BABI NA ARBA'IN

1.7K 322 95
                                    

Idanunta suka fara kawo ruwa, kallon kofar dakin take cike da jiran zuwan mijinta amma taji shiru. Wani tsoro da fargaba ne ya darsu a ranta, abunda samarin nan suka mata ya fara dawo mata sabo kawai ta fara ja baya cike da tsoro tana girgiza kai. Wata irin tsawa Arhaan ya daka mata "Zaki gaya man me kikeyi a nan ko kuwa?" Ya tsaneta, tsanar da baisan irin yawanta ba, ganinta anan kuma ba karamin kara kunna wutar tsanar yayi ba.

"Kayi hakuri, I'm not here to harm you. Nan gidan aka kawo ni, and Mama told me nan zamu zauna da miji na. Ka ganshi?" Dakyar take magana tana baya har saida ta zauna dabas saman gadon, a lokacin ne kuma fargaba ya fara seeping into her soul, to kodai Arhaan shine mijinta? Girgiza kanta ta fara tana kallon Arhaan wanda yake jifanta da wani irin kallon tsana, if looks could kill, she would've been dead by now.

"What's your name again?" Hankalin Arhaan in yayi dubu to ya tashi, fargaba da tsoro sune abubuwan da suka mamaye zuciyarshi. Allah ya sa wannan Sakinar ba ita bace Sakinar da Mama ta aura mashi ba. Ubangiji Allah yasa tunanin da yakeyi akan Aunty Halima ce ta samar ma Sakinah aiki a gidanshi, Allah yasa hakan ne.

"Sakinah Abdullahi Bello." Haka kawai she felt the urge to tell him her full name, dan yanzu burinta bai wuce ace ya fita yabar dakin nan ba ko waye mijin nata ya shigo ta ganshi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" A hankali kalaman suke fitowa daga bakinshi, dama akwai couch opposite gadon dan dole ya zauna saman couch dinnan yana kallon Sakinah, sai kallon shi take cike da tsoro.

"Me Mama tace miki kafin a kawoki nan?" So yake kawai ya kara confirming doubts dinshi, baya tunanin Aunty Halima would let Mama get him married to a girl like this, a girl like Sakinah.

Ita kuwa hakan da yayi ya kara tabbatar mata da abun da take tunani hakan ne, wata irin zufa taji ta fara keto mata; Safiyya had put on the air conditioner amma Sakinah batajin duk zafin dakinsu na gida zai kamo irin zafin da takeji yanzu.

Hawayen da ta dade tana rikewa suka sulalo saman cheeks dinta, hango Arhaan kawai takeyi lokacin da yake asibiti, irin jina jinan da Ya T suka mishi, wani tsoron ne ya kara shigarta. Na shiga ukku, ta furta a ranta tana me kara kankame kanta, dan gani take babu abunda zai hana Arhaan lakada mata na jaki ya kuma saketa cikin daren nan. To wai ma meyasa Mama zata rasa wanda zata aura mata sai dan cikin ta? Dama akwai masu kudi irin Mama a doran kasa ne?

"Ba dake nake ba?!" Wata irin tsawa ya daka mata cike da bakin ciki da tarin takaici, shidai Mama bata taba mashi mugun abu irin na yau ba. Fisabilillahi ta rasa wadda zata hadashi aure da ita sai Sakinah? Wai kodai dan batasan wacece Sakinah ba da kuma abunda ta aikata mashi?

"Tacemin nan gidan mijina ne, kuma mijina zai shigo ya ganni. Amma ni bata fada man waye mijin ba, ko tare kuke dashi?" Har yanzu so take yace mata mijin ya rako ko kuma wani abun yazo yi a gidan, har yanzu fata take ta farka daga wannan mummunan mafarkin da takeyi. How in the world would Arhaan be her husband? Tasan kashinta ya bushe.

Wata irin iska me zafi Arhaan ya furzar, paper din da Mama ta mishi rubutu a ciki ya kara murzawa cikin aljihunshi. This is what Mama wants, the woman he can take a bullet for. Amma kallon Sakinah a saman gadon nan tana kuka while shivering with fear infuriated him, and she even had the guts to ask him ko tare suke da mijinta.

Tsaki yayi me sauti kafin ya mike tsaye, shi saidai a hade sama da kasa amma bai ganin kukanta. To what changed her? Ko duk cikin sentiments din auren ne? What happened in the first place ma da zaace Mama ce wadda zata zabar mata miji tayi aure? All this questions are for Mama, dan haka ya maida hankalinshi akan Sakinah with so much disgust.

"Ke data tashi daura maki auren bata fada maki waye mijin ba? Aren't you even ashamed of yourself ki kira kanki matata? To nine mijin, and welcome to hell." Yana fadar haka ya dauko katin bikin daya gani a kan bed side drawer dinta, wanda tunda Safiyya ta kawosu ta aje Sakinah ko kallonsu batayi ba ya watsa mata a face dinta.

"I guess you're educated ko da cikin cokali ne, because bakin rashin kunyarki yayi yawa, check the name written. Mind you, duk wani rashin kunyar ki ajeshi zaki gafe, I'll let you be for the sake of Mama. But keep this in mind, Na tsaneki." Ko kallo bata isheshi ba ya juya ya fice daga dakin, jikin Sakinah kamar ya balle haka ta fara kiciniyar bude card din nan, and behold she saw his name boldly written: Arhaan Aliyu Zubayr.

