Wani irin duka taji gabanta ya bada, shikenan yau tata ta kare. Kallonshi takeyi cike da fargaba da wani irin tsoron da bata taba tunanin zataji a rayuwarta ba, yadda ya rufe mata baki da hannunshi ba karamin razana ta yayi ba ga kuma hannayenta duka ya hade ya rike, wannan shikenan shima yi mata zaiyi, girgiza kai ta shiga yi tana wani irin zillewa aman hakan bai hana Arhaan kara riketa tamau ba, in hankalin Sakinah yakai dubu to ya tashi.
Shi kuma Arhaan ganin yadda hawaye ke zubowa daga idanunta kamar da bakin kwarya ba karamin tunzurashi yayi ba, janyo ta yayi da niyar ya zaunar da ita kan kujera kafin duk ma abunda zai mata ya mata, amma to his dismay, duk step din da suka dauka towards kujerar sai yaga numfashin Sakinar kamar ma niyar daukewa yakeyi. Yasan halin Sakinah, dan ire iren iskancinta babu irin wanda bai gani ba, kuma yau sai ya maido mata da hankalinta cikin kanta, inma zata daina wannan munufurcin na kuka ta daina inba haka be wahala zatasha wajenshi.
Saman kujerar yayi wurgi da ita kafin ya taka ya isa wajen, girgiza mashi kai kawai takeyi, hawaye kuwa kamar anyi mata ambaliyan su. Ganin ya nufota da gasken gaske yasa Sakinah fashewa da wata irin razanannen kara "Na shigo ukku! Dan Allah dan Annabi kayi hakuri, dan Allah!"
"Wai baki da hankali ne?! Wani abun kikaji ance za'ayi maki? Me ma za'a dauka a kazamin jikinki?!!" Wata irin tsawa me razanarwa Arhaan ya mata wanda garin ta hade kukan nata saidai yaga idanunta sun juye sun kafe suna kallon sama. Shi a daukarshi duk cikin iskancin ta ne, ganin tayi shiru yasa yaja tsaki ya kashe tv kafin ya nufi dining table ko kallon inda take bai kuma yi ba.
Saida ya gama cin abincin shi, and to his surprise yaji abincin babu laifi ta dan iya. Wayarshi ya fito ya ida replying text messages dinshi, dan shi har mamaki yake a ina sukaji labarin auren nashi? Wannan aure ko auren kaddara? Tsaki yayi da yaji takaicin abun yazo zai koma side dinshi yaga tana nan dai a yadda ya barta dan ko yanayin zaman fingers dinta bai motsa ba. Har yazo zai wuce sai yaji bari dai yaje yaji wani sabon salon iskancin ne ta fito dashi kuma?
Daidai saitin kanta ya tsaya yana karema jikakkiyar face dinta kallo, wanda a yanzu hawayen ma sun fara bushewa dan kansu. "Ke ki tashi kije ki kwashe kayancan, wani sabon salo ne kuma kika fito dashi?!" A dan tsawace yake magana, dan yasan halin Sakinah sarai idan yace zai bita da lalama tabbas sai takaici ya kusa kasheshi.
Ganin shiru bata motsa ba yasa ya saki wani tsakin yana me wasa da keys dinshi dake aljihu. "Wai ke ba magana nake maki ba? Wallahi karki bari raina ya baci. Zaki tashi ko kuwa?" Har ila yau dai ko bugawar zuciyarta bai ga ya motsa ba ballantana ma yasa ran ko duk dauriya takeyi. Lura yayi sosai da ydda kirjinta ya tsaya cak babu alamun motsi, hakan ba karamin tada mashi hankali yayi ba dole ya sunkuya ya riko hannunta amma sai ji yayi kamar hannun ya fara yin sanyi.
Innalillahi! Arhaan baisan sadda yakai kunnenshi saitin zuciyarta ba dan jin ko tana bugawa ko kuwa abunda zuciyarshi ke fada mashi gaskiya ne. Wani faint and weak beat yaji zuciyar nayi, a gaggauce ya wuce dining table ya dauko bottle din ruwa ya dawo tsakiyar falon da ita, shi wallahi baiyi tunanin suma tayi ba. And from the looks sumar ba irin wadda masu lafiya keyi bace.
A fuska ya fara yayyafa mata amma shiru, babu irin yadda baiyi ba amma kwata kwata ruwan nan ya gagara tayar da Sakinah. Yama yi kokarin maido da idanunta ko rufe su yayi amma abu ya gagara, cikin rudani ya kira family doctor dinsu ya gaya mashi. Fada mashi yadda zai bata taimakon gaggawa yayi kafin ya karaso gidan nasu.
Kamar yadda doctor din yace mashi haka ya fara, instead of cardiopulmonary resuscitation kafin isowar doctor din. With both hands ya fara danna mata chest dinta saita lungs and heart dinta, ganin dau still Sakinah bawai tana da niyar motsi bane yasa Arhaan danna wajen da karfi nan take wani tari ya sarke ta, baisan sadda yace "Alhamdulillah," ba.
Ganin shi gefenta with such proximity yasa ta nemi ta kara birkicewa, ganin gabanta ya cigaba da tsananta fadi yasa Arhaan lura da tabbas tsoro takeji. With the little knowledge he has, yasan idan mutum ya suma baa motsi dashi unnecessarily inba haka ba attack din zai dawo.
Dan yunkurowa tayi tana taba jikinta taji me ya mata? Shima yayi ne akan wanda sukayi? Amma she felt her clothes as she passed out on them, kuma ita kanta a jikanta tana feeling kanta intact, wata ajiyar zuciya ta saki sai hawaye. Ga wani weakness dake addabar ta, ko hannunta bata iya jin zata iya dagawa. Kokarin tashi take daga kujerar amma ta kasa, dakyar ta samu ta mike zaune tanajin kamar zata kara suma.
To her surprise, gani tayi Arhaan ya koma ya zauna kusa da ita, ta bude baki zatayi magana kenan ya janyo ta zuwa jikinshi yana side hugging dinta "Listen, don't panic, babu abunda zai sameki, ko so kike ki kara suma? Kuma idan kina mosti heart dinki will fail shikenan zaki mutu. Ki natsu the doctor is on his way." Yadda yayi maganar cikin kwantar da hankali yaba Sakinah mamaki, amma to make use of the moment, dan ita kanta bawai zata iya motsawa daga wajen bane ba, hakan yasa tayi lamo hade da kwantar da kanta saman shoulder dinshi tana me kulle idanunta.
Suna a haka sai ga doctor yayi sallama, kafin Arhaan yaje ya bude kofar haka kawai ya tsinci kanshi da zuwa dakinta ya dauko hijab ya bata ta saka kafin yaje ya bude ma doctor din. Koda ya shigo saida yayi yan dube dube kafin ya fada ma Arhaan cewa idan mutum ya suma to ba'a mari ko duka ko zuba ma mutum ruwa wai dan ya farka, hakan yana kara bada gudunmuwa akan sumar.
"She had a panic attack, but luckily abun bai taba heart dinta ba. You should sit and ask her abunda yake damunta da kuma abunda ke maido mata wancan panick din, she should avoid it at all cost." Magungunan da zai rage mata panic din ya bada kafin Arhaan ya mishi godiya ya tafi, koda ya dawo isketa yayi ta bingire a saman kujerar ta fara bacci. Saida ya dan dade a tsaye yana kallonta, shi kanshi baisan dalilin kallon nata ba, sai can ya taka ya isa inda take yasa hannu ya dauketa ya nufi dakinta.
Rabonshi da ko kallon dakin nata tun daren jiya, a hankali ya bude ya shiga, sassanyan kamshi ne ya daki hancinshi, komai na dakin neat yake, kan gadon yaje ya kwantar da ita, har zai fita sai ya tuna doctor yace mashi ya tabbatar iska bata mata karanci ba, dan haka ya koma ya fara cire mata hijab dinta sai ya lura zufa ma take.
"Sakinah tashi ki canza kayanki," a hankali yake maganar kamar yana tsoron tada yaro me rigima. Ko motsawa batayi ba, a hankali ya fara tapping shoulder dinta, "Sakinah..." shi kanshi saida yaji sunan wani iri a kunnenshi.
"Ummm..." da kyar ta amsa tana me juya mashi baya, "Ki tashi ki cire kayanki, ko so kike ki rasa numfashi ki mutu?" A hankali lazily ta mike zaune, dan kwalin kanta ta zame cike da magagin bacci, hannu ta daga sama kamar yarinya kwata kwata ta manta wanda yake tare da ita, ita bama muryar maza takeji ba duk tunaninta Habibah ce.
"To cire mani rigar dan Allah, wallahi ban iyawa." Cike da shagwaba Sakinah ke magana hannayenta a dage a sama, idanunta a rufe suke tsabar baccin da takeji, yadda akayi ma ta tashin wani ikon Allah ne.
Kallonta kawai ya tsaya yanayi, zaar innocence ne kwance kan fuskar ta, yadda takeyi tsab sai kayi tunanin yarinya ce yar shekara 13 ko kasa da haka. Ganin da gaske tana cigaba da baccin nata a hakan yasa dole ya mike tsaye, shi gashi ba abun ya barta a hakan ba yayi tafiyarshi suffocation ya kamata cikin dare ta siqe ta mutu bai sani ba.
Daure fuska yayi can kasan ranshi ya furta "For the sake of Mama." Kafin ya fara cire mata rigar. Sakinah najin an cire rigar ta koma luuu ta kwanta kan gadon "Kinga Beeba, ki dauko man wata white nightgown a wardrobe dina please, skirt dinnan ma yadan matseni ki cire man, sai bra dinnan sai inji tana hanani numfashi please. Thank you." Daga haka ko motsi bata kara sai ma numfashinta ya fara fita cikin sanyi da nauyi alamar baccinta ta shiga yi me cike da kwanciyar hankali.
Sakake Arhaan yake kallon ta, shi a hakan ma kawai dai balle har ya mata sauran abubuwan datace, hada wani cire bra, yau shikam yaga ta kanshi, Gashi Doctor ya tabbatar mashi da idan har wani abu yana takura mata tabbas ta cire shi, saboda har yanzu numfashinta bai dawo daidai ba. Yanzu ya zaiyi?
My Wattpad readers, inajin dadin comments dinku matuka! Nagode❤️
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...