Koda Mama suka koma gida dole yasa ta kara kwana dan su gana da Arhaan, tasan tabbas abunda tayi ba karamar husuma bace, shi kanshi Baba there isn't assurance cewa zai yadda da hadin auren, but that is the least of her worries in har Arhaan ya yarda to komai ma yazo gidan sauki.
Koda dare yayi suna zaune suna hira da kowa a parlor, Arhaan ne kusa da ita yana danna mata kafa cike da soyayya suna fira can kasa baby maijin abunda suke fadi inba su din ba. Kallon Aunty Halima tayi ita kuma ta mata nodding kanta alamar yes tayi kawai, the earlier the better. Riko hannun Arhaan Mama tayi ta jashi har zuwa dakin Aunty Halima, zama kan gadon Mama tayi shima Arhaan ya zauna kusa da ita. Kwanto da kanshi tayi ya zamana ya dora kanshi bisa laps dinta before she started talking, caressing her hands into his silky hair.
"I need a favor from you, Dan Mama, hope bazaka watsa man kasa a ido ba?" She spoke softly, tana kallon yadda reaction dinshi ya canja zuwa hurt. Kallonta yayi kafin ya mike zaune yana me rike da hannayenta.
"Mama it's you fa, the only woman I've loved and will ever love. Babu favor tsakaninmu, just ki fada and it shall be granted Mamana." Yana fadin haka yayi side hugging dinta, placing his head on her shoulders. Haka kawai yaji zuwan Mama ya tayar mashi da hankali wannan karan.
"To nagode Dan Mama, aure na nemar maka, na fada masu nanda kwana biyar su Baba zasuje a saka rana and all." Wata irin razana da Arhaan yayi saida ya kusan faduwa daga kan gadon, riko hannunshi tayi with so much plea in her eyes.
Cike da fargaba da tsoro yake kallonta, to see if he could catch a rope of joke a face dinta amma babu. Yes, mamansu was used to maganar yayi aure tanasan ganin dan mama, but from what he saw a face dint she's not joking. Auren ta nemar mishi da gaske. "Mama dan Allah ki daina wasa, wai ba dare yayi ba kuma kince ni zan maidaki Abuja gobe? We shall all go to bed, zan tafi saida safe." Mikewa yayi da niyyar fita, yana juyowa dan ya kara kallonta amma abunda ya gani ya sakashi zubewa saman kafafunshi sai kuka.
Mama sanin Arhaan ciki da bai, from how he reacted she knew bai yarda ba, kuma a hade sama da kasa ba yardar zaiyi ba. She knew his weaknesses, amma yau kukanta babu abunda zai ma Arhaan from the looks on his face, and she resorted to the next option in her mind, ta kai guiwowinta kasa. Yana juyowa ya ganta tayi kneeling down kawai ya zube kasa yana kuka, kiciniyar mikar da ita tsaye yake amma ya kasa.
"Mama ki taimaka ki rufa man asiri, Mama dan Allah ki tashi, wallahi ko gobe ne kikeso ayi auren na yarda, ko yanzu ma amma dan Allah ki mike haba Mama!" Kuka ringis yakeyi, Mama cikin danne farin cikinta ta mikar da kafafunfa ta zauna saman carpet din dakin shi kuma ya kwantar da kanshi saman laps dinta yana kuka.
"Ya isa haka, to kukan na miye kuma tunda gashi na zauna? Karka zama raggon namiji mana, nan da shekara daya fa jikoki na zan gani."
"Maaamaaa!" Cike da shagwaba yayi maganar, wanda hakan ba karamin sata dariya yayi ba. Tunda yayi haka tasan ya yarda, sannan kuma duk wani pertaining auren da duk wacce zai aure bazai tambaya ba amma ya aminta dasu koda kuwa wadda zata aura mashin miskiniya ko kuma tanada wata makusa.
Dakyar Mama ta samu ta lallaba shi ya tafi ya kwantar, but she knew; bawai zaiyi bacci bane dan yau. Washe gari bayan sunyi breakfast suka kama hanyar Abuja, and throughout the ride itace ke janshi da magana saida suka kusa goda kafin Mama tace "Wai Dan Mama ko sunan amaryar taka bazaka tambaya ba?"
Tabe fuska yayi yace "Kai Mama, kedai ba kin auro abunki ba? Ni ina ruwana toh, ko sunanta zuwaira ai aurenta zanyi a hakan."
Dariya sosai Mama tayi before she patted his shoulders tana cewa "Dan mama kenan, ai kai na aurowa matar bani ba. Sunanta Sakinah, na yan gayu ko? Karka wani damu, kyakyawa ce san kowa kin wanda ya rasa."
"Kin wanda ya samu san wanda ya rasa dai." Dukan da Mama takai mashi yasa ya kauce yana dariya, but still, he was scuppering the name in his mind 'Sakinah'.
•
Kamar wasa wai yau ne za'a kawo lefen Sakinah, ita kallo kawai take yadda Inna da sauran yan uwanta Iya Lami da Iya Saratu suketa kai kawo da sauran yan uwansu. Hada Maman Iliya cikin yan dafa abinci da suyar gara. Ko ina Inna ta samo kudin nan? Allahu A'alam. Burin Sakinah daya Allah yasa har ayi bikin a gama Ya T bai dawo ba, dan cikin sa'a ranar da wannan abu ya faru da ita ranar yabar garin wai ya tafi benue neman kudi.
Tun Inna bata damuwa da rashin samun Habibah da dillaliyarsu har abun ya fara damunta, kullum idan ta shigo zata iske Sakinah crumbled at the end corner din dakinsu while crying her eyes out, maganar Inna kullum shine karta dama, shi dama aure yakan zo ma kowace mace ta fanni daban ne. Kuma takan mata maganar Habiba da jimamin Allah yasa lafiyarta kalau.
Yau ya kasance saura sati daya bikin, wanda su Mama sunce karta damu da kai dinki dan har gida Aunty Halima tazo ta auna ta dan su kaiwa tailor awonta. Sati daya, kalma datafi tsayawa Sakinah rai kenan fiye da kowace kalma.
A bangaren Arhaan kuma ko da Mama ta kirashi Abuja dan kawai ta bashi katin bikin da kuma fada mashi za'a kai lefe after sati kuma amarya zata tare a gidan da Baba ya bashi baice komai ba, ko bude katin baiyi ba, illan tanbayar ta da yayi "To ni ba'a bukatar komai nawa? Ba abunda zan bada?"
"Aa auren Dan Mama fa akace, ai komai kyauta ne. Jeka kawai ka jira amaryar ka, unless kanasan wani event ne kuma sai na hada maka."
"Aa banaso, daurin auren ma ai event ne. Amma Mama basai naje ba ko? Can kadunar wai." Ya wani turbune fuska duk dan ta tausaya mashi, dan shi yanzu kwata kwata garin ya fitar mashi a rai.
"Ah zuwa Kaduna kuwa ya zama dole, me kakeso iyayenta suyi taunani, Arhaan? That mijin ba santa yake ba ko me? Zaka Kaduna insha Allahu." Baiyi gaddama ba, illa he bid her adieu and left for his apartment.
Koda ya isa daki kati daya ya dauka cikin ledar ya tura saurin kasan table din dake dakin, shi he doesn't have wasu friends balle ya bayar, bare ma wannan auren da ko a kasan rigarshi.
Kwanciya yayi saman gadonshi ya kura ma karin ido, kamar wanda aka zare ma lakka haka ya fara bude katin a hankali ya fara karantowa daga samu. Arhaan Aliyu Zubayr and Sakinah Abdullahi Bello. Kasa karanta date da wani venue yayi, rufe kati yayi ya jefar tsakar dakinshi kafin ya rufe idanunshi, shidai wallahi komai da yakeyi dan Mama yake yinshi.
Lefe ya amsa sunanshi lefe, gaba daya matan da sukazo amsar lefen kasa boye mamaki da kuma kauyancinsu sukayi, hada Aunty Halima cikin yan kawo lefe, koda zasu tafi saida ta bukaci ganin Sakinah inda taita bata baki tana kara nanata mata insha Allahu alkhairi ne.
•
Rana bata karya dama, saidai uwar diya taji kunya, kamar saukar aradu haka Sakinah tahi anata maganganu tun kafin gari ya ida wayewa, ita tama manta ana wani abu mai sunan biki a gidan, ta koma gaba daya rayuwar daki take. Ko abunda ba'aso Inna bata bata ba wai da sunan kayan mata, itama din abun bawai ya dameta bane.Amma jin yan gidansu Inna da sauran yan uwansu, dama su haka Allah yayisu bakinsu bai taba shiru; magana suke cakai cakai tun kafin a kira sallar subahi. Wani tsaki taja kafin ta tsame jikinta daga katifar ta mike tsaye dan zuwa tayi wanka, tasan ko batayi ba dole Iya Lami ko Iya Saratu sai sun sakata gaba da bakin surutu dole taje tayi. Yau batajin tanada bukatar wannan hayaniyar kusa da ita, She wants to sip in the juice of her pain alone.
Har ta fita tayo wankanta ta dawo babu wacce ta kula da ita, wanda hakan ba karamin dadi ya mata ba. Ko mai bata shafa ba ta duba cikin karamin akwatin da aka ware mata domin sakawa cikin hidimar biki ta dauka wata super ta saka ta yafa gyalenta, dama ba sallah take ba balle ta damu. Koda Sakinah taga lefen abun bai wani d'ad'a ta da kasa ba, dan tasan babu irin abunda Mama bazata iya ma ko waye mijin nata ba.
Ba irin yadda ba'ayi da ita ba akan taci abinci amma taki, karshe ma sai kuka ta saka masu, suka zageta iya yinsu suka rabu da ita nan. Bakin cikin duniya yai mata tsaye, gashi ko Habibah babu balle taji wani saukin a ranta, yau harta da kewar Ya T saida taji.
Tana nan dunkule tsakiyar katifarta taji yan karadi sun shigo, yaran Iya Lami ne wanda suke kira da Alolo, "Iya! An daura auren Sakinah! Iya kinga manyan motoci? Har angon saida na gaisa dashi, gashi fari, ga kyau, ga gashi jikinshi kamar wani balarabe..." ai Sakinah bata ida jin zancen ba ta mike zumbur, ita har ga Allah batayi tunanin har 1:30pm tayi ba.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...