Wani irin kuka ne ya kufce mata, sulalewa tayi kasan gadon har saida tayi mai isarta. Tunani take yanzu ya zatayi? Which hell would she prefer? Hell din gidan Inna ko tanan gidan? Dan tasan they'll be the same. In har Arhaan ya saketa ko ruwa bazata iya sha ba a gidan Inna, idan kuma ta zauna gidanshi tabbas na lahira sai yafita jin dadi.

Dakyar taja jikinta ta shiga toilet ta watso ruwa ta fito, kayanta da Safiyya da Muhibbah suka shirya mata cikin wardrobe dinta ta duba ta samo wata nightgown cotton me taushi har kasa with long sleeves, yadda takejin ranta ko kadan batasan iska ta shiga jikinta. Da addua bakinta haka ta kwanta hade da lullubewa da comforter bawai dan tasan zatayi baccin ba. She has seen worst, this shouldn't take a toll on her.

A bangaren Arhaan kuwa yana komawa dakinsa ji yayi kamar ya fashe da kukan bakin ciki, kallon dakin yake yana tunani what in the world made Mama get him married to that girl? Ko dan bai fada masu itace silar kwanciyarshi asibiti ba? Wayarshi ya ciro ya fara dialing number din Mama amma ya jita kashe, bata kashe waya saidai in da dalila yasan for sure tasan abunda ta mishi.

Aunty Halima ya kira yaci sa'a ita ta daga, tun kafin ya fara magana yaji ta fara. "Arhaan nasan mi yasa ka kirani, kuma nice nasa Mama ta kashe wayarta. Arhaan Mama tayi abunda tayi maka ne with a good intention, dan Allah ina rokan ka da ka dubi soyayyar dake tsakaninku da Mama kayi accepting auren nan, kar kasa tayi feeling guilty of what she did. Tun lokacin data man maganar I objected, but ganin ta damu yasa na hakura, dan Allah Arhaan..." magana ta cigaba da mashi cikin sanyin rai da tsananin kulawa, duk duniya baida wand aya wuce Mama da Aunty Halima, dan dole dan babu yadda zai iya mata gardama yasa ya amsa da toh daga haka suka kashe call din, but deep down yasan he has to speak with Mama. Everything seems choked.

Washe gari ko da Sakinah ta farka dakinta ta gyara tayi wanka ta shirya tsaf, dama kusan rabin kayan lefenta a dinke suke. Saida tayi kusan zaman thirty minutes cikin dakinta tanajan addu'o'i Allah ya rabasu lafiya da Arhaan, ita ko ganin shi ma bata kaunar yi. A hankali jiki a sabule ta bude dakin ta fito dan taga wane hali gidan yake ciki.

Masu aiki guda biyu ta iske a falon, wata tana aikin jera warmers saman dining table daya kuma tana goge gogen kayan kallo. Dukansu dagowa sukayi suka gaisheta ta amsa a mutunce, so take ta tambayi mai gidan amma ta mishi me?

Bayan sun gama komai suka wuce boy's quarters inda anan ne masaukinsu yake. Dining din ta karasa, dan kuwa wata irin wahalalliyar yunwa takeji kamar ranta ya fita. Ta zauna kenan tana serving kanta taji karat bude kofa, kallon wajen tayi, and behold; kofar data dade tana tunanin ko store ko wani abu taga an bude sai gashi. Directly eyes dinta cikin nashi suka fada sai taji ya mata bala'in kwarjini, yadda taga ya daure fuska kuwa dole ya darsar mata da wani mugun tsoronshi.

Jiya yace mata 'Welcome to Hell.' For sure tasan she would taste what a hell is like. Arhaan wani siririn tsaki yaja cikin ranshi, yau da asuba ya tashi yaga text message din Mama which reads 'Morning yaran mamanshi. Ka tashi lafiya? I hope you didn't cry ko? Dan Allah Arhaan accept this marriage kaji? Treat her well as though the girl you spent decades in love with. Mama zaka mawa, please. Go check up on her da safe, ka sauke hakkokinka dana gaya maka a kanta, dan Allah Arhaan. Sai kazo da safe we shall talk, but please do this for Mama, kaji Dan Mama?'

Shi abun har mamaki yake bashi yadda Mama ke pleading with him akan wannan yarinyar. Yadda tayi saurin dauke idanta akanshi yasa dakyar ya taka ya isa inda take, wani kallon banza ne yake watsa mata while her eyes were fixed on the plate wanda ko abincin ma takasa ci sai wasa take dashi. He hates her with passion. But he's doing this for Mama.

"Baki iya gaisuwa bane? Ko har yanzu rashin kunyar taki bata sauka ba?" Cike da disgust da hatred yayi magana, wanda hakan yasa ta dago eyes dinta that were filled with tears ta saukesu a kanshi.

Murya na rawa Sakinah ta furta "Kayi hakuri, ina kwana?" Wannan sabon halin nata yafi komai kona mashi rai.


Hello guys!

Na lura kamar ba dadin littafin nan kukeji ba right? Ace babu comments fisabilillahi? Ina ganin zan daina rubutun kawai kowa ya huta.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now