BABI NA SITTIN

1.7K 249 44
                                    

After sallar Isha'i ya shigo gidan his face full of smiles, direct dakin Sakinah ya shiga yaga ta zauna tayi jugum, alamar wani abu yake damunta ko kuma ta kara mafarkin nan, because she looks extremely sad duk time din da tayi mafarkin ko kuma ta tuna da abun mafarkin. Zama yayi kusa da ita saida ya riko hannunta kafin tasan cewar ya shigo dakin.

Share hawayenta tayi ta juyo tana kallonshi, a ranta tunani take yadda zata fara ma Arhaan bayani yau dinnan, batasan yadda zai dauki maganar ba. Gashi ba Mama, Aunty Halima kuwa tayi dialing number dinta yafi sau dari kila. Tasan duk wannan happiness din nasu tabbas sai ya kare daga time din da daren yau ya kare, dan yadda taga alamun shi babu mai kwatar ta hannun Arhaan.

"Anina meya faru? Ko bacci kikayi tsakanin maghrib da isha kafin na dawo kikayi mafarki?" Tambayar daya fara mata kenan kafin yayi side hugging dinta. Duk idan tana cikin wannan halin sam baya jin dadi a zuciyarshi, shi gani yake ba soyayya bace, but yasan he cares for her. Ba karamin tausayi take bashi ba, gashi kuma koda wasa bata taba yarda ta fada mashi damuwarta ba. Shi duk burinshi bai wuce ta fada mashi minene wannan abun ba, if there's a way da zai iya mata magana wallahi zaiyi.

"Aa banyi bacci ba, amma still. Arhaan I'm afraid..." sai kuma ta fashe da kuka. Burinta taga Mama, she has a lot to tell her.

"Whatever it is, ki daina saka ma ranki damuwa kinji? You have alot of important things to think about, ki daina bari damuwa tana zama cikin ranki. Ko ba komai, you have me in your life, kuma I'll always be there for you, Anina. You have Mama and your family. Duk sadda kikaji you're ready to open up, ki fada man kinji? I'll be a good listener kuma if inada possible way da zan yaye maki damuwarki zanyi."

Da magana mai dadi har tayi shiru, karshe ma cewa yayi ta tashi suje wajen Mommy an kusa three weeks basu leka ba. Shiryawa tayi suka fita. Koda sukaje  Mommy kadai suka iske a parlor su Muhibbah da Safiyya duk suna daki. Bayan sun gaisa sai Arhaan yake mata magana. "Mommy dan Allah ki kara rokar mun Baba ya barmu muje egypt dinnan, wallahi tun last two weeks visar dana mana applying ta fito, ni bansan ya yakeso nayi ba. Dakyar fa nake coping zamana nigeria yasani amma wai kiri kiri ya hanani naje." Ya karashe magana kamar zaiyi kuka, saida Sakina ta riko hannunshi a hankali alamun lallashi.

Cike da damuwa Mommy take kallonshi, "Ni kaina Arhaan mun rokeshi koda Safiyya naje yace wa zanbar wa gidan? Ga Firdausi , Khadija da Muhibbah fah amma still. Ni kaina rashin sanin halin da Mama take ciki yana damuna, gashi ko video call bai taba kira an ganta ba. Nace ya barka kaida Sakina kuje yace shima duk Aa, amma zan kara trying kaji? Adduar mu kawai take bukata for now."

Saida ta lallasheshi kafin suka mata sallama, tun kafin su isa Sakina ta fara bacci, not that baccin na gaskia ne but duk burinta bai wuce su isa ba Arhaan yayi considering ko ta gaji take bacci ko kuma damuwa ce ta mata yawa. Suna isa taji ya kashe wayar amma still bata nuna tasan sun tsaya ba. Zagayowa yayi ta side dinta ya dauketa bridal style har saida ya ajiyeta kan gadonta.

Zuciyarta faduwa take kanar ta fito, amma bata nuna mashi tasani ba. Hijab dinta ya cire mata before ya fita dakin. Tanajin ya fita tayi hanzari shigewa toilet, wani irin kuka ta fashe dashi kamar ranta zai fito. She's in between, tasan Arhaan amma kuma tana tsoron irin fadan da zasuyi da Arhaan idan har akace ya gane halin da take ciki.

Saida tayi kukanta mai isarta kafin tayi wanka tayi alwalla ta fito daga toilet din. Nightgown ta saka light purple tayi kyau sosai kafin ta dauko hijab ta fara sallah. Tanajin ya shigo dama tana sujjada sai ta fashe da kuka, babu abunda take furtawa sai Ya Allah, bama tasan me zata ce ba. Saida ya jira ta sallame kafin ya tambayeta ta tashi barcin? Nodding kanta kawai ta mishi, kafin yace ta tashi suyi sallah.

Tana binshi sallar tana kuka, ita kam yau da kasa na budewa ka shige da babu abunda zai hana ta roki Allah akan kasa ta bude ta shige shikenan babu wanda zai kara ganinta. Wata zuciyar nace mata ta fada mashi wata kuma is against it, ita gani take kamar Mama is the right person data fada mashi maganar nan.

Hannu ya dora a kanta yayi addua kafin ya mata tambayoyin da akeyi. Koda ya lura a tsorace take da alamar kamar ma kuka takeson tayi. Hannunta ya riko ta dawo gefenshi, sai ta kwantar da kanta saman laps dinshi sai kuka ya balle mata.

A hankali ya fara mata magana "Sakinah, you're not ready?" Saboda shi duk ya gano lagon ta, daga kuka sai yan noke noke.

Nodding kanta ta mishi tana rufe fuskarta da hijab dinta. "Sakinah every girl you see passed through this stage before she became a woman, you're going to be fine kinji?" Hijab din ya yaye daga face dinta.

Wasa wasa daga magana Arhaan ya fara kissing din Sakinah, tanaji tana gani abu ya fara escalating, hankalinta gaba daya ya gama tashi, zuciyarta kamar ta fito mata, ta daina ganin face dinshi a gabanta, face din samarin nan gake hangowa, dukdai a hankali yake binta amma still fargaba biyu ya hade mata, ga tsoron abinda zai faru after he found out ga comeback din memories dinta.

Ganin da gaske dai yasa ta fara tsaidashi tana kuka, lokacin ta sadakas zata fada mashi duk abunda ya faru amma sam Arhaan bai saurari abunda ma take fada mashi ba har saida burinshi ya cika ita kuma time din ba gado takeji a kasanta ba face bare floor din dajin nan, da duwatsu da duhun dare, hannayenshi dake jikinta ba nashi takeji ba na samarin nan takeji, lips dinshi that were clasped with hers ba su takeji ba, face zafin marin samarin nan. Kuka takeyi har muryarta ta kasa fitowa, eyes dinta a kulle kamar ranta zai fita. Dukkan wani kunci da bakin ciki ya gama filling heart dinta.

Batasan yadda akayi tayi bacci ba saidai ta farka taga dakin babu kowa, she was alone. Farko bata gane abunda yake faruwa ba saida taga blanket saman jikinta and then she recalled, wani irin gigitaccen kuka ta fashe dashi kamar ranta zai fita. Shikenan ta faru ta kare dama abunda take gudu kenan.

Tana kuka kamar ranta zai fita har wani shidewa take. Dakyar ta samu ta lallaba ta shiga toilet ta kintsa jikinta kafin tayi wanka ta dawo ta tada sallah, karatun sallar ma kasa yi tayi, irin bakin cikin da take ciki irinshi wanda bawa yakanji kamar ya fidda ranshi ya huta, tana sallah tana kuka tana fada ma Allah, ta rasa takamaimai adduar da zatayi. Na Mama ta tashi ne? Ko kuwa Allah ya karkato da zuciyar Arhaan ya fahimceta idan ta fada mashi? Ko kuwa Allah ya bawa Aunty Halima ikon samun network dan suyi waya?

Tsoron fita take waje, gashi har wajen 10:30am. Yunwa takeji kamar ranta zai fita amma tana gudun ta fita su hadu a parlour. Sai da taga 12 ta kusa ko motsin mutum bataji ba ta fito falon, eyes dinta sunyi ja daka ganta kasan tana cikin bakin ciki kuma taci kuka har ta gode Allah.

Custard kawai ta hada ta zauna falon tanaci tana kuka bawai dan tanajin dadinshi saidan yunwar dake cinta. Haka ta wuni cikin gidan, taje part dinshi yafi sau hamsin amma baya nan tasan bama ya gidan gaba daya. Iyakarta indomie taci da rana daga sallah sai kuka babu abunda tayi. Har dare wajen 10pm bai dawo ba, wani kukan ta fashe dashi yanzu tsoronta ya tashi daga matsalarsu ya koma kan kodai shaye shayenshi ya cigaba dayi?

Nan falonshi barci ya dauketa tana kuka, sai wajen 1am kafin taji karar shigowarshi gidan, zumbur ta mike ta nufi inda yake amma wata hankada daya mata saida ta fadi kasa tana kallonshi. Tsayawa tayi tana kallonshi babu alamar maye a tattare dashi amma zataso ace dukanta yayi akan maganganun da yake fada mata.

"Me zaki fada man? Ni kaina I was a fool for believing wai zan sameki a kamila kimtsatsiyar mace. Kinsan kuwa babu abunda na tsana a duniya kuma nake kyama kamar zina? To hakan take a mazinaci, na tsani duk wani mutum da yake alakantar zina, yau kin shiga, tsanar da nake miki yafi na duk wani mazinaci a duniya."

Cikin wani gunjin kuka take girgiza kanta tana riko kafafunshi amma haka ya kara shureta still ta sake dawowa dakyar kalma uku "Mama ce shaidata." Abunda kawai take iya furtawa kenan.

Cikin wata razananniyar kara ya furta, "Karki sake ki alakanta Mama da kazantartar rayuwarki! Mazinaciya!" Dif komai na jinta ya dauke ta tsaya tana kallonshi har ya shiga daki babu kalmar dake mata ringing cikin kai face wannan mummunar kalmar da yau Arhaan ya alakanta ta da ita 'Mazinaciya!'

Kuyi hakuri da rashin jina kusan wata daya, jarabawa mukeyi yanzu haka ba gamawa mukayi ba nadai samu time ne. Nagode.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now