Wani irin wawan tsaki yaja, ganin Sakinah tsaye da wayarshi a hannunta. Mamaki abun ya bashi kafin daga bisani ya tuna cewar yana asibiti baida lafiya fah. Dan yunkurawa yayi ya jingina da pillow kafin yasa hannu ya karbi wayar.
"Wai ke dan Allah baki da hankali ne? Maganar serious ba wasa ba. Ke komai sai kinja fitina? Yanzu raguwa zaki idan kika tadani cikin kwanciyar hankali? Aa amma saboda tsabar neman magana irin naki dole sai kin firgita mutum. Kuma wama yace maki budurwa tace? Ko baki iya karatu bane?" Shi dama in kanaso kaga vulnerable side dinshi to ya fara bacci, Allah yasa abunda yafi bacin rai ya shiga, tabbas kuwa bai iya magana cikin hargitse ko makaman cin haka, indai ya fara bacci.
Maimakon ta koma ta kwanta, kawai sai ta janyo kujerar kusa da gadon ta zauna, dan ta bashi amsar data kamace shi. "Miye neman fitina kuma nan ciki? Aa ka manta, world war 3 na tado wallahi. Tunda ni ban iya karatun ba ai kai naga ka iya ko? Dan rainin wayau, inga ansa Ajay da heart ba sai inyi tunanin budurwarka bace? Kuma ka taba ganin namiji ya kira namiji cikin tsohon dare?" Bacin Mama dake bacci cikin dakin, inches away from them, da muryar Sakinah bazata taba yin kasa haka ba, dan da ace wani zai jisu sai yayi tunanin labari suke mai dadi.
Girgiza kai kawai yayi, da dai bai fara bacci bane sai ya bata amsar data dace da ita, amma shi yanzu tashi ta kare kuma. "Ke ni banda lokacin ki, rashin abunyi ne ya maki yawa. Miko man wayar ko? Ko taki ce? Kin wani kama abu kin rike gam," baisan yadda akai yake biye ma yarinyar nan ba, dan da da ne saidai kawai yayi tsaki ya fizge wayarshi ya barta nan zaune.
"To masu waya, muda bamu da ita sai kaga mun fadi mun mutu." Harara ta galla mashi kafin ta mika mashi wayar, yafito hannunshi yayi yanasan marinta amma ta kauce tana kara harararshi, kafin yayi mosti kiran ya kara shigowa, dauka yayi murya kasa kasa.
Abokinshi ne wanda tare sukayi makaranta tun primary har karshe, dan hada dalilinshi ma yasa Baba da Mama suka yarda Arhaan ya taho kaduna service. Sakinah na nan zaune tana jira ya gama wayar ta juye mashi kwandon rashin mutuncin ta, gabanta yayi wayar ya gama kafin ya mika mata.
Kin amsar wayar tayi saima kauda ido da tayi kamar bataga abunda yakeyi ba. Wani dan siririn murmushi yayi, dan shi harga Allah bawai ya cika san fitina bane, balle cikin wannan tsohon daren, "Ki ansa ki ajeyimin saman drawer dincan." A hankali yayi maganar dan ma gudun karya kara tunzura ta, dan ya lura saurin fushi gareta.
Saida yai magana sau uku kafin ta juyo ta kalleshi, "Bazan karba ba, aini bari kaji, ko gani nayi wayar nan nada niyar fadawa cikin ruwa bazan janye ta ba. To wai kai ma tsaya, da na tsaya sai ka mareni? Wallahi Arhaan kana wasa dani, yadda baka da lafiyar nan sai in karasaka ni ba damuwa ta bace." Wata irin muguwar harara ce take galla mashi kamar idanuwanta su fado, shidai baice komai ba saima binta da ido da yayi, mamaki ma abun yake bashi, yadda mutum cikin tsoron daren nan yake iya bude baki yayi masifa.
"Naji toh, yi hakuri yanzu dai ki ajiye." Ba ita kadai ta razana bashi, harshi saida yaji mamakin abun, saida ya waiga yaga ko wani ya shigo dakin yaga su kadaine dinne dai.
Hannu tasa ta karbi wayar ta ajiye, har ta mike ta koma inda take yayi gyaran murya, juyawa tayi ta kalleshi, dan kuwa idanunta sun fara lumshewa saboda bacci, "Ya akayi?" ta furta cikin muryar masu jin bacci, tana kureshi da idanuwanta lumsassu.
Gabanshi yaji ya fadi, amma daurewa yayi ya kalli inda kayan abinci suke "Ki hada man tea mai zafi." yana fadin haka bai kara kallonta ba, yanaji ta gama galla mashi harara kafin tayi hanyar wajen kayan abincin.
Hado mashi tayi ta kawo. Tana ajiyewa yace ba bread yakeso ba ta miko mashi biscuit, mika mashi tayi ta juya zata tafi ya kara tsaidata "Ki tsaya idan na gama in baki cup din ki ajiye."
Wata irin wawuyar juyowa tayi, zama tayi kan kujerar kafin ta fara maganar cike da takaici, amma kuma murya kasa kasa "Kai ka bar ganin fa ina daga maka kafa yau, na rantse da Allah darajar Mama kakeci da yau saidai kasan nayi, dan rainin wayau kawai."
