BABI NA ASHIRIN DA TARA

1.4K 202 24
                                    

Dare ne kamar ko wanne. Babu karar dake tashi cikin gidan face slow hums of the air conditioners. Habibah ce ta fito daga toilet din dake adjoined with her room, a towel wrapped firmly over her full chest. Zuwa tayi gaban mirror kafin tayi applying lotion sannan ta fesa body spray.

Wajen wardrobe dinta ta nufa, dan kam zuwa yanzu Saheer ya siya mata dukkan wasu kaya da yarinya wacce ta taso cikin gata zata samu. Zamanta a gidan nan wata daya kenan, and she couldn't point out a single day she wasn't happy about.

Rayuwa sukeyi me cike da farin ciki da annashuwa, dan kuwa Saheer kusan kullum idan ya dawo aiki da yamma yakan dauketa haka nan su fita cikin gari suje yawo, wani lokacin kuma sukan kare yammacinsu cikin garden din gidan. Tsakaninta da Maama kuma wata irin girmamawa ce sosai, though har yanzu she isn't feeling comfortable with the kind of stares she's getting herself from the woman. But she's okay living in the house as long as she would be together with Saheer.

Kayan bacci ne ta dauko cotton ta riga da wando kafin ta sanya ta koma kan gafonta. Har ta kwanta ta tuno da littafin da Saheer ya bata da yamma domin ta karanta, dan yanasan yaga idan da hali yasa ta kara zana waec dinta ta koma makaranta.

Janyo littafin tayi from her bedside drawer ta fara karatu, sama sama bacci ya fara daukata nan ta ajiye littafin kawai ta fara bacci abunta. Cikin bacci kamar a mafarki, a feeling like a deja vu; taji ana wani tattabata ana shafa wasu bangarori na jikinta wanda tasan tabbas wannan ba abun arziki bane. Fuskar Ramcy ce ta fara fado mata a rai, sai kuma ta tuna cewar Ramcy fah yanzu basu tare, And there's no way Ramcy ta shigo gidannan nan cikin irin wannan daren.

Idanunta ta fara budewa a hankali, amma babban tashin hankalin; Maama ta gani cikin wata irin shiga wacce bata da kyan gani. Zumbur Habibah ta mike ta sauka daga kan gadon gaba daya, not wanting to believe what her eyes just show her.

Rufe idanunta tayi tana karanto innalillahi! Tun tanayi cikin ranta har maganar tadan fara fitowa fili. Maama ce ta taki tazo har gabanta kafin ta riko hannunwanta tana me kureta da idanu hade da jifanta da irin kallon da sak Ramcy take mata. Ita kam taga rayuwa.

"Maama lafiya? Me kikeyi a nan?" Ta tambaya, for she doesn't want to believe what her subconscious was trying to make her believe about the woman that gave birth to one of the kindest men on earth.

"Babu wani abu fah a ciki Beebah, menene toh duk kin wani bi kin daga hankali? Kwanta kinji? Bacci kawai nazo na tayaki nothing more." Yadda Maama ke magana kai ka rantse da mijinta take magana, hakan ba karamin tada hankalin Habibah yayi ba, from how she talks seductively and the lust roaming around her eyes.

"Maama nifa ban gane ba, dan girman Allah ki tafi dakinki ki kwanta, wallahi banasan irin wannan abun. Dan Allah na rokeki," sil sil taji hawaye sun fara sauka saman kuncinta, dan ita kam ta gwanmaci rayuwar kunci akan irin wannan kazantacciyar rayuwa.

Ganin zata tara mata jama'a yasa Maama tayi saurin mikewa tana me murmushi irin na yan duniya. "Karki damu kanki kinji? Dama mafarkin tsoro nayi shine nazo mu kwana tare amma tunda bakiso ba wani abu. Bari naje saida safe." Wani irin mischievous smile tayi flashing mata kafin ta bude kofar discreetly ta fita ta rufota a hankali again.

Tana fita Habibah ta hade kai da guiwa ta fashe da kuka, ita kam haka Allah yaso da ita, wannan wata irin jarabta ce? Ya zatayi da rayuwarta fisabilillahi. Saida ta farajin kiraye kiraye kafin ta mike jiki sakaka ta wuce toilet tayo alwalla kafin tazo ta gabatar da sallah.

Wata daya daya wuce anyi abubuwa iri iri wanda kwata kwata Sakinah bata kaunar ta tuna ko daya daga cikinsu. A yanzu haka an sallamo Arhaan ya koma Abuja a cewar Mama bazata iya barinshi a gidan ba har sai taga lallai da gaske ya warke din.

Sakinah rayuwarta take cike da jin dadi da annashuwa, dan kuwa yanzu babu wanda yake takura mata face Baban Shaheed, dan haka nan sai yazo ya tsaya tsakiyar falo yace sai ta fiddo kaf kayan dake cikin dakinta ta wanke dakin, wai kaf gidan zaurin fitsarinta yake. Kai wulakanci yau na gobe daban, ita kuwa Aunty Halima babu yadda ta iya sai in ya tafi ta bawa Sakinah hakuri.

