Hada ido sukayi kafin Sakinah ta saki wani irin triumphant smile da saida ya bawa Arhaan mamaki. He became curious, wasn't she just crying minutes ago? A yadda ta nuna kenan, though shi dama yasan ko sama da kasa zasu hade Sakinah bazata taba mashi kuka ba, not after what he did to her hours ago.
"Dan Mama kenan, so this is how you're so much loved and pampered? Dole ka zama sangartacce wallahi. Opps, you're a patient right? Bai kamata na bata maka rai ba, inba so nake yanzu a fashe mani da wani kukan ba," cike da jan fada da kuma wata irin dariyar ban haushi take magana, kallonshi take tana mischievous smile har ta karaso kan kujerar da Mama was sitting on some minutes ago.
Kara kallonta yayi yama rasa abunda zai furta, anya yarinyar nan bata da sa hannu kuwa? Ji yadda take magana with full confidence kamar wacce keda assurance din cewa bazai iya mata komai ba. Kauda kanshi yayi waje daya amma abunda ta furta dole yasa ya juyo yana kallonta.
"Yau Dan Mama babu bakin magana ne wai? Ya naga duk ka zama so weak ne? Ko waka kakeso inyi maka sai kadan wartsake?" Sarcastically take magana, harara take balla mashi daya bayan daya, shi kuwa Arhaan yama rasa mezai ce mata ya huce haushi, infact kunya ma yakeji yadda ta ganshi in the most vulnerable and emotional side of him.
"Tashi ki fita dakin nan!" He thundered, yana kallon kofar da idanunshi alamar ta bashi wuri.
Clapping hands dinsa tayi tana galla mashi harara. "Waikai dama sakarcinka har ya kai nan ban sani ba? In fita waje insu Mama sun dawo ince masu me? Dallah gafara malam kaji da ciwon dake damunka, kuma mind you; karka kara man tsawa!" wuri fa ya samu, magana take cike da rashin kunyar da bata taba yi ba, dan tasan ko yunkurin tashi bai isa yayi ba.
Ganin intense infuriated look din dayake flashing mata yasa ta daure itama tana kallonshi with the same look of his eyes. Their orbs were merged together, ido cikon ido suke kallon juna; kowanne idonshi na emoting his intense hatred for the other, but what surprises her was; she felt weak under his scorching gaze.
Yawing gaze dinta tayi from his bandaged face, fiddling with her long well sculptured fingers. "Kai malam wai lafiya ka wani kureni da idanu kamar zaka cinye ni? Idan kyau na maka ai sai ka fada bawai ka zuba mani idanu ba. Ba lafiyar ma sai yar banzar jarabar tsiya." wani uban tsaki taja kafin ta mike daga kan kujerar, for he was still staring at her, and if looks could kill; Sakinah would've been dead by now.
Blinking eyes dinshi yayi kafin yayi k'wafa. Yarinyar nan karshen raini wallahi ta raina shi, dan iskanci shi zata kalla tace wani in santa yake? Such a fool she is. "Amma kinsan ko a dakikai ke layin jakkan dakikai kike ko? Inba tumasanci ba ta ina kamata zan fara ganin kyaunki balle har in so ki, ke dalla matsa ni ki bani wuri; kibar mata suyi magana ba muna mata ba." Yadda yake maganar yana wani yamutsa fuska kamar yana magana da kashi ya k'ule Sakinah. Harararta yake yadda kasan mace na harara, wani tukukin bacin ciki ya tsaya mata a zuciya.
Wata shewa ta saki cike da shakiyanci, wato Arhaan ita yake cema ba mace ba ko? Wallahi sai ya gane kurenshi. "Allah gani kasheni! Kai wai in ana sabotaging halittar Allah ma har ka saka baki? Kai inba kaddara ba ai babu wanda zai kiraka namiji wallahi, kai bari fa kaji; ni nan yadda na raina ka ko Ahmad nafi tsoronshi a kanka, yo mi ake da sakaran namijin da mace ma tafishi jarumtaka. Dalla matsa can, talasuru kawai." Alama tayi da hannu alamun ya matsa din da gaske, ita kanta tasan ta kaishi karshe; kamar an shiga ranta saiga Mama da Aunty Halima sun shigo suna yar fira sama sama.
"Auntynmu har kun dawo? Bari inje inyi sallar nima, naga tunda kuka fita ma ko magana baiyi ba; kuma na tambayeshi ko yanasan wani abu saidai ya girgiza kai." Yadda take magana sai ka rantse da Allah ba Sakinar data gama zazzage ma Arhaan ta cikinta bace, so calm and respectful; har wani kallonshi take irin bawan Allahn yaki cewa komai.
"Allah sarki nagode maki sosai wallahi. Kije kiyi sallar kinji?" Mama tayi magana cikin kwanciya hankali tana patting shoulder dinta.
Sakina daga kai tayi suka hada ido da Arhaan ta sakar mashi wani murmushin mugunta wanda saida yaji kamar ya bita wajen ya mata jan dukan da sai ta kasa tashi.
"Auntynmu sai na dawo toh." tana furta haka ta sakai ta fita daga dakin, koda taje masallacin wata irin shewa ta saki tana dariyar mugunta kafin tayi alwalla ta gabatar da sallah, ita jin dadinta daya; tasha alwashi kafin Arhaan ya warke sai ta rama dukkan wulakancin daya mata kuma baida bakin magana.
"Wallahi Halima yarinyar can tanada kirki, ina santa gaskia." Mama ta furta, wanda maganar har kasan zuciyarta yake.
"Laah ai Sakinah akwai kirki sosai Mama, bata da matsala; danma dan Mama yana mata rashin mutunci idan ta motso." Dariya suka kwashe dashi kafin Mama ta fara ma Arhaan nasiha akan ya daina yawan yima mutane wulakanci, daga nan kuma hirar ta koma ta gidansu da sauran harkokin rayuwa.
***
Koda suka isa Habiba sakin baki tayi tana kallon tangamemen gidan, ita ta dauka she've seen all in Hajia's house, not knowing there are people that lives in luxury more than her.
Parking Saheer yayi kafin Maama ta sauko daga motar, still Habiba na cikin motar; unable to lift a finger. Ta rasa irin feeling din da has been ebbing in her mind tunda suka shigo gidan. Saheer dinne ya bude kofar da take bangarenta, but she was deep in thought da harma bata lura da cewar ita suka kura ma ido ba.
"Yar baka lafiya dai ko? Ko gidan ne bai maki ba?" Saheer ya tambaya cikin murya mai taushi da lallashi, a lokuta da dama yakan hango damuwa male male cikin idanun Habiba, amma da worst thing is that; bata iya furta tata damuwar.
Firgigit ta dawo cikin hankalinta kafin ta juyo ta kalleshi taga har Maama hankalinta na kansu. "Pardon my absent mindedness dan Allah, I've been carried away. In sauko?" ta tambaya with an innocent voice, dilating her eyes tana kallonsu; wanda hakan yayi swaying Saheer off his feet.
"Muje ciki Beeba kinji? Saheer tayata da jakanta mana." Maama na fadin haka ta wuce cikin gida. She doesn't like what she's seeing in Saheer's eyes towards Beeba, but in the most coolest ways zatayi maganin abun. No need to vent over it.
Boot ya bude ya dauko jakan, zuwa lokacin Habiba ta sauko tanata kalle kalle harabar gidan. Gidan ya mata kyau sosai ma kuwa. "Muje Yar Baka." Abunda ya furta kenan kafin suka jera suna tafiya zuwa cikin gidan.
"Dan gayu ashe dai I wasn