫😭._ da hanzari tayi replying nasa _I'm kidding kar kayi kuka, I'll miss you 😘_

Yana murmushi ya tura mata _I'll miss you too take care Xx 😘_ seda ta tabbata ya fita sannan ta fito parlourn, d'akunan ta bi each tana kalla dama chan ranan da suka taho da Afzal bata samu dama tayi kallo kaman yadda takeso ba gudun karya cemata 'yar k'auye ta cika kalle-kalle. Bayan ta dawo ta zauna a parlour so take ta kunna TV'n amma kuma gudun karta rikitar da wani abun ta fasa dan haka ta zauna kawai. Wayan ta da take rik'e da shi ne ya shiga ruri dubawanda da zatayi taga Maamah ke kira da hanzari ta d'aga.

"Mata agidan Ya Afzal" ta soma da cewa.

"Uhmm ya kike?"

"Ai baki amsa ba nace mata a gida Ya Afzal."

"Kin fara ko?"

"Ko yana kusa ne bakison ki d'aga murya ya jiki?"

"Seki kwantar da bokatin hankalinki Yaya baima gida ya fita."

"Ashe shiyasa aka d'au wayana nasan da yana nan da bazaki d'auka ba."

"Haka dey kikace."

"Toh ya kike?"

"Lafiya k'alau."

"K'alau k'alau de?"

"K'alau mana" ta amsa a tak'ure.

"Ba wata jinya?"

"Allah Maamah ke 'yar iska ce."

"LOL" ta furta tana dariya "Ai gaskiya ce toh ya jiki?"

"Ce miki akayi ina jinya?"

"Ai ba se an fad'a ba da ganin Ya Afzal an san uhm uhm uhm ne."

"Ni wallhi ba ruwa na."

"Ohh Amarsu ina yaje toh ya bar mana ke kad'ai a gida?"

"Ni kawai cemin yayi ze fita and ban tambayesa ina zasa ba."

"Kode gidan uwar gidansa zasa?"

"Ban sani ba."

"Kuma baki damu ba?"

"Toh mutum da matarsa? Na isa in hanasa ne?"

"Ahh ashe k'awar tawa bata da kishin hauka ai dama jin bakinki nake bale nasan ma ba gidan Nazeefah zasa ba."

"Uhm so ya hutu?" hira suka ta6a sannan chan sukayi sallama. Tunanin me zatayi ta shiga yi zama hakan ne ya isheta gashi Afzal be dawo ba, chan dabara ta fad'o mata kitchen ta zarce ta shiga fito da groceries, had'ad'd'en jollof na spaghetti ta girka da minced meat ta ko ina a ciki, frozen chicken data ga a fridge ta ciro ta yanka ta gyara tayi pepper chicken da shi, bayan nan ta had'a zo6o me d'ankaren dad'i tayi slicing abarba aciki. Kan dining table d'in ta shirya gwanin sha'awa sannan ta kunna wuta ta turare gidan se k'amshi ke tashi. Nan ta kaiwa me gadi abincinsa sannan ta dawo ta fad'a bayi tayo sabon wanka tana fitowa ta idar da sallah ta ciro sabon d'inki ta sake sawa ta feffeshe jikinta da turare tayi kwalyanta ras. Har ta d'auko ribbon zata kama kanta seta tuna da kalamun Afzal na d'azu akan cewa tafi kyau idan ta sauk'e gashinta. Tajewa tayi ta sake a bayanta yana lilo, tana cikin d'aukan selfie taji k'aran bud'uwan gate nan fa gabanta ya fad'i seji tayi kaman ta goge kwalyar ma gabad'aya.

Rana D'aya Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