Tsayawa yayi da shan tea din ya kalleta, "Ke nine dan rainin wayau? Sakinah wallahi baki da kunya." Sai duk sukaji abun wani banbarakwai, dan bai taba kiran sunanta ba.
"Ance dan rainin wayon, kai ba dan rainin wayon bane? Dallah malam ni kayi kagama inada abunyi." Tana fadin haka ta runtse idanta hade da langabar dakai jikin hannun kujerar.
***
Kamar a mafarki Sakinah take jin ana mata magana kasa kasa "Sakinah ki tashi ki gyara jikinki, fitsari har kusan bakin kofa fah." Idanunta rufe suke, amma bata san lokacin da hawaye suka fara gangaro mata ba, tanano inda take da kuma wadanda take tare dasu.
A hankali take bude idanunta, gudun kar tayi gamo da fuskokin da batada bukata, tar ta bude idanunta a kan fuskar Arhaan, with amusement painted on every nook and cranny Of his face. Tsam tayi sai taji jikinta baa jike yake ba, dan tabawa tayi saboda ta kara tabbatar wa, amma still babu alamun fitsarin. Sai a lokacin ta tuna kwana tayi saman kujera tana jiran Arhaan ya gama shan tea ta ajiye cup din. Kallonshi tayi a karo na biyu, sai kawai ya fashe da wata irin dariya, a haka ma wai yana daurewa gudun karya tada Mama, tunda gari bai ida wayewa ba, dan ko lokacin sallah baiyi ba.
"Kam balai na rantse da girman Allah bashi kaci. Nidai kayiwa wannan abun ko? Zaka gane kurenka." Wata kwafa tayi wadda saida Arhaan yajita har cikin jikinshi, dan she sounded determined, sai ta rama din.
"What's my fault a ciki kuma? Na tadaki cikin mutunci kinki tashi, so I remembered that masu fitsarin kwance idan aka tashe su akace sunyi amalala sunfi saurin tashi, that's why na miki haka." Dariya yake yana bata amsa, harga Allah yadda ta farka da kuka ba karamin enjoying abun yayi ba.
"Wallahi zakayi bayani, kuma mantawa kayi ba amalala ba amalalo, kai bari ma ka gani," Ko ita bata gama registering actions dinta ba kawai taga ta mike ta bugar mashi guiwowi cike da mugunta, wata irin muguwar kara ya saki wadda dole Mama ta farka ta gansu tsaye, Sakinah tana kallonshi shi kuma ya runtse ido cike da azaba.
"Subhanallah Sakinah meya faru?" Mama ta furta da murya ta masu bacci.
A hankali Sakinah ta juyo, gudun ace Mama taga abunda ya faru, "Wallahi fa Mama, tun cikin dare naji yana magana sai na farka yace na hada mashi tea, to dana bashi shine har nayi bacci saman chair dinnan, ina cikin baccin naji yana nishin masu ciwo, na dan taba kafar naji ko ita ce shine ya fasa kara." Har wani kalailaye murya tayi, ga Idanuwanta dake emoting sheer innocence. Dukda Mama taji tausayin irin halin da Arhaan yake ciki, amma hakan bai hana wani irin farin ciki mamaye zuciyarta ba, dan kuwa wata kima da mutuncin Sakinah ne suka cika mata ido.
"Wayyo sannu kinji nagode, meyasa baki tadani ba? Ai da kinyi bacci kema," Mama ta furta tana saukowa daga kan katifar.
"Lah Mama gani nayi kinsha gajiyar hanya, kuma wallahi ba wani abu, ai na samu baccin."
"Sannu kinji? Nagode maki kwarai da gaske. Bari naje nayi alwalla nai sallah, kema sai ki shiga tunda ga toilet nan, anjima kadan sai mu kira doctor yazo ya duba shi." Mama na fadin haka ta kalli inda Arhaan yake kwance da idanu rufe gam kafin ta wuce toilet din.
Saida yaji Mama ta shiga toilet din kafin ya bude idanunshi ya sauke su akan Sakinah, wacce babu abunda takeyi banda dariya mara sauti. Wani tukukin bakin ciki yaji ya tsaya mashi a rai.
"Yadai dan Mama? Naga ka wani tsaya kana kallona," Hakkun bil maalum dariya take mashi, dan yadda ya fasa wata kara kamar wani yaro shi yafi bata dariya.
"Kisa a ranki bashi kika dauka, wallahi wannan dariyar saita zaman maki kuka." Maimakon ta bashi amsa sai ta kara danna kafar, amma baikai da karfin na dazu ba.
Ganin kallon dayake mata yasa ta sakar mashi murmushi, "Allah ya isa is very easy, ka furta tun kafin ta kasheka, kuma this is just the beginning, ka shirya shan bakar azaba in gaya maka. Sannan indai kai shagwababbe ne to zaka fadawa Mama da Aunty Halima." Tana sauke numfashi sai Mama fito daga toilet din.
"Ah Arhaan ka farka?" Mama ta tambaya tana karasowa inda suke.
"Eh mama kina shiga ya farka. Yanzu shi bazaiyi sallah ba toh?" Ta tambaya innocently, tana jifanshi da kallo me cike da tausayi, har ya bude baki zaiyi magana ta girgiza mashi kai, dan dole ya dauke kai, amma ya dauki aniyar takura ma yarinyar nan har sai ranar data bar gidan.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...