Chapter Fourty

3.4K 227 21
                                    


Da Asubah alarm na Afzal yayi ringing yana kashewa ya tashi ya shirya bayan nan ya tayar da Amal sannan ya fice masallaci, tana idar da sallan ta koma bacci ko jiransa ta kasa sa6anin yadda ta saba. Murmushi kawai ya saki ya tu6e jallabiyansa ya kwanta a gefenta sannan ya saita alarm nasa. Shida na bugawa alarm d'in ya shiga ruri sa6anin yadda Amal ta saba rigasa jin alarm d'in harma ta tashi ta kashe ta tayar da shi se gashi yau se baccinta kawai take, lallai nauyin baccin masu ciki daban yake. Mik'ewa yayi a hankali gudun kar ya farkar da ita sannan ya gyara mata kwanciya ya shige bayi yayi wanka, breakfast nasa ya had'a da kansa yaci ya shirya sannan ya komo kan gadon ya mata placing gentle kiss a goshi ya fice. Ba Amal ce ta tashi ba se chan wajajen k'arfe goma. A razane ta farke had'e da duban lokaci a fankacecen agogon dake manne a sentan gadon d'akin nasu.

"Subhanallahi!" Tayi exclaiming "Yaya you're going to be late" ta furta cike da tashin hankali yayinda ta juya tana neman Afzal kan gadon sede wayam ba kowa. Mik'ewa tayi ta lek'a bayi nan ba shi wayanta ta d'au ta kirasa a karo na farko ya d'aga "Good morning My Rania" ya gaisheta yana mey barin duk wani abinda yakeyi focusing on the phonecall just.

"Morning Ya Omri where are you?"

"At work" ya amsa nan take.

"Kana nufin kana office?"

"Yes Rania."

"How? Yaushe ka tashi ka shirya? Baka sa alarm bane?"

"Kina bacci duk nayi hakan alarm kuma na kunna har ya gama ringing baki ji ba."

"Omg! Ya Omri I'm sorry yanzu ka karya?"

"No harm done Rania I prepared breakfast myself."

"Next time ka tayar dani in tayaka shiri kaji?"

"No Rania, you're pregnant and still sick, kina buk'atan hutu sosai so karki damu kinji? I can manage."

"Are you sure?"

"Yes Rania, yaushe kika tashi?"

"Yanzu ban san yaushe na soma bacci mey nauyi ba, daga cewa barin kwanta kafin ka dawo daga Masjid kawai se bacci ya d'aukeni ban kuma sake jin komai ba."

"Dama chan haka baccin masu ciki yake."

"Gaskiya bazamu shirya da baby'nka ba idan zena sani bacci kaman gawa haka."

"Toh da mey zakiyi mishi?"

"Punishing nashi zanyi."

"Ta yaya kenan Rania?"

"By starving myself."

"So kike yunwa ya addabe min baby na?"

"Toh ba yana sani bacci ba."

"Yi hak'uri Rania beyi zafi haka ba, ga breakfast a kan dining nasa driver ya saya miki je kici kinji?"

"O'o" ta amsa tana turo baki tamkar yana tsaye a gabanta.

"Yi hak'uri ko in dawo in baki?"

"Eh" ta amsa da gan-gan don jin mey zece.

"Toh shikenan I'm on way ki jirani."

"Lol Ya Omri yanzu dagaske office d'in zaka bari dan ka taho ka bani abinci?"

"Anything for you Rania."

"Wasa nake maka yi zamanka kayi aiki, zanci da kaina bari inyi wanka."

"Are you sure ba sena zo ba Rania?"

"Don't worry Ya Omri sekace wacce ba tada hannu."

Rana D'aya Where stories live. Discover now