BABI NA TALATIN DA BAKWAI

1.5K 206 19
                                    

Kamar wasa, haka Sakinah taga Aunty Halima tana swerving steering wheel din motar ta cikin unguwarsu, ihu kawai ne bata zumduma ba lokacin daga gansu a kofar gidan, tasan tabbas ita ta musu kwatancen gida tun suna gidan Aunty Halima, amma she hadn't thought about what coming back home would cause on her, the repercussions.

Mama ce ta juyo daga seat din da take name zaman banza tana jifanta da soothing smile, yadda taha Sakinah tayi freaking out abun ya bata tausayi sannan kuma ya kara mata kaimi akan abunda take da niyyar aikatawa, shi jihadi basai kaje filin yaki ba, da bakinka ma da duk abunda Allah ya hore maka kana iya yi. Fidda musulmi cikin wani iftila'i ba karamar fa'ida gareshi ba.

"Sakinah you need not to freak out kinji? Ba gidanku bane ba? You were born and grownup here, babu abunda zai sameki kinji? Sannan kuma...." before she could finish her sentence Sakinah's waterworks had begun, kuka take cike da fargaba da tsoron abunda zata riska cikin gidan nan, kwana fa tayi a waje! Without a tangible reason! She left Inna's awara at bay, ta tafi yawon gantalinta wanda yaja mata saukar dukkan wani bakin ciki na rayuwar ta.

Mama da Aunty Halima fitowa sukayi suka zagayo bayan, patting bayanta Mana takeyi before she spoke. "Sakinah ki saurare, nasan what you're going through is a pain that can never be erased in your life. Amma you need to be good at pretense, especially yanzu da you have to pretend ko da na thirty minutes ne. Duk abunda kikaji na fadawa mamanki karki nuna ba haka akayi ba kinaji na? Be brave, I need you alive."

Da lallashi da ban baki haka Mama da Aunty Halima suka samu suka fitar da Sakinah daga cikin motar nan, tafiya suke dakyar dan har yanzu azaba takeji ta ko ina a fadin jikinta. Sunzo zasu shiga zauren gidansu ne Aunty Halima ta saka mata kudi cikin hannunta, tasan duk yana daga cikin plan din da sukace shiyasa bata tanka ba ta kara damke kudin a hannunta.

Behold! Suna shiga gidan suka iske Inna tsakar gida ta inda take shiga ba tanan take fita ba, masifa ce take zazzaga ma Baba kamar zata ci shi danya akan dole sai ya tashi ya shiga gari neman Sakinah. Sakinah najin an ambaci sunanta nan take cikinta ya tsinke.

"Na rantse da Allah zama be ganka ba cikin gidan nan, inba sakaran namiji ba ta ina zakayi sototo ka zauna wai kai ala dole cikin damuwa kake alhalin yarka bata kwana gida ba, itama shegiya gantalallar banza, wallahi idona idon Sakinah kila saida yan sanda su ansheta, ni zata jama abun kunya cikin unguwa? Ace wai har yan yara sunga lokacin da saurayi ya dauketa a mota? Gidan uwarwa taje? Na rantse da Allah...." Inna bata ida kaiwa aya ba right leg din Sakinah stepped into the house, all shaking.

"Zo nan dan ubanki! Gidan ubanwa kikaje kika kwana? Wane dan iska ne Lantana tace man ya daukeki cikin mota kun tafi har da kwana waje? Ke gaki kin zama karuwar gida ko? Na rantse da Allah yau cikin biyu za'ayi daya, ko dai masu wankan gawa su ansheki hannu na ko kuma yan sanda dan su mika ki wajen malaman asibiti dan ubanki!" Kukan kura tayo tayi kanta amma cikin ikon Allah Mama ta shiga tsakanin su, Inna masifa kawai take amma bata lura dasu Mama dake tsaye suna kallonsu ba sai da Mama tayi nata shamaki da Sakinah.

Kallo ta bisu dashi sosai taga alamun kudi daure saman jikinsu da kuma fatarsu, hakan yasa ta washe gonar bakinta yadda kasan ba ita bace me kumfar baki tana masifa ba. "A'a ha, baki mukayi? Barkanku da zuwa, ku rabu da wannan shegiyar yarinyar zata gane kurenta daga baya. Ku shigo dan Allah, kai Audu tashi ka basu tabarmar mana, kayi zaune tubus." Dayake tun saurayi da budurwa Inna take kiran Baba Audu instead of tace mashi Abdullahi ko Abdul.

Kanshi a duke dan wata irin kunyarsu yaji, duk sunyi witnessing abunda ya faru tsakaninshi da Inna sannan kuma Inna da Sakinah. Har yazo zai fita sai Mama ta tsaida shi. "Aa kaima da ka dawo, dan maganar da mukazo da ita tana bukatar mahaifinta." Ganin yanayin gidan da kuma halayyar da Inna ta nuna cikin yan mintunan da suke gidan yasa Mama taji duk duniya babu abunda take bukata face da fitar da Sakinah cikin halin da take ciki. Ita bataki su daura auren yanzu ba ta tafi da Sakinah abuja.

Zama sukayi saman tabarmar su duka, shi kuma Baba ya dauko kujera ya zauna nesa dasu. Bayan an gama gaisawa ne Mama ta bude baki ta fara bayani, ita dai Aunty Halima iyakar ta kallo, dan kuwa sai yanzu take kara yadda da points din da Mama ta kawo mata akan aurarwa Arhaan Sakinah a lokacin da take tunanin shawarar ba me bullewa bace, Allah ya basu ikon cimma burin nan.

"Kamar yadda kuka gani, tare muke da Sakinah. Wannan itace matar da Sakinah tayiwa aiki. Ni kuma mahaifiyarta ce. Sakinah ba wani wajen banza taje ta kwana ba, hasalima Halima ce ta kirata domin ta kai mata awara gidanta, yaran da akace miki yazo ya dauketa kuma kanin Halimar ne, ni kuma da na. Amma dan Allah kiyi hakuri, dalilin rashin dawowarta motar ce ta lalace sai yau aka gyara, mu kuma muna tsoron ta hau abun hawa dan yanzu mutane basu da tsoron Allah. Kuyi hakuri dan Allah."

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Inna ta sauke kafin ta kallesu cikeda girmamawa, "Babu komai wallahi, mungode sosai da kulawar da kuka bata. Allah ya bar zumunci."

Gyara zama Mama tayi kafin ta maida hankalinta a kan Baba, "Sai kuma wata bukata da nazo da ita, nasan dai ba haka akeyi ba, amma hausawa sunce a bari ya huce shike kawo rabon wani, to ina neman ma wani da'na auren Sakinah, ina fatan ba'a rigamu ba. In mun kammala magana nanda sati maza zasuzo insha Allahu a tsaida magana."

Ba Sakinah kadai ba, harta Inna saida yan cikinta suka kada. Su kuma wadannan mutanen haka Allah ya yisu? Wannan wane irin karamci ne fisabilillahi? Sakinah kallon Mama da Aunty Halima takeyi kamar idanta zai fito waje, wannan shine dalilin dayasa sukace kar tayi objecting ma duk abunda sukace? Ita Mama yanzu waye zata aura mata? She trusts Mama, tasan bazata kaita inda zata wahala ko ta wulakanta ba, tasan tabbas bai wuce me gadin gidansu ko wani me yi masu hidima, amma Sakinah deep down knew Mama ta yarda da hankalinshi sai yasa ta yarda ta aura mata shi.

Numfashi Baba ya sauke sai ya kalli Sakinah, dan kwata kwata bai bi ta Inna ba, yasan yadda taga alamar kudi jikin matan nan ai ta yarda ta gama, idan ma yace bai yarda ba to za'ayi ruwa ne da kankara. Kallon Sakinah yakeyi kallo me cike da tambaya, tambayarta yake miye ra'ayinta kafin ta tofa albarkacin bakinshi a lamarin?

Sakinah wani irin yawu ta hadiya, jikinta ko ina rawa yake, tama rasa abunda zata fara tunani, ta gane kallon da Baba yake mata, he needs her approval even with a single nod, but she couldn't. Aure fah, auren ma batasan waye ba, auren kuma bai tashi zuwa ba sai a day after she was being stripped off her dignity. Hawaye taji sun taho mata amma she remembered Mama tace she should pretend well, juya fuskar ta tayi tana kallon Mama, a hankali Mama ta daga mata kai alamar tace yes, she should trust her choice.

Rufe ido tayi ta maida hawayenta ciki kafin ta kalli Baba, carving the most painful smile she can ever, daga kanta tayi alamar ta amince, and it was a seal. Gabanta suka gama maganar komai da Mama, a gaban idanta Mama ta dauko rafar kudi wanda take ganin kaman 50k ta ajiye saman tabarmar wai kudin nagani inaso, lallai wannan ko waye yayi sa'ar boss dan kuwa ta lura Mama auren gata zata ma ko waye wannan ma'aikacin nata.

A gabanta Inna taita washe hakora har ta rakasu bakin kofa inda Mama ta kara jaddada masu cewar lallai fa nan da kwana biyar maza zasuzo da kayan saka rana suyi tambaya suyi komai kuma dan Allah batasan a saka bikin da tsawo, dan ko tsinke bataso a kaiwa Sakinah, ta dauki nauyin komai da komai na bikin. Baki me naci ban baka ba, haka Inna taita murna kamar ta mayar da Mama ciki.

Suna tafiya Sakinah ta mikawa Inna kudin tace ga kudin awarar ta nan, kafin ta mike ta shige dakinsu. Kuka takeyi kamar ranta ya fita, tasan Mama did what she did because she wanted her to have a better life, a life devoid of pain and tears, amma Sakinah couldn't help but feel like an being sold out ko kamar wadda aka bawa sadaka.

Kamar yadda Mama tayi alkawari haka bayan kwana biyar maza sukazo, itadai Sakinah jinsu kawai take daga daki, san gani take kwata kwata abun nan ba mai yiwuwa bane. A kan kunnenta suka saka ranar aurenta; nanda wata daya, a wata dayan ma dan Baba ya dage ne da basuki after two weeks su dawo ba. Idanu kawai ta rufe daidai lokacin da hawaye sukayi washing down her cheeks.




Ko ya akayi ko kuma za'ayi da Arhaan?

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now