BABI NA SHA BAKWAI

1.6K 259 18
                                    

Ganin dai ya tsaya yana kallon yadda kafarshi ta baci, wanda dalilin ganyen flower dinne da suka jike da ruwa_Sakeena ji tayi kamar tayi vanishing a wajen; dan she couldn't risk looking_dan batasan da wane zakin zata hadu ba. Ita harma ta fitar da rai yau kafin tabar gidannan sai an mata dukan da bazata iya tashi ba.

Wata iska ya furzar daga bakinshi, sai a lokacin ya dan fara motsar da yatsun kafar danjin ko suna motsi ko kuma akasin hakan.

Something gnawed at her instinct; hakan ya tilasta mata dagowa domin taga waye me wadannan yatsu. Alas! Tana dagowa tayi kacibus da fuskar infuriated Arhaan_he was just staring at her as if his orbs would fall down any minute from now; without a blink.

Daga duken da take ta mike; hada da sakin wani siririn tsaki irin 'Dama kaine na tsaya bata lokaci na?' Tsaye ta mike wanwar hade da kakkabe doguwar rigarta; kafin ta dubeshi da raini. "Wai dama kaine? Wallahi dana san kaine bazan tsaya bata lokaci na har ina tsoron wa na zubawa shara ba," ta furta cike da raini putting her hands at akimbo.

Kallonta kawai ya tsaya yi, dan ya gama cika fal da ita! Wato tsabar iskanci ma da tasan shine bazata duka a tsorace ba ko? Lallai duk inda yake tunanin rainin yarinyar nan ya wuce nan. Wato she wasn't remorseful akan abunda ta mashi; rather, she was regretting for ever being afraid that it was someone else not him! Gaskiya level din rainin wayonta yakai.

Sakinah ganin ya tsaya kawai ma ya kasa magana ya bata kofar kara jeho mashi magana san ranta. "Wai ni yaushe ma ka dawo? Dan I can't remember seeing you in this house for two days ko fi ma. Allah bakaji yadda gidan...," bata ida magana ba ya wanketa da wani gigitaccen marin da saida tayi taga taga kamar zata fadi.

His eyes had already turned to bloodshot, duk abubuwan da take mashi bai taba jin bacin rai irin na yau ba_ta kaishi makura. Dagowar da zatayi cike da masifa ya kara zabga mata wani ta left side dinta_har wani huci yake kamar wani zaki. Ko shi kanshi bai taba ganin irin wannan bacin ran nashi ba.

"Ni tsaran wasanki ne? You threw something on me and even uttering stupid words at me? How dare you! Ke kinsan koni wanene kuwa? Idan baki wasa ba wallahi sai na saka an batar dake daga kasar nan!" Har kasan ranshi yakejin kunar abunda ta mashi. Shi bawai zuba sharar ba, Aa maganganun data fada after realizing it was him.

Sakinah dafe kuncinta kawai tayi ta tsaya tana kallonshi, tunda take ko Ya T bai taba mata irin wannan marin ba, wanda inma dabanci ne Arhaan jariri ne wajenshi. Zafin marukan takeji har cikin kwakwalwarta; hakan ya talista wasu anguish tears sauka bisa kuncinta. Kallonshi take without blinking an eye; irin kallon nan na how dare you? Kallo me cike da rashin gasgatawa.

Arhaan ganin ta tsaya tana kallonshi kawai; dukda bakin cikin dake addabar zuciyarshi hakan bai hana shi sakin wani siririn triumphant smile ba hade da turning on his heels da niyar wucewa bangarenshi. Wata wawar damkar da aka kawowa hannunshi ce ta tsaidashi, kamar statue haka ya tsaya yana kallonta tana rike da hannunshi tamau har ta karaso gabanshi.

She was crying amma hakan bai boye jarumtakarta da determination on what she intended to do ba. Tana ganin irin kallon da yake mata na tsananin mamaki amma hakan babu abunda yayi mata banda karin kaimi. Cak ta tsaya gabanshi kafin tayi wurgi da hannun nashi, wanda koda ta rikeshi bata iya zagaye dukan hannun ba.

"Ka bani hakuri!" Abunda ta furta kenan tana me kallonshi ido cikin ido. Hawayen ma da suke fitowa da karfi da yaji ta hana saukarsu saman kuncinta.

"What? Are you insane or what? Zaki bani waje ko sai na balla ki a wajen!" He yelled, trying to push her aside; which she swiftly flinged his hand on the air.

"Ka kama kanka! Nace ka kama kanka Arhaan! Bari ganin nazo ina aiki gidan yayarka kayi tunanin duk wata sharar iskancinka zaka sauketa a kaina; wallahi na wuce nan kuma nafi karfin nan, karfi kuma na har abada. Zamana talaka wacce take neman halal dinta a karkashin yaruwarka bazai baka damar mayar dani jaka ba, kayi na farko na nuna maka ban damu ba_to wallahi I won't take this easy with you.

Kai bari kaji, na rantse da Allah ko ka bani hakuri ko yau mu kwashi yan kallo dakai! Bar ganinka gardi haka; karfi ba a jiki yake ba a zuciya yake! Kuma yadda ka kaini karshen nan zan iya babbalaka cikin gidan nan.

