A gajiye suka iso asibitin, jikinsu babu inda baya rawa, burinsu bai wuce suje suga halin da Mama take ciki ba. Baba ne ya juyo ya kallesu, dama shi yaje daukosu asibitin. He wanted it to be a surprise, tun last month ta farka, amma kasancewar jikin nata time din bama gane mutane take ba yasa babu wanda ya fada mawa. Bata fara magana ba sai last week, maganan ta na farko was ina Arhaan? Tun Baba yana gani kamar zafin ciwo ne har dai ya kira mata Arhaan din, lokacin har ya musu booking din flight and all.
"Arhaan kodai na kaiku masauki ku huta anjima kun dawo? May be itama baccin take yanzu." Ba dan komai yace haka ba saidan Sakina, yaga abun ciki shi baima san akwai cikin ba, kuma kullum sai sunyi waya da Mommy amma bata taba fada mashi ba.
Sakina ce tayi karaf, "Aa Baba dan Allah zamu jirata har sai ta tashi," gani take ita tafi Arhaan kosawa suga Mamar nan, she has alot to tell her.
Baba yar dariya yayi kafin yayi leading dinsu hanyar dakin da Mamar take ciki, "Sakina ke nake tausayawa, naga kinyi nauyi da yawa. Kai Arhaan shine ko ka fada man na fara siyayyar kaka ko?" Left kunnenshi ya kamo ya murza cikin wasa.
Kunya ta lullube Sakina, shi kuwa Arhaan ihu ya fara, "Baba kayi hakuri to, ba gashi ka gani ba yanzu? Kyautar me zaa bawa baby?"
"Kaci gidanku! Kyautar kaina zan bawa dan, dan gidanku mara kunyar banza!" Duka ya kai mishi daidai time din da suka bude kofar suka shiga dakin.
Da dariya fuskarsu, amma dukansu tsayawa sukayi suna kallon Mama wacce nurse take bawa magungunanta. Sakina bayan Arhaan ta boye, dan wata irin kunya taji ace Mama ta ganta da uban ciki haihuwa gobe ko jibi.
"Dan Mama..." Mama ta furta da murya mai rawa, daka ganta kasan dauriya kawai takeyi amma kuka takeso tayi.
Kamar karamin yaro haka ya fara takawa har inda yake, hannunta da take miko mashi ya rike a hannunshi sai hawaye, hugging dinta yayi gaba daya. Ita kuka shi kuka kamar wacce ta shekara dari ba lafiya. Sai can cikin kuka ya fara magana.
"Mama I thought you're going to leave me, Mama I thought bazan kara ganinki ba, your hands, your voice, your laps, everything about you Mama. I kept dreaming About Aunty Yo, she's laughing at me saying that dama tace zata rabami dake har karshen rayuwata, yanzu bazan kara ganin ki ba." Aunty Yo matar Baba ce wacce suka rabu tun Arhaan bai kai 10 years ba. A lokacin suna zama Lagos, Mummy kuma na Kaduna. Kudirat sunanta, bayerabiya ce, kamar wasa ta fara kai tallar abinci wajen aikin Baba a nan dai tasan yanda tayi har ta aureshi. Muzgunawa babu irin wacce bata yiwa Mama dasu Arhaan ba, yakai Baba ko magana baya masu. Karshe dai saida tasa akawa Mama saki daya, kafin ranar da dubunta ta cika asirinta ya kare Baba ya saketa.
A zaman da sukayi da ita, Arhaan babu kalar rayuwar da bai gani ba, har takai da dukda Mama ta dawo gidan kullum da daddare sai yayi mafarkin Aunty Yo tana azabtar dashi. Mafari kenan duk idan ya fara bacci tofa jikinshi ya mutu kenan, dan har yau gani yake Aunty Yo zata dawo cikin rayuwar shi. Shi da Aunty Halima suka saka mata Aunty Yo. A cewarsu she's Yoruba, gashi Mama tace su rika ce mata Aunty. Hence the name, Aunty Yo.
Breaking hug dinsu Mama tayi, "Haba Dan Mama, ba nace maka babu kai babu Aunty Yo ba har abada? Ka kwantar da hankalinka kaji? Maza daina kuka kar Sakina ta maka dariya. Naji kamar ka dan rame, kuka ka rikayi ko?" Jikinshi ta fara dubawa kafin tayi cupping face dinshi, kuka yake har yanzu, ita kuma she's trying all she can do ta danne nata kukan amma ta kasa. Dukda watannin da tayi a kwance she can feel his absence a tare da ita.
"Nayi missing dinki Mama, I almost gone crazy wallahi. How are you feeling? Thank you for coming back to me, to us, and your little Arhaan as well." Yana fadin haka yayi breaking hug dinsu kafin ya janyo hannun Sakina ta dawo gabanshi.
Kallon mamaki Mama ta bisu dashi, ido sake take kallon Sakina, wacce hawaye sun gama wanke mata fuska tas. A hankali eyes dinta suka sauka akan cikin Sakina, dole ta saki hawayenta suka zubo. Sakina ce ta karasa jikinta tayi hugging dinta.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...