Masifa ke cinta, zaune take kan gadonta while Maama na kusa da ita. Duk inda ake daure fuska to Habiba takai karshen haka, har wani huci take amma still jira take taga yanda zasu kare, dan ita wallahi tunda taje India ta dawo tama kanta alkawari babu kasar da zata kara zuwa. Ta gaji da wannan rayuwar, tasan yanzu she can't remember kowa nata, amma she knows cewar kudaden dake cikin account dinta komin banza zasuyi fending for her needs kafin taga me rayuwa zata bata.
"Beeba kinga bafa wani abu bane, tace mun five mil zata baki for just one week a thailand, dan Allah karkiyi wasa da damar ki." A hankali take lallabata, dan ta lura kamar asirin da suka mata nema yake ya kwance, dan wani kafiya da taurin kai Beebar ke neman shigo mata dashi cikin lamuransu. Tunda take daukar yan mata bata taba samun yarinyar data janyo mata arziki kamar Beeba ba, sai yasa duk yadda zatayi zatayi amma bata taba bari ta kubuce mata.
Ta lura tsaf da kusancinsu da Saahir, amma ko kadan hakan bai taba tada mata hankali ba, dan ita tasan daga Saahir din har Beebar dukansu a tafin hannunta suke. Dan jiya ma ta bada aiki akan Saahir din. Ita kanta tana san yarinyar balle kuma ayi maganar dukiyar da take samu wajenta.
Shiru Habiba tayi, bawai dan kudin dataji ba ko kasar da taji sun saka ranta yayi salama, Aa saidai mamakin da take inda matan nan ke samun kudin da suke wasa dasu haka. Sai daga baya ta fuskanci cewar manyan masu kudi sukebi, idan sukabi maza suka samo kudi wajensu sai su koma kan mata su kashe masu. Wannan rayuwar ba ita bace rayuwar daya kamata ace ita, Habiba Abdullahi Bello lives, batasan su waye iyayenta ba, amma tasan basuyi deserving haka daga wajenta ba.
Mikewa tayi tsaye tana kallon window, "Maama gaskia ni babu wata kasar da zan kara zuwa, infact aure zanzo nayi I'm tired of living this dirty life. Kyamar kai na nake, kiyi hakuri amma gaskia bazanje ba." Abunda ta furta kenan kafin tayi hanyar barin wajen, wani wawan riko Maama ta mata ta maidota gabanta kafin ta faska mata mari.
Ranta in yayi dubu ya baci, har ankai stage din da Habiba zata kalli kwayar idanta tace mata ita aure xatayi? Kodai maganin mutumin can ya fara daina aiki kan yarinyar nan ne? Saboda yanda sukayi dashi ko sha'awar tayi magana da namiji bazata taba ji ba inhar ba yaruwarta mace ba. To ya haka?!
"Ke har kin isa ki kalli idona ki furta man cewar kin daina wannan rayuwar? You feel dirty of yourself? Aure zakiyi? Duka yaushe kikasan luxury din rayuwa da har zafi zabar ma kanki abunda kikeso? Karki manta ni na fiddoki daga cikin kazantartar rayuwarki na maidoki cikin daula, I gave you life!" Cikin masifa da hargagi da tsananin tashin take magana, ranta in yayi dubu ya baci, she couldn't think of a way out, gashi in two days matar take bukatar ta tura mata ita thailand din, ita yanzu ya zatayi?
Habiba bata san lokacin fara zubda hawaye ba, "I know you gave me life, but should I tell you the kind of life you gave me? It's nothing but a filthy life, rayuwa me cike da kazanta da tarin zunubai, rayuwa wacce take abar kyama, ko da ban sani nasan tabbas idan na dore akan wannan rayuwar babu abunda zai hana tayi leading dina zuwa jahannama. Maama, ki hango cewar yau danki Saahir shi ake transferring from one man to another, shine ake dauka daga wannan kasa zuwa wannan kasa ba dan komai ba sai dan yaje yayi alfasha da mazan banza? How would you feel?! Just how?!" Ko kafin ta rufe baki Maama ta kara kai mata wani marin, idanunta har sun rina sunyi ja tsabar bakin ciki da bacin rai, dan iska babu abunda ya tsana kamar ka alakanta danshi da irin abunda yakeyi, to abunda ya fara wa Maama kenan.
"Ke har kin isa ki alakanta Saahir da wannan maganar? Duka yaushe ya dauke daga cikin tsummar rayuwarki?!" Abunda Maama ta iya fadi kenan, karshe ma sai fara dukan Habiba tayi.
Habiba kuka take bawai dan tanajin zafin dukan da Maama take nata ba, Aa saidan irin kunar da zuciyarta take mata, wato ita alakanta kawai tayi da abun, amma kalli yadda matar nan ta zzagehada dukanta saboda taji zafin maganar. What of her? Ita da alfashar babu irin wacce bata aikata ba? Idan da tata mahaifiyar zataji abunda ya faru da ita sai tace me?!
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
Genel KurguLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...