Yau ma wasn't an exception, dan kuwa daren jiya Aunty Halima ta kawo ma Sakinah five alive tasha, hakan ya haifar mata da malale katifarta jagab har falo zaurin fitsarin bai bari ba. Kasancewar ranar weekend, tun wajen karfe takwas ta fara jiyo muryar Baban Halima tsakiyar falon yana surfa masifa.

"Halima mena fada maki akan yarinyar nan? Bafa zata maidamu kazaman karfi da yiji ba, tun waccan wata ya kamata ki sallameta amma you're hell bent on making her stay. I'm tired of this, ko Shaheed baya fitsari balle ita babba da ita." Ya cika baki sai masifa yake, nan take Sakinah taji hawaye sun fara gangaro mata, ita kau taga rayuwa wajen mutanen gidan nan, farko shagwababben kanin Aunty Halima, yanzu kuma wannan mijin wanda kullum fuska daure kamar an aiko mashi da sakon mutuwa.

"Dan Allah Baban Shaheed ka tsaya kaji, kaddara ce fah, Kuma kowa bai wuce Allah ya jarabceshi ba. Ita tata jarabtar kenan. Kayi hakuri dan Allah." Muryar Aunty Halima cikin taushi take, ita dai fatanta karya kori Sakinah, wulakancin sai yayi yawa.

"Na riga na yanke shawara fah, can ita ta sani da jarabtarta ni babu abunda ya shafemu bazata maida man gida kamar gulbin fitsari ba." Bai jira me Aunty Halima zata ce ba ya fado dakin da Sakinah take.

"Ke ki shirya gobe ki koma gida na sallameki. Tana maganar albashinki na wannan watan da bai dade da kamawa ba, gashi dana watan bayan dukan dana gaba kije ki samu abunyi amma aikatau bai dace dame fitsarin kwance ba!" Yana fadin haka ya fiddo rapper din 500 ya jefa mata saman fuska kafin yaja tsaki ya fita daga dakin.

Sakinah na jiyo muryar Aunty Halima da alamu kuka take tana fadin ya zai mata haka. Cikin wani gunjin kuka Sakinah ta dauko kudin ta ajesu gefe kafin ta lalubo wayarta hade da kiran number din Ya T. This is what she had been wanting to happen tun sadda tazo right? But why is she feeling bad about? Kaman she's leaving some part of her in this house?

"Hello Ya T, dan Allah kazo address din gidan dana maka kwatance. Amma ba daidai kofar gidan ba, in kazo ka kira in fito akwai abunda zan fada maka." Tana fadin haka ta kashe wayar dan tasan bai zama lallai ya amsata ba.

Baa jima ba sai ga kiranshi, hijab kawai ta saka sidip sidip ta fita daga gidan. Few houses away from the house sai ga T zaune saman mashin dinshi yana busa sigari, yana ganinta ya wurgar da tabar ya take ta da kafarshi.

"Ke ya akai kina kira mutum kina kuka kuma? Ko wancan shegen yaron ne ya kara maki wani abun?" Yanzu a tsaye yake hovering over her, muryarnan tashi ta yan daba data sani sam bata chanza ba.

Fashewa Sakinah tayi da kuka kafin tayi hugging dinshi, dukda kaurin dayake na hayakin taba bai hana taji wani relief ba. "Mai gidan ne ya koreni Ya T saboda fitsari, kaga dama ba saida na fadawa Inna banaso nazo ba? Yanzu gashi nan ya wulakanta ni. Yace gobe na tafi, yanzu ya zamu fada mata kar taga kamar da gangan nayi laifin daya koreni." She broke their hug and kept looking at him hopefully that he would come up with something that would satisfy Inna's curious mind.

"Goben zanzo na tafi dake, idan munje sai ace mata nazo gyaran wani abu a gidan banma san gidan kike aiki ba naga mai gidan yana dukanki dan kin manta ki share wani bangare a gidan. Dan idan na fada mata tuntuni nasan gidan zatace ni nazo na masu tashanci naja suka koreki. Hakan yayi ko?" Sakinah smiled gratefully and hugged him again. Babban farin cikinta bai wuce duk lokacin datake bukatar dan uwa Ya T would always be there for her.

"Hakan yayi sosai Ya T! Amma idan na koma zamu fadawa Baba gaskia sai kar ya fada mata ko? Yanzu ka tafi kafin mijin yazo ya hangomu. Nagode sosai, goben zan kiraka time din dazaka zo Ya T." Tana fadin haka tayi shaking hand dinshi with a fully etched smile on her lips kafin tayi waving dinshi goodbye ta kama hanyar komawa gidan.

Abunda bata sani ba shine Baban Shaheed wanda bai jima da fita ba ya dawo idanunshi sukayi arba da Sakinah a lokacin da take hugging T for a goodbye. Tana shiga gidan ta fara jiyo sautin muryarshi yana masifa, karasawa falon tayi taganshi tsaye shida Aunty Halima and the person she least expect-Arhaan, and hakan ya tabbatar mata da cewar Arhaan yaje daukowa a train station and now Arhaan ya ganta da Ya T kuma zaisan tabbas itace ta tura Ya T yai mashi wannan dukan kawo wukar.

Inda ba kasa nan ake gaddamar kokowa.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now