Dan haka; idan kana san zaman lafiya, na rantse da Allah ka bani hakurin marukan nan, sannan kar kayi gigin kara saka hannu ko dungirina kayi balle har ta kaiga mari ko duka. Idan ba haka, wallahi zaman gidan nan sai ya gagareka_because I will not take it lightly with you!!!" Cike da hargagi da huci take sauke wadannan kalaman, muryarta har wani karshashi tayi kamar ta maza; ido cikin ido yake kallonta amma Sakinah ko gezau; she was so fed up.

Bai jira ta ajiye numfashin ba ya kara zabga mata wani marin da yasa dole ta duk'e; har wani bakaken stars ta rika gani cikin idanuwanta. Cike da huci da tsananin bacin rai ya fara magana da muryar da bai taba tunanin shi ke da ita ba.

"Kinyi kadan na kalleki na baki hakuri, kaskantacciya dake. Idan har kinfi karfin duka ko mari kibar gidan muga idan zaki iya. Kuma da kike cewa zamu kwashi yan kallo, kiyi rephrasing maganarki_rather kice; zaki samu yan ceto_dan wallahi yau idan baki wasa ba mai kwatarki sai Allah. Banza, wawiya, jahila wacce bata da kamun kai batasan ciwon kanta ba!" Yana fadin haka ya saka kafa yayi ball da ita kafin ya wuce; amma abunda ya daure mashi kai shine jin da yayi an kama kafafunshi tamau an rike ko jijiyoyin kafar sun kasa motsi.

Wata irin wawiyar mikewa tayi hade da saita hannunta daidai left cheek dinshi da niyar zabga mashi mari taji an kira sunanta da wata irin murya.
"Sakinah!!!" Ya furta da karfin gaske yana karasowa inda Arhaan; wanda ya kasa motsi yake tsaye.

Baban Shaheed bai jira wata magana ba ya wanke Sakinah da marin da saida hawaye suka zubo mata. "Baki da hankali?! Yanzu da ban zo ba saiki daga filthy hand dinki ki mareshi? Ke wace irin jahilar yarinya ce?!" He clamoured, yana tunkudeta har saida ta fadi guiwar hannunta ta fashe.

Wata irin kara ta saki wacce ta janyo hankalin yan gidan hade da Aunty Halima suka fito harabar gidan. Cikin hanzari Aunty Halima tayi wajenta tana tambayar ko lafiya; ga jini sai zuba yake daga hannunta_dan ba karamar yankewa tayi da karfen data buga ba.

"Mena fada maki kan wannan kaskantacciyar? Mena ce maki? Ba wataran har ke sai ta nuna ma yatsa ba? To yau Arhaan ta daga hannu zata mara!" Baban Shaheed ya fada cike da fushi, shi dama can ya tsani yarinyar, yau kuma she give him more reason to hate her.

A razane Aunty Halima ta kalli Arhaan, amma ganin yama kasa magana kawai ta tabbatar da instincts dinta; kallon Sakinah tayi cike da bacin rai "Sakinah mena fada maki ranar game da Arhaan? Yanzu har rashin kunyar da rashin mutuncin naki yakai nan? Ke yanzu idan aka barki da Arhaan basai ya babballa duk wani kashi dake gangar jikinki ba?" Ganin fushi sadidan saman fuskarta yasa cikin Sakinah durar ruwa; dan dama she was the only one takeda hope on zata iya karbarta.

"Aunty...," ai bata ida maganar ba Aunty Halima ta daka mata wata gigitattar tsawa.

"Bace man da gani, kuma ki jirani a dakinki!" Tana fadin haka kafin ta juya suka nemi Arhaan suka rasa. Tasan yana dakinshi, dan haka batayi gigin binshi ba_domin bai taba nuna irin wannan fushin ba a rayuwarshi sai sau daya_shima that was when Baba yama Mama fada a gabanshi.

Arhaan kuwa yana shiga daki ya kulle ya zauna kan kajera; tunaninshi daya da ace Baban Shaheed baizo ba yarinyar nan da marinshi zatayi? Dan shi rayuwarshi, ko a gidansu dama Muhibbah ce mara kunyar_amma karshen iskancinta wajenshi baifi kunkuni ba_ko magana bata taba fada mashi ba. Sai yau shi yar aiki zata daga hannu tace zata mara!

***

Tun daga wannan lokacin babu wanda ya kara ma wani magana cikin gidan har lokacin bacci yayi kowa ya tafi ya kwanta. Amma sam Aunty Halima hankalinta ya kasa kwanciya, dan tasan dole ta amsa query wajen Mama; ga Baban Shaheed shima tasan shirun nan bana banza bane.

Sai gabanin sallar asuba ta samu bacci ya dauketa. Kamar a mafarki ta jiyo muryar Baban Shaheed yana rangada mata kira, a dan gajiye ta mike ta nufi falo inda ta nan take jiyo sautin muryar tashi na tashi.

Shi kuwa Baban Shaheed daya tashi sallar asuba sai ya biyo ta falon daukar takardun daya manta jiya; dan yadda idan zai dawo masallaci basai ya biyo ta bangaren su ba. Amma yana shigowa yaji wani irin zaurin fitsari na tashi_wanda da alama lokacin ake yinshi ko baafi minti biyar da gamasa ba.

Lekawa yayi ko ina amma bai gano daga inda abun ke fitowa ba, hakan yasa ya shiga dakin inverter_anan ya hango Sakinah kwance male-male cikin fitsarin kwancen. Wanda silar bacin ran data shiga jiya ne yasa ta manta bata shimfida ledar fitsarinta ba.






I think I should go on writers block, tunda baku commenting😭💔

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now