BABI NA SHA BIYAR

1.7K 307 11
                                    

With glassy eyes, haka take kallonshi, dan jikinta har rawa ya fara; ganin yadda ya murtuke fuska-tasan koda ace azara'ilu ne yazo daukar ranta kila ba haka zai daure fuska ba. Baya baya ta fara ja, tana kallonshi idanunta cike da tsoro.

Shi kuwa kallonta ya tsaya yanayi, idan akwai abunda yafi bacin rai to tabbas yau ya shigeshi. Kallon yadda idanunta suka cika taf da hawaye yake, ga jikinta yana rawa ta kasa koda motsa baki.

Da kyar kwakwalwarta ta tuna mata abunda ya kamata tayi, for she fell into a hiatus; after colliding into the Lion-as she named him. "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan kai bane ba," she stuttered, a daidai lokacin da bayanta ya bugo da bangon dan corridor din; that means ta zo karshe kenan, amma tasan babu halin guduwa tabar wannan zakin me gurnani-dan definitely sai ya biyota.

Yadda kasan da bango haka take magana, fuskar nan kuwa hade kamar an turo mashi mutuwa-kwakwalwarshi tunani take akan abunda ya kamata ya mata, bacin baida lokacin batawa yau da sai ta gane kurenta; kuma saboda Halima bazai iya korarta ba-dan yaga san yar aikin take.

"Dan Allah Baban Shaheed kayi hakuri, na rantse da Allah wallahi bansan kai bane-nayi tunanin wannan dan...," sai kuma tayi shiru, dan tunanin she would've spilt that to this roaring lion before her.

Sai a lokacin yayi gulping lump din da yake throat dinshi kafin yayi magana "wanene dan rainin wayon? Dan naga kafata da inda kika daka bai maki kama dana yara ba balle kice Kamal ne ko?" Shi kwata kwata ma hankalinshi bai kawo wajen Arhaan ba, dan ya dauka raina mashi wayau kawai zatayi.

"Aa wallahi ba haka nake nufi ba, nidai kayi hakuri dan Allah," duk ta rude, dukda a nutse yake maganarshi amma ba karamin kada mata yan hanji take ba.

Ko kala bai kara ce mata ba, dan a ganinshi kaskantar da kai ne ya tsaya yana magana har haka da yar aikin gidanshi, amma dole yama Halima magana domin taja mata kunne-dan shi if it's possible ma-she should make herself oblivious idan yana nan.

Yana wucewa-Sakinah heaved a sigh and cleared the line of sweat that formed on her forehead, with a relief smile adorning her full lips.

"Na tsira yau, Allah ka kara kareni nan gaba," daga haka ta shiga ta cigaba da aikace aikacenta, amma dukda haka duk wani motsi da zataji sai tayi tunanin duk shine ya dawo domin ci mata mutunci.

***

Zuwa yanzu ciwon dake jikin kafarta ya warke kamar ma baayi shi ba, amma duk karin second dinta daya a duniya-ciwon dake cikin zuciyarta yana kara linkuwa linkin ba linkin ne. Normally, a well functioning heart beats 80 beats per minute, to her-with each beat-the pain in her heart intensifies itself into millions.

Kullum cikin dare sai tayi kuka, gashi kusan yanzu kullum Ramcy tana nanike da ita-but what baffles her was she couldn't even say no to whatever Ramcy does to her body, dukda dai she never exceeded her limits, amma dukda haka it was over exceeded to her frail heart.

Tunani akan iyayenta kuwa, tun tana lalube cikin zuciya da kwakwalwarta-har ta daina, dan kuwa it causes nothing but a throbbing headache to her already thudding brain. Iyaka idan ta gama dan lalubenta cikin brain dinta ta kasa ganin information daya-to zata zauna ta dizgi kukanta har ta godewa Allah.

Phone-was her only companion, dan it's the only thing she used in taking off her mind from this hideous world. Kamar ko wanne marece a kowacce rana, dolene kafin Ramcy tabar gidan zatazo ta dan lulubeta kafin kuma hakan idan ta dawo da daddare-amma bata taba wuce iyakarta ba. A cewarta, sai ta gama koya mata dadin abun tukunna. Allah ya tsaremu.

Tana zaune cikin dakinta tana game sai wayar ta fara ruri, sliding answer button tayi before ta amsa da "Toh gani nan" kafin ta wuce kitchen. Yadda ta saba hadawa Hajia Hauwa kayan motsa baki idan tazo haka ta hada kafin ta wuce hanyar main living room.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now