Chapter Fourty-Seven

5K 266 59
                                    




LAST AND FINAL CHAPTER DEDICATED TO EVERY SINGLE READER ❤️

"Toh kai Afzal haka akeyi ne? Ka rik'e 'ya tun d'azu ka hana mu kakanninta rik'e ta?" Mami ta fad'a cike da wasa wanda hakan ya sanya su duka dariya a wajen.

"Mami sai de fa kuyi hak'uri dan wallahi duk yadda naso bayyana muku kalan farin ciki da walwalan da nake ciki a yanzu ba ganewa zaku yi ba, dan murna har gani nake kaman mafarki nake, I can't believe that this beautiful here is my daughter and that Amal is her mother, Alhamdulillah Allah abun godiya."

"Tabbas Allah abun godiya ne Afzal" Mummy ta sanya baki.

"Thank you Amal, Allah miki albarka."

"Ameen Yaya" ta amsa da wahalallen dariya, tana wasa da canular'n dake hannunta.

"Toh shin za ayi wa Nazeefar tamu alkunya ne ko da Nazeefan zamu na kiranta? Naga ku iyayen zamani yanzu haka kuke yayi." Mami ta kuma tambaya inda Mummy ta gyad'a kai in agreement.

"Yaya?" Amal ta kira Afzal da ya kafa wa 'yar nasu ido ko kyaftawa ba ya yi. "Yaya?" Ta sake kiransa se anan ne ya amsa gabad'aya hankalinsa yayi nesa da shi.

"Na'am Rania?" Ya amsa yana d'ago kai.

"Baka ji Mami ba?"

"Sorry meney?"

"Za'ayi wa Nazeefah alkunya kokuwa?"

Murmushi mey alfarma ya saki sannan yace, "Rania ni ai se abinda kikace."

"But Yaya I'm asking you now."

"A'a nikam se abinda kikace, don baze yi ace bayan wannan gaggarumin kyauta da kika mun in sake cewa ga abinda nake so ba, this's your moment live in it, idan kina son mu sanya wa Nazeefah alkunyan fine se mu nemi mey dad'i mu sa mata in kuma a'a we all good banida matsala." Kewayawa Mummy tayi ta kalli Mami cike da jin dad'in amsan da Afzal ya bada, inda itama ta juyo tana kallonta suka sakar wa juna murmushi. A gaskiya Allah ya amsa mata addu'an da ta dad'e tanayi wa Amal tun tana 'yar yarinya na cewa Allah ya bata miji nagari wanda ze darajata ya kuma kula da ita fisabilillah.

"Tuna mun wannan suna da kace yana maka dad'i."

"Wanne d'aya?"

"Wannan da muka gani a cikin littafi ranan."

"Wai NIHAL?"

"Yes shi why not muyi mata alkunya da shi you once said you like the name."

"I really do but are you sure? In be miki ba, ba semun sa ba."

"Of course Yaya duk wani abinda yake maka dad'i nima yana mun ko Mami?" Ta kewayo tana kallon Mami da murmushi d'auke a fuskanta. Murmushin Mami ta mayar mata had'e da amsawa "Eh Baby."

"Toh kaga se mu sanya mata shi ko?"

"Thank you so much Amal, Mami har yau bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba na tarbiyyattar da Amal da kikayi kika raineta har izuwa lokacin da na zo nayi muku wayo na d'auke ta" dariya suka sa sannan ya cigaba "Allah ya sak'a miki da mafi alkhairi da ke da Papi gabad'aya."

Mami na murmushin jin dad'i ta amsa da "Ameen. So kun yanke shawaran kenan yanzu? Nihal zamu na kiran jikar tamu da 'yar uwata?"

"Yes Mami" yayi saurin amsawa.

"Toh Abban Nihal baka sanar damu ma'anar sunan ba" fad'in Mummy.

"It means gratified; delighted; happy; prosperous; and a blissful person just like she truly is."

"Masha Allah gaskiya sunan yayi ma'ana Allah d'ayyiba ya raya mana Nihal" ta kuma cewa inda duk suka amsa da ameen. Mami ta cigaba "Duk yadda zan so cigaba da zama anan in kula da Nihal hakan baze yiwu ba yau girki na ne ko tukunya kuma ban aza ba, ni zan wuce Mummy seta bi ki kin gane?"

Kamu telah mencapai bab terakhir yang dipublikasikan.

⏰ Terakhir diperbarui: Sep 08, 2019 ⏰

Tambahkan cerita ini ke Perpustakaan untuk mendapatkan notifikasi saat ada bab baru!

Rana D'aya Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang