Babu irin kukan da Sakina batayi ba, tasan yana jinta daga cikin dakinshi amma ko alamar ya bude kofar baiyi ba. Karshe ma bakin kofar dakin ta koma tana bugawa tana magiya akan ya bude kofar ya saurareta, babu wata kalma me tsawo dake fitowa bakinta data wuce "Mama ce shaidata." Tun tanajin alamar motsin shi cikin dakin har ta daina. Kuka kam ta sha shi har ta gode Allah, a nan bakin kofar bacci ya dauketa badan tasan yadda akayi ta fara baccin ba.
Da Asuba saidai karar fitowar shi taji, ko kafin kalma daya ta fito daga bakinta har ya tsallaketa ya fita daga gidan. Yadda ya fita da wayarshi a hannu tasan yau ma bazai sake dawowa gidan ba. Yini tayi cikin gidan nanntana kiranshi a waya amma ko sau daya baiyi mistake din dauka ba. Tayi text din har ta gaji, gashi bata taba tunanin soyayyar da take ma Arhaan tayi zurfi ba saida wannan abun ya faru har ya kaurece mata.
Wasa wasa har sunyi sati a haka, tun yana kwana cikin gidan har ya daina. Tasan babu inda zaije ya kwana daya wuce gidan Mama. Tun tana kuka har ya koma saidai ajiyar zuciya, zuciya da gangar jikinta babu inda baya mata ciwo. Ya koma iyakarta daki sai kitchen, kitchen din ma sai dare yayi take zuwa it's either taci indomie ko kuma ta hada custard. Gaba daya tayi hiri hiri kamar ba ita ba, duk yar kibar da tayi attaining da kyan skin duk tabi ta komade.
Suna cikin sati na biyu ne ranar taji motsi a falonta, cikin hanzari ko dankwali bata tsaya ta saka ba ta fita sai ta iske shi dauke da robar ruwa ga jakar kayanshi a saman kujera. Kallo daya ta mishi hawaye suka fara zarya a saman cheeks dinta, kana ganinshi kaga wanda yake cikin dunbin damuwa, amma dukda haka baiyi lalacewar da Sakina tayi ba.
Ko kallon inda take baiyi ba, amma yasan for sure tana kallonshi kuma yaji fitowarta, "Ki hada kayanki na kaiki kaduna..." wani irin dukan da kirjinta yayi sai kayi tsanmani ce mata akayi ya rasu. A hankali ta kama bangon dake gefenta ta rike, har wani jiri take gani. Sai can taji ya furta "Zanje nayi week a can, I guess you need to visit home kema." Ko jira yaga halin da take ciki baiyi ba ya dauki bag dinshi ya fita gaba daya sai taji ya bude mota.
Kamar mutum mutumi haka ta dauka madaidaicin akwatinta ta fara hada kayanta, yadda yace zaiyi sati tasan ita sai ta wuce sati gidan Inna. Hawayen ma sun daina zubowa banda kuna babu abunda kirjinta yake mata. Hijab ta saka ta dauka karamar jakarta wacce wayarta ke ciki da sauran abubuwa kafin ta fita.
Booth ta gani bude, akwatinta ta saka kafin ta rufe ta zagayo gaban motar ta shiga. Sai bayan ta shiga ne ya juyo ya kalleta, tayi wani irin fayau da ita kamar wacce babu rai a jikinta, idanunta kuwa tsabar kuka duk sun kankance, maganar kwarin jiki kam baa nemanshi wajenta.
Har suka kusa kaduna babu wanda yace da wani komai, ganin ga chance ya samu kar tayi loosing yasa ta juyo tana fuskantar shi, sai hawaye taji suna saukar mata. "Ina sanka, Arhaan." Abunda taji bakinta ya furta kenan, wani wawan burki Arhaan yaja ya tsaya kafin ya gangara dasu bakin hanya.
Ya kusa minti biyar yana analysing words dinta, bawai kuma dan baisan da zancen tana sanshin ba, Aa yanda tayi maganar ne a lokacin da bai taba tunani ba ya mugun bashi mamaki. "Idan kinada abun cewa kice, dan I have to be somewhere kafin time ya kure." Ya kalli inda take ma Sakina bata samu wannan arzikin ba.
Share hawayenta tayi, amma hakan bashi ya hana wasu zubowa ba. "Ka yarda dani Arhaan, ina sanka, sosai nake sanka wallahi. Dan Allah ka daina azabtar dani da rashin ganinka ko jin voice dinka. Arhaan ka yarda dani, bazan taba yin abunda ya saba ma addini ba, Mama ce shaidata. Ni ko bazaka yarda dani ba ka yarda ina sanka." Hannunshi ta kama zata rike ya fizge tare da juyowa yana mata wani irin mugun kallo, kuka take can can karfinta kamar ta shide.
"Idan kin gama inada abunyi." Yana fadin haka yama motar key suka cigaba da tafiya. Tun daga lokacin take kuka. Abunda yasa ta fada mashi tana sanshi bai wuce dan ta rage zugin da zuciyarta take mata ba, sai taji abunma yafi na da azaba. Dan kuwa babu abunda yakai rejection na soyayya tarwatsa duk wani farin ciki.
Tambayar unguwarsu yayi ta fada mashi, sun kusa kaiwa ya tsaya yana kallonta kafin yayi parking gefen titi. Ruwa ya miko mata ta karba ta wanke face dinta suka cigaba da tafiya. Har kofar gidan Inna ya tsaya, sai ganin Lantana sukayi ta fito guskarta a kumbure daga gani ranta a bace yake. Bata lura dasu ba tayi gaba abunta.
"Ki fitar min a mota, ko gidan naku ne baki gane ba akwai inda zan kaiki?" Mamakin rashin tausayin shi takeyi, kamar ba wannan shagwababben Arhaan din da yake very soft ba.
"Saki na kayi?" Tambayar da tayi kenan, dan ita bataga dalilin maido ta gida ba indai ba sakinta yayi ba.
"Ko zan sake ki sai Mama ta farka, shima dan bazan iya wannan hukuncin ba tare data sani ba. For now dai, ki zauna gidanku." Yana fadin hakan ya janyo wayarshi ya fara latsawa batare da ko kallon mutunci ya mata ba.
Tafi minti ashirin tana kallonshi kafin ta hadiye kukanta a hankali, dan bazata iya shiga gidan Inna tana kuka ba. It's a relief ma tunda yace bawai ya saketa bane, indai har sai yaji ta bakin Mama to tabbas bazaiyi sakin ba.
"Akwai ranar da zakayi regretting Arhaan, amma still nasan zan yafe maka kuma zan fahimce ka ba kamar yadda kai ka kasa fahimta ta ba. Duk ina alkawarin I have you in my life? Duk ina promises din you'll always be there for me? But believe me it's fine and I totally understand. Just know that, Mama ce shaidata." Fita tayi daga motar ta bude booth din ta dauki akwatinta ko kallon inda yake bata kara yi ba ta shiga gida.
Saida ya kusan five minutes kofar gidansu kafin ya wuce inda zaije. Sakina tayi mamakin irin tarbar da Inna ta mata, dan sosai suka sake suna labarin amma kuma ainun hankalinsu ya fara tashi akan rashin Biba sai kace wacce aka sace? Kamar yadda Arhaan ya fada mata cewar sati daya zaiyi itama haka ta fadawa Inna bawai dan tana da tabbacin sati dayan zatayi ba. Koda Ya T ya dawo gidan da daddare ba yabo ba fallasa suka gaisa dan har yanzu haushinta yakeji.
•
Bayan Wata Biyu
Fadin yadda rayuwa ta juya ma Sakina ma bata baki ne, tun tana kiran wayar Arhaan tana shiga har ta daina shiga. Text kuwa tayi mashi shi yafi guda dubu. Tunda sati biyu ya wuce ta koma irin zaman da takeyi a gidan Inna na da. Kuka kuwa babu irin wanda batayi ba. Inna tayi dukan tayi zagin akan ta fada mata abunda tayi mashi amma fir taki magana sai kuka.
Baba har yayi lallashin ya gaji, saboda zagin Innar kuwa har ta daina fitowa tsakar gida kullum tana daki, ta rame ta lalace. Ranar tana zaune babu abunda takeyi sai kiran wayar Arhaan tana kuka sai ga Inna ta shigo da jug a hannunta. Dukda zafin zuciya irin na Inna da kuma haushin da Sakinar take bata, can cikin zuciyarta tausayinta ne fal, dan kawai batasan ta yadda zata fara jan Sakinar a jiki ba har ta fada mata damuwarta. Duk wata magana da tsiwa ta Sakina ta kare.
"Dan ubanki tashi kizo ki ansa kisha, bazaki kashe kanki ba mijinki yazo nemanki ince kin mutu ba. Tsabar bakin hali Allah kadai yasan irin jarabar da kika mashi har ya koro ki gida." Yadda tayi tsaye a bakin kofar ya tabbatar ma Sakina jira take taje ta ansa. Dama akwai hadari kiris ya rage ayi ruwa a garin, a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka Sakina take takawa har wajen kofar dakin. Gab da zata isa iska ta daga labulen hakan yayi nasarar dage rigar Sakina cikinta ya bayyana.
Wani wawan ihu da Inna ta kurma ta yadda jug din kunun sai kayi tunanin cewar gawar Sakina ta gani a kwance. Allah yaso su babu kowa gidan saboda yamma tayi. A hanzarce Sakina ta karasa wajenta tana tambayarta ko lafiya? Ita tsoro ma ta bata.
"Ubanki lafiya shegiya yar iska. Dama Sakinah abunda kikawa Arhaan din kenan Sakina?" Wani wawan mari takai ma Sakina dan dole tayi baya ta fadi kasa sai hawaye.
Cikin tashin hankali ta fara magana, "Inna mena mashi kuma? Zuwa yayi? Yana iya naje na ganshi? Kinji Inna?" A hanzarce ta mike zatayi hanyar waje taga Arhaan din.
Finciko ta Inna tayi ta hadata da bango hade da shakareta. "Ki ganshi a gidan ubanki ko? Sakina sharri dai kike bina dashi ko Sakina? Halan cikin dake jikinshi ba nashi bane saiyasa ya maidoki gidanku dan ubanki!"
As I promised, na gama exams dita yanzu we're back.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
Ficción GeneralLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...