Chapter Twenty-Six

2.9K 181 49
                                    


Asuban fari alarm na Afzal yayi ringing, bayan ya kashe ya kunna bedside lamp ya kewayo yana kallon Nazeefah dake ta bacci a hannunsa cikin kwanciyan hankali. Peck yayi placing mata a goshi had'e da furta "Allah sassauta miki wannan kishi Rabba'atul Bait, I love you" cike da dabara ya rabata daga jikinsa ya sauk'a daga kan gadon ya nufi bayi. Bayan ya fito yayi shirin zuwa masallaci sannan ya shiga tayar da ita.

"Ta shi kiyi sallah zan wuce masallaci" yana tabbatar da ta tashi ya fice.
Dawowansa ya tarar Nazeefah bata d'akin dama yasan za ayi hakan. Kwanciya yayi kan gadon ya koma bacci kasancewar yau Asabar ne ba aiki. Se wajajen goma sha d'aya ya tashi bayan yayi wanka ya d'au wayansa ya fice parlour inda ya tarar da Nazeefah zaune kan kujera tana faman latsa wayanta. K'amshin turarensa ne ya buga mata hanci, ba shiri ta d'ago kai tana kallonsa ba k'arya yayi kyau ina irin morning shower glow d'innan? Se wani k'yalli fatan jikinsa yake k'ark'ashin ranan dake haskowa ta window. Daga bisani ta kawar da kanta badan wai kallon sa ya isheta ba se don haushinsa da take ji.

"Rabba'atul bait yau ba gaisuwa?" Ya tambayeta yayin da yake takowa zuwa inda take. Shiru ta mai ko kallonsa bata sake d'aga kai tayi ba. "Good morning Babe" ya gaisheta had'e da sauk'e mata light kiss a gefen baki. Hannu tasa ta dirje cike da takaici wanda ya mugun basa dariya amma ya dake tare da yin tari dan korar da dariyan.
"Islamiyya fa yau bazaki je ba?" Shide a dole seya sata magana.

"Mallam kana damuna da surutu please."

"Rabba'atul Bait please kiyi hak'uri haka nan" ya fad'a had'e da zama a gefenta "Nasan nayi miki ba dai-dai ba and I'm sorry bazan gaji da baki hak'uri ba but please kar ki 6ata tsakanin mu saboda Amal."

"Seka fasa aurenta tunda baka son tsakanin mu ya 6aci as simple as that."

"Tayaya kike tsammanin zan iya fasa aurenta bayan an riga an gama komai, mey kikeson incewa iyayenta bayan nan duk hidiman da Abba da Ummi suka yimin ya tafi a iska kenan?"

"I don't care, kade sani zaman lafiyanka da na ita karuwar taka yayi depending akan hakan."

"Subhanallahi! ki daina kwatanta Amal da karuwa Nazeefah tunda bata yi miki komai ba kuma baki ta6a ganinta tana wani alfashan ba."

"Bata yi mun komai ba?" Ta tambayesa yayinda take k'yalk'yalewa da dariya. "Bata yi mun komai ba fa kace? Tana shirin k'wace mun miji ka ce bata mun komai ba?"

"Amal bata da shirin yin hakan Nazeefah, wannan abu da kikeyi shi ze sa in nisantar da kaina daga gareki please cut it out."

"Oh really? So what do you expect me to do then? To fold my arms? K'ara aure fa kake shirin yi, kuma se three weeks to auren kake sanar dani how do you expect me to react? Ince Allah sanya alkhairi?"

"Hak'urin nan dey shi zan cigaba da baki I know am at fault but abinda kike yin nan kuma ba shi ze sani fasa auren nan ba kisani fa kaman yadda nake son kasancewa dake haka nakeson kasancewa da Amal, nasan da zafi amma idan kika hak'ura komi mey wucewa ne Nazeefah, I'm never leaving your side and as far as am concerned kece Rabba'atul Bait d'ina not Amal."

"K'aryar banza kawai" tayi maganan had'e da mik'ewa "Ni zan fita ina iya kai yamma kuma kafin in dawo."

"Breakfast d'ina fa?"

"Ban girka ba kana iya samun karuwar taka aww sorry amaryar taka ta girka maka" bata kai da jin abinda zece ba ta wuce d'akinta. Nan da nan ta fito sanye da hijabi shide Afzal bece mata komai ba banda binta da ido da yayi. Gabad'aya ya rasa mey ke masa dad'i Nazeefah isn't at all ready to understand him, anya kuwa ze iya da wannan bala'in da yake neman afka masa?

Gidansu aminiyarta Rumaysa ta taje inda take bata labarin abinda ya faru.

"Kar ki gaya mun Babe!" Tayi exclaiming.

Rana D'aya Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz