BABI NA SHA TARA

1.6K 242 33
                                    

Saheer baisan wacece ba, amma haka nan yaji yana bukatar shielding dinta. Yadda hawayenta ke zuba saman kafadarshi was enough evidence to show she was in a dilemma. Bai jira komai ba, dakyar ya samu ya jasu zuwa mota, dan ko tafiya ma dakyar take yinta. With his help-Habiba ta shiga motan ta zauna, kafin shima ua zagaya ya zauna gefenta_dayake a back seat suke.

Ta kankame idanunta kaf, hannuwanta da jikinta babu inda baya rawa-sannan ga hawaye sai zarya suke bisa kuncinta. Daga gani tana cikin matsanancin tashin hankali. Kallonta kawai yake yadda hawayen ke zubowa, haka kawai yaji yanaso yasan tarihin yarinyar nan. Wacece ita? Da gaske din bata san iyayenta ba? Haka ta taso ta ganta cikin gidan Hajia a matsayin yar aiki?

Dakyar ya samu bakinshi ya iya furta-"Habiba, look up mana_kukan ya isa haka kinji? Me aka yi maki? Meya faru?" A hankali yake magana kamar yanama jariri, da gaske tausayinta yakeji har cikin bargonshi.

Jim tayi kafin daga bisani ta fara squinting eyes dinta slowly, afraid she might see someone she wasn't used to. Tar bloodshot eyes dinta suka sauka saman worried fuskar Saheer_kallo ne yake binta dashi me cike da ma'anoni.

Tana ganinshi kawai ta kara fashewa da wani kukan, dan ita yanzu ko ance ta nuna dan uwanta to tabbas shi zata nuna, batasan kowa mata ba. Kuka take sosai tana girgiza kai, so take ta fada mashi abunda ake mata cikin gidannan, halakar da ake san jefeta a ciki, amma kamar yan yanke duk wanj connection daga kwakwalwarta zuwa bakinta.

Tashin hankali ba'a saka masa rana, kallonshi tana tana zare ido amma sam baki yaki motsawa_so take ya shiga zuciyarta ya dubo abunda ke jagula mata lissafi but all seemed to be only her hallucination. She doesn't know what's procrastinating her, but one thing she knew is that; wannan ba yinta bane.

Ganin dai da gasken ba maganar zata iyayi ba, kawai sai ta fashe da wani kuka mai taba zuciyar mai sauraro, har yanzu tana girgiza kanta alamun kar kaimun haka bakina. Defeatedly, tayi palming face dinta kawai ta cigaba da dirzar kukanta.

Saheer rabonda yani tausayin wani na ratsashi kamar na Habiba an dade, kusan zai iya cewa ma tun yana yaro. Dauriya ce kawai ta hana bai biye mata sunyi kukan ba, amma tabbas zuciyarshi ta tabu iya tabuwa. "Kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa. Don't stress yourself idan baki iya magana, whenever you can; I'll be a phone call away kinji?" Ya furta da murya irin wanda tausayi yan kama kagon zuciyarsu.

Bata yarda ta kara yunkurin yin magana ba, dan tasan koda tayi bawai maganar zata fito bane ba. Ga abunda takeso ta furta amma ta kasa? What's the use toh? Nodding kanta kawai tayi tana kokarin fita daga motar, amma har lokacin hawaye suna zuba kamar waterfall.

Shima fitowar yayi a tare suka jera suka shiga cikin gidan, magana ya mata akan ta kira mashi Hajia kafin ta wuce ciki. Saida ta saita nutsuwarta kafin ta sami Hajia a falonta, durkusawa tayi ta gaisheta-abun mamaki sai ga maganarta zar kamar daukewar wuta da maidowa.

"Ya akayi ne, Beeba? Ramcy na bacci, banasan surutu ya tashe ta," Hajia ta tambaya, tana kallon kofar dakin kamar wani sabon jinjiri ke ciki.

Jin sunan Ramcy ba karamin haifar mata da tashin hankali yayi ba. Amma haka ta daure ta hadiyi yawu kafin ta fara bawa Hajia amsa. "Dama Saheer ne dan kawar nan taki yazo yace in kiraki." Ai kafin ma ta ida maganar Hajia har ta shiga daki ta dauko wani kunshi a leda ta fita_girgiza kai kawai tayi ta nufu dakinta, saida ta tabbatar babu kowa cikin kafin ta garka mashi lock ta kwanta saman gado ta cigaba da rizgar kukanta.

***

Tun lokacin da Baban Shaheed ya gane Sakinah na fitsarin kwance rayuwa bata kara mata dadi ba cikin gidan. Takai yanzu ma har su Kamal da Hafsah na mata wulakanci saboda fitsarin, danma Aunty Halima nadan tsawatar masu.

Yau ta kasance Friday, goge goge takeyi tanata hanzari gudun kar su dawo bata idasa aikinta ba_ga wani wahalallen ciwon ciki na dawainiya da mararta. Jan jiki kawai take, amma daidai da motsi daya idan tayu ji take kamar ranta ya fito, tsayuwa ma kuwa sai taji kafin kasusuwan duk zasu zubo.

Ta saba a gida duk masifar Inna idan tana wannan ciwon cikin takan sassauta mata, amma nan fa wa gareta? Dole ta zage tayi aiki. Kukan ma daina zuwa yayi, tana cikin aikin ne taji kamar bude kofa amma sai bata damu ba_dan tasan tunda sukayi last fadansu da Dan shagwaba rabonda ta ganshi, dama shine bai dawowa da wuri ranar Friday.

"Keh!" Taji an dama mata tsawa, a wahalce ta juyo, tana sauke kallonta kan fuskarshi dake murtuke kamar an aiko mashi mutuwa, waishi a dole sai ya bata tsoro ta bar raina shi.

Tuno fadan da Aunty Halima ta mata da kuma ciwon jikinta yasa bata ce komai ba, "Na'am," rather, she answered politely.

Ko kallon inda take baiyi ba, saida yaje ya zauna kafin ya harde kafafunshi yana kallonta a kaskance "Tashi kije ki fere man dankali, ki daura man ruwan zafi kuma_but firan kawai zakayi," dan he can't imagine eating her rubbish. Yau dinma matsala aka samu, bacin ya fita da wuri bai jira Aunty Halima ta dafa mashi breakfast dinshi ba, da babu yadda zaayi ya nemi wata kazamar yarinya.

Mararta ce ta kara wani matsawa, daurewa kafin tayi ta cije baki ta kalleshi, idanunta har sun kawo ruwa-dan ita idan tana ciwon nan wani abun tausayi take komawa. "Kaga yanzu 9 da wani abu, kuma inaso na gama aikin kafin ta dawo. Dan Allah ko zakaci wanda suka rage?" Ita har ga Allah bata tambayeshi da wani abu ba, dan azabar dake cin mararta ma bazai barta tayi wata rashin kunya ba.

"Keh, ni kike fadawa naci remnants din wasu? Zaki tashi kiyi abunda nace ko kuwa? Rashin kunyar zaki kara man?" At the top of his voice yake magana, yana jifanta da wani kasakantaccen kallo.

Batace komai ba ta ajiye kayan goge gogen kawai ta nufi kitchen, a wani durkufe take tafiya, harga Allah babu abunda take bukata yanzu kamar hutu, amma tasan wannan dan rigimar husuma yake nema. Tana shiga ta debo dankalin ta fara ferewa tana yanakawa, tun tana tsaye har ta koma a durkushe. Idan marar ta matsa mata sai ta saki wukar ta kama numfashi dakyar har sau ta sauka, daga nan kuma ta cigaba.

Ganin dai ta kusan minti talatin bata dawo ba daga firar dankali yaso Arhaan binta kitchen din, amma sai ganinta yayi rike da cike sai mukurkusu take kamar macijiya. Karasawa yayi without a sign of emptahy towards her, wukar ya cira daga hannunta kawai ya cigaba da ferewa.

Sakinah dagowa tayi tana kallonshi, ga hawaye shar shar na zubowa kamar da bakin kwarya. "Dan Allah in tafi? Wallahi ban iyawa," muryarta har karyewa takeyi, ga hannunta saman mararta tanata murza kamar ranta ya fita.

Ko kallon inda take baiyi ba, "Jeki hadaman custard idan ruwan zafin yayi," haka kawai ya furta ya mike tsaye da bowl din peeled potatoes din.

Dakyar da jibin goshi ta mike ta karasa wajen ruwan zafin, tana tafiya dai dai tana kuka haka dakyar ta gama hada custard din ta ajiye mashi ba tare da ta saka madara ba, dan tsaf tasan yana iya cewa ta mashi jagwalgwalo. Wajen da tayi peeling potatoes din taje ta share kafin ta dawo, zuwa lokacin Arhaan har ya saka mai yayi zafi.

Zuba dankalin yayi cikin mai aikuwa da gudu yayi baya, saboda irin tartsatsin dake tashi idan mai ya hadu da ruwa. Harara ta galla mashi ta gefen ido kafin ta nufi wajen ta fara motsawa tana cijen lebe.

"Ke ni fa karki man kazanta, abeg matsa," ya furta hakan ne daga nesa,a kuma yaki karasowa, dan gudun karya kone.

"Ai sai yasa naga daga zubawar farko ka ruga baya." Abunda ta furta kenan, sarcastically kafin ta cigaba da abunda take. Daidai ya karaso wajen kawai ta saki kara tayi slumping a kasa. Wata irin azaba ce takeji har cikin hakarkarinta, shi kuma wannan mugun ya kasa fahimtar abunda yake damunta balle ya barta ta tafi.

"Ke dallah tashi, sharri kuma zaki ja man? Zo kiga idan yayi na kwashe." A dardare yake motsa abun, yana kallonta with urgency in his eyes, alamun ta taso dinfa.

Tanajin lokacin daya fara zubowa a hankali, wani irin tashin hankali ta shiga, dan batasan ta inda zata fara tashi ba_gata idan tanayi yadda kasan tap haka take komawa. Ganin ya kwashe wancan din bai jirata ba kuma ya zuba wani gashi ya kwasa da gudu yasa a daddafe kawai ta mike, amma tana mikewa jinin na diga saman tiles din-addua take har ranta kar hankalinshi yakai ga jinin.

"Keh, menene nake gani haka?!" Shi sai ma yanzu brain dinshi ta mashi registering yadda taketa mukurkusun, yana lura da su Safiyya da Muhibbah idan suna wannan ciwon.

Kafin ta bashi amsa taji wata juwa na dibarta, luuu ta tafi amma kafin ta fadi sai ta jita an rike gam gam.


Bakwa comments sai yasa nake tunanin taking book din down.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now