Sakeena na fitowa ta saki wani gauron numfashi, so all she had been dreading would happen kenan? Dan from the looks of this husband, he surely isn't benevolent.
Tana nan tsaye ta rasa abinyi su Hafsah suka fito; hannunsu ta kama tana fadin "A ina zakuyi wanka ku cire wadannan kayan? Come, let me help you kunji?" Ta fada tana kakaro murmushin dole, but deep down; only Allah knows what she's going through.
"Nidai da kaina nake wanka, so you can help them, but not me," Kamal ya fada egotistically, daga ganinshi he's the exact replica of his father.
"Toh fah!" Sakeena hushed. "Hafsah muje dakinki, so Shaheed kai kanaso?" Ta tambaya gana riko hannayensu, tare suka nufi dakin Hafsah.
A kitchen din kuwa, Halima ce ta tsare Baban Shaheed da idanu, dan kuwa ba tun yau ta san halinshi ba"Ina wuni? An dawo lafiya," ta furta a hankali, kasantuwar ta mace ma tsananin biyayya, duk kuwa da hali irin na Baban Shaheed.
"Wacece wannan? Ni fa na fada maki wallahi banasan kayan masu aikin nan. Me zaisa bazakiyi adhering ma words dina ba?" Ya fada in a wrathful voice.
Kara kwantar da murya tayi, "Haba Baban Shaheed, kana gani fa aikin gidannan yamin yawa, kuna ba munyi maganar dakai ba jiya ka yarda? Kaga ga aiki ina zuwa; gidan sai ya lalace idan bai samun cikakkiyar kulawa fah. Kar muyi haka dakai dan Allah, kaji?" Yadda ta marairaice mashi bazai iya cewa Aa ba, dan kuwa ba karamin ganin girma da darajarta yake ba, kuma tsananin kaunarta yake dukda halinshi.
"Naji. Amma kinsan dai halina da abunda banaso, she should make sure batayi abunda banaso ba, kuma banasan ganinta anywhere da nake sannan banaso naga tana mingling da Ya'yana, abinci, wajen...," bata bari ya karisa ba tayi cutting dinshi off with a chuckle and a soft smile on her lips.
"Baban Shaheed duk na sani, karka damu zata kiyaye kaji? Yanzu go and have a bathe kafin na gama abincin, ko ma kai zaka ida ne?" Ta fada tana shooing dinshi waje.
Dan yak'e yayi, dan shi saita kure mutum yake ganin dariyarshi. "Bari naje na shirya na fito, sai na tayaki," yana fadin haka ya fice. Dan ba yau farau ba, sometimes ma saidai ta zauna ita da yara suna kallo yaje yayi girkin ya kawo masu.
Yana fita ta girgiza kai tana murmushi, "Abun Baban Shaheed sai shi," daga haka ta cigaba da aikinta, without any worry in the world. For she knew Sakeena is with the kids, dan ta fada mata kullum ta rika masu wanka idan sun dawo.
***
Inna ce zaune kusada Baba, tunda ya dawo ya tambayi whereabouts din Sakeena ta fada mashi ta tafi aikatau bai kara magana ba, don from all indications he's ruminative akan zuwan Sakeena aikatau dinnan, could he allow her ko kuwa yaje ya karbi yar sa? For he couldn't stand her being humiliated.
Zama kusa dashi Inna tayi, dan kuwa duk wulakancinta idan yana cikin damuwa bata jin dadi. "Naga baka ci abinci ba tun lokacin dana kawo maka, ko baka lafiya ne?" Inna ta tambaya tana tsareshi da fiesty orbs dinta.
Har ya juyo kamar ya amsa sai kuma yaga arguing with Inna isn't worth his time. For he knew the moment he utter a word about Sakeena being a maid, she wouldn't take it easy on his. And her rants are the last thing he wants his brain to consume.
Ganin da gaske fa ba magana zai mata ba yasa Inna dan daga murya alamar ranta ya fara baci "Wai kai bawan Allah tun yaushe nake maka magana ne? Kasan halina fah, danma ka samu ana lallaba ka? To kar kaci abincin, ita zama da yunwarka. Aikatau ne kuma sun tafi, dan nasan shine abunda yake eating dinka up," tana fadin haka ta mike tsaye hade da dusting off zaninta kafin ta shige cikin daki.
Girgiza kanshi yayi yana adduar Allah ya shiryata. Daga sama ya fara jiyo hayaniyar Tukur da matan gidan, dan da alama saida yasha yayi tatul kafin ya dawo gidan, holding a black leather, it was obviously for Sakeena.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...