BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI

1.9K 266 61
                                    

Abunda Safiyya ta lura dashi shine, kwata kwata Sakinah bata sakewa a gidan. Dan suna shiga part dinta sukaga Arhaan har ya shigo ta kofar shi ya zauna, yana kallom TV hankalin shi kwance. Ko kallon banza Sakinah bata mashi ba tayi excusing kanta wajen Safiyya ta wuce dakinta. Dama ga Safiyya sarkin surutu, zama tayi kan kujerar da Arhaan yake zaune kafin ta fara jifanshi da tambayoyi.

"Wai Yaya meke faruwa ne? Naga har yanzu bakuyi magana ba fah. Gashi ta kama hanya ta tafi dakinta, kuma naga tana shanya kayanta dazu, ko dai wani abun kake mata? Dama naji Mama tana ma Mommy complain wai baka kyautawa Sakinah. Haba Yaya," Duk da surutun Safiyya akwai ta da sanin ya kamata da kuma girmama nagaba, kallonshi take cike da tuhuma amma hakan baisa ta jefeshi da kallon raini ba.

Gyara zama Arhaan yayi, cikin ranshi kuwa tunanin karyar da zai yanko ma Safiyya yake ta yarda dashi, dan in har taje ta fadawa Mama wannan abun to lallai kashin shi ya bushe. "Kinga Safiyya, wallahi babu abunda nake mata fah, kawai Mama ce da komai sai tayi exaggerating. Ita kuma Sakinah dan sabani muka samu jiya shine fa take fushi dani, to ya suke so na masu?" Dama duk gidan bayan Aunty Halima a siblings dinshi to sai Safiyya, marairaice mata fuska yayi nan take ta fara tausayawa mashi. Tasan yadda fushin Mama yake tasiri a zuciyarshi, dan yanzu haka jinshi yake kamar a saman kaya yake, tun safe yake kiran layin Mama amma taki picking, karshe ma reject list ta sakashi.

"Allah sarki, kayi hakuri kaji Yaya? Kasan mata sai da hakuri. Bari naje wajen Aunty Sakinar, ita kuma Mama nasan yadda zanyi da ita. Amma fa kaima kar ka rika mata wannan mugun halin naka." Zumbur tayi ta mike tsaye, dan yana iya kai mata duka daga fadin gaskia.

Wani murmushin jin dadi Arhaan yayi kafin ya kalleta, "Mugun halin me kuma, Tatiyya? Ni halayena duka masu kyau ne."

"Mugun halin rashin magana da daure face mana, kuma Allah Yaya indai baka daina ce man haka ba zan tafiyata gidanmu kaje ka koya mata wayar da kanka."

"Haba yar kanwata, wallahi ban iyawa da masifar wancan matar."

"Gata nan tana jinka ai!" She franked him, zumbur ya juya yana kallon kofar Sakinah sai yaga bata nan, dariya yayi ma Safiyya kawai ya tashi ya nufi part dinshi, dan shi bawai fitowar Sakinah ba, maganganun da yasan dole ta dankara mashi sune abunda yake gudu.

Murmushi Safiyya tayi kafin ta shiga dakin Sakinah ta iske ta zaune kan gado tayi zugudum tana kallon kasa, ita gashi ko littafi daya bata dashi balle ta karanta taji saukin boredom din dake damunta. Kan gadon Safiyya taje ta zauna kafin suka kara gaisawa, apologizing na barinta ita kadai Sakinah tayi akan tanada wani aikin da ta karasa a dakinta, bata nuna mata cewar Arhaan bane ya hanata zama inda yake.

"Gashi; kyauta daga miji zuwa matarshi. Yace a bude maki duk abubuwan da nasan zasu maki amfani, yanzu sai mu fara saka charge ko? Kafin na tafi sai ayi duk abunda za'ayi." Cikin farin ciki Sakinah ta karvi wayar tana jujjuyawa, har ga Allah wayar ta shiga ranta, saboda iri daya ce sak da ta hannun Safiyya saida ita ta Safiyyar silver ce.

"Nagode sosai, Safiyya." Sakinah tayi side hugging dinta cike da nuna farin cikinta.

"Aa godiya kuma ai saidai a yima ango ita. Yanzu kinga kizo muje in tayaki girkin rana kafin time ya kure ko?" Zuwan Safiyya ba karamin dadi yama Sakinah ba, domin kuwa duk yadda takejin bata san magana Safiyya taki yarda da hakan, dan dole ta saki jikinta suka rika fira while suna girkin kamar ma babu abunda yake damunta.

Bayan sun gama da komai dakin Sakinar suka koma sukayi Sallah, dan dole Safiyya ta saka Sakinah ta zake wanka ta fiddo mata wata gown me laushi ta material cikin kayanta. Mint green ne yadin, ba karamin kyau ya ma Sakinah ba. Suna zaune suna yar fira sukaji anyi knocking, kafin Sakinah ta rufe kanta da dankwalin Arhaan ya shigo dakin.

"Ku fito muci abincin ko?" Yayi maganar to no one in particular, amma kuma idanunshi kyam a kan gashin Sakinah. Dan zai iya cewa it was the first time yaga kashinta in a bright daylight, baki ne sumar kuma cike take, ta kwanto saman goshinta sosai.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now