BABI NA TALATIN DA BIYAR

1.5K 209 26
                                    

Kallonsu take tana girgiza kai, ko dan hawayen dake cascading down her cheeks she might be lucky ta samu su rabu da ita. Wanda ya dauko ta take kallo, amma lips din Sakinah sun kasa furta kalma daya da zaisa suji tausayinta. Wayyo Allahn ta, yanzu ita wannan itace kaddarar ta? Ina zata saka ranta?

Ganin da tayi daya ya nufota gashi yana niyar dage maka sutura yasa tayi wani gunjin kuka, zuciyarta har harbawa take kamar ranta zai fita. Dama haka bakin ciki yake? Haka kunci da rashin sanin madafa suke? All her life she thought she had seen all, the pain of life and everything. Amma how she knew she's hopeless today yasa tasan cewa duk wancan abubuwan na baya labari ne, this is the real deal.

"Ka taimaka man, dan Allah karku cutar dani, ba haka mukayi dakai ba." Kuka take can cikin ranta, dan voice dinta ma bawai fita yake sosai ba, amma tana addu'ar Allah yasa ko daya daga cikinsu ne yaji tausayinta.

"Ba ice cream kike so ba? Zamu biya asai maki yan mata. Ki bari kawai yanzu ayi agama, baifi five minutes zamuyi ba fah, ba dadewa abun ai." Cikin kwayar idonta yake kallonta har yayi nasarar dage mata skirt zuwa saman cibiyarta. Data nemi ta ishesu da ihu dan kwalin kanta suka cira suka kulle mata baki dashi, tanaji tana gani haka saurayin nan da friends dinshi uku sukayi raping dinta.

Hawaye kawai ke zuba daga idanunta, kwayar idan kuma tana kallon a starless sky wanda babu ko hasken farin wata a cikinshi. Wani irin bakin ciki ne da kunci taji ya dabaibaye mata zuciya har babu inda take tunani zata ita saka ranta. Da fingers of anguish were slowly caressing her whole body and it felt like the caress of fire.

Da kansu suka mayar mata da skirt dinta yadda yake, da kansu suka tayar da ita tsaye ba tare da sun sake ko da kallon fuskarta ba, da hannu daya suka rikota har cikin mota sannan suka tada motar suka koma cikin gari. A hankali Sakinah ta kwantar da kanta saman glass din motar, motsin kirki ma kasa yinshi tayi, hawaye kuwa silli silli haka suke bin idanunta amma ko kokarin sharesu batayi ba.

Hayaniya sukeyi cikin motar me cike da nishadi da walwala. Who wouldn't rejoice deflowering a beautiful virgin like her? Da sautin muryoyinsu dana wakar da suke bi ya isheta sai ta runtse idanunta, amma har can kasan bargonta take jiyo sautinsu. Kwata kwata bakin ciki bai da dadi.

Bata ankara ba taji sun tsayar da mota and before she took in her surroundings taji sun jefar da ita. Tana kallo suka tada motar suka tafi, leaving her with a souvenir of dust. Ita yanzu ya zatayi? Ina zata saka ranta? Wace irin rayuwa ce wannan ta tsoma kanta? Wannan itace kaddarar ta? Irin kaddarar da kowane bawa akwai tashi a rubuce? Irin kaddarar da ko a mafarki bata taba tunanin zata sameta ba? Dama haka duniyar take cike da marasa imani da marasa tausayi? Dama akwai abunda yafi bakin cikinnda Inna take cusa mata kauna da zafi?

Dukda batada abun dubawa, tasan dare yayi, daren kuma na sosai bawai farkon dare ba. Sanyin da taji yana yawo da jikakkiyar hijab dinta ya tabbatar mata da cewar tsakar dare yayi. Babu abunda zaija mata komawa gida, tasan Inna sai ta kusan halakata da duka, Ya T kuma wallahi sareta kawai zaiyi kowa ya huta. Inama ace zatafa Habibah? Inama ace zata ganta ta rungume ta tace mata dukkanin abun nan mafarki ne? Bata rasa budurcinta a bakin titi ba cikin dajin bayan gari ba, bata rasa budurcinta ga wadanda ba muharramanta ba, bata rasa budurcinta tana me kuka da tsananin bakin ciki ba, bata rasa budurcinta tana me hango irin kumcin da yake jiranta ba nan gaba.

Rumfar wani shago ta hango, da kyar ta lallaba ta isa gurin ta zaune, nan take kukan ya dawo mata sabo, kuncin da bai tafi ba kuwa ya dawo kamar an rura wuta cikin dajin da babu komai face itace, itacen ma busassu. Zuciyarta takeji a hankali tana transforming tana zama dutse wanda a yadda takeji ko zaa shekara fasa dusten nan bazai fasu ba. Kuka take har tana ciccijewa, ga wani wahalallen zazzabi daya rufeta kamar yadda bakin ciki yayi ma ruhinta dabaibayi.

Saman dakalin shagon ta shingida ta huta, dan kuwa zafin zazzabi bai bari ta motsa koda dan yatsa ba, a haka wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, baccin da ko a cikinshi babu wani abu mai dadi face kunci bakin ciki da tarin takaici.

Habibah tana zaune dakinta kamar yadda ta saba duk dare tana bitar littatafan da Saheer ya bata, kasan ranta damuwa ce fal a ciki amma ita har yau bata san me yake damunta ba. Duk wani abu na duniya ta sameshi, ga Momma da kullun yanzu tare ma suke kwana tsabar yadda shedan yayi galaba a kan Habibah.

Kofar taji an bude a hankali, da sallama saman labbanshi ya shigo yana jifanta da murmushi, komai na Habibah na burgeshi, natsuwarta da kamun kanta abun wuya ne a sameshi a sauran yan matan garin nan, yanzu da yan mata nagari sukayi wuyar samu.

Karasowa yayi ya zauna saman kujerar dake facing dinta "Malama Beebah, haka naji Momma na kiranki ko?" Yayi murmushi, Habibah mayar mishi da murmushin tayi kafin ta tattara books din ta aje gefenta tana maido da attention dinta kanshi.

"Shopping nakeso ki rakani, Momma taman list din abubuwan da babu, kema nasan bazaki rasa abunda zaki siya ba." Babu gardama ta mike tsaye, dama cikin gown take me kyau gyale kawai ta yafa saman shoulders dinta ta saka takalmi kafin suka kama hanya. Saida sukayi siyayyar komai suka fito har sun kusa gida Saheer ya tuna da abu yasha U-turn suka koma cikin gari.

"Dan gayu mantuwa kayi?" Ta tambayeshi tana garema garin kallo, tanaji a ranta bata saba irin wannan yawon ba a rayuwar da tayi a baya, amma sam bata iya tuna yadda tayita.

"Kayan dinkin da Momma ta bada akai maki shine tailor din yace in karba yau, amma na manta."

"Baka ganin dare yayi? Minutes to 1am fah, munyi wasting time a cinema kasan. Nasan ya rufe ma ai."

"Karki damu ai kullum shagon a cike yake da mutane, bai zama lallai ba." Daga nan babu wanda ya kara magana cikinsu, dama dagashi har ita bawai san magana ne dasu ba.

Sunje wajen shagon suka ganshi a rufe amma ga wata budurwa nan kwance saman dakalin shagon, da alama bacci take. Babu juyin duniyar da Habibah batayi ba akan ya barta taje taji idan lafiya amma yace yanzu mutane babu tabbas, kila ma sun hada kai da wasu mugaye tana fita zasu fito, karshe ma sai yayi saurin barin layin.

Sanyin asuba shi yayi nasarar tayar da Sakinah daga baccin wahalar da takeyi, tana bude ido wani dafin bakin ciki ya harbi zuciyarta nan take hawayenta suka soma zuba kamar an bude tap. Da gaske a waje ta kwana, wajen ma a bakin shagon da batasan na menene ba, ganin sayran yadikan dinkin da aka yadda yasa ta gane shagon dinki ne.

Bakin titi ta nufa tana sauke numfashi, dakyar ta samu machine ta hau ta mishi kwatancen gidan Aunty Halima, dan ta lura kusa da unguwarsu ne. Batasan meyasa zuciyarta ke fada mata taje can ba, amma duk fadin garin kaduna bayan gidansu bata da inda zata inba can ba. Gidansu kuma is a no go area.

Bakin gate din ya ajeta, cikin kudin da take cusawa cikin bra dinta ta fiddo ta bashi kafin ta kwankwasa gate din. Mai gadi na budewa ya ganta ya fara murmushi, dama wataran suyi tsiya suyi dadi da Sakinah. Bata jira sun gaisa ba tayi ciki, ta kofar baya tabi dan tasan basa kulleta, tana bude kofar idanunta suka sauka akan na Aunty Halima wadda kallo daya zaka mata ka hango baccin dake tattare da ita.

"Innalillahi! Sakinah ke ce?!" Hannunta saman kirji take kallon Sakinah kamar taga aljana.

Sakinah sulalewa tayi a kasa tana wani gunjin kuka "Sun cuceni Auntynmu, sun lalata ni. Na shiga ukku!" Kuka take kamar ranta zai fita, da hanzari Aunty Halima tayi hugging dinta tana lallashinta. Ganin kukan Sakinah bazai kare ba yasa ta jata har dakinta, kwantar da ita tayi saman gado cike da rarrashi.

"Sakinah kiyi hakuri dan Allah, kiyi shiru kinji? Ni ban gane me kike nufi ba, naji jikinki akwai zafi sosai, bari in kawo lemu kisha sai kisha magani. In kika samu bacci anjima sai muyi magana kinji? Yi shiru." Haka akayi kuwa, bayan Sakinah tasa maganin ne tayi kwance amma har zuwa lokacin hawaye basu daina fita daga idanunta ba. Saukar zazzabin ne yazo mata da wani nannauyan bacci.

Arhaan ya shigo dakin Aunty Halima da sallamarshi da niyar yi mata sallamar zuwa aiki kamar yadda ya saba sai yaga mutum kwance harda lulluba. Shidai har wajen 11pm jiya yana cikin gidan, yasan basuyi bakuwa ba, amma kuma wannan tabbas ba jikin Aunty Halima bane. A hankali ya fara takawa har ya isa gaban fuskar mai barcin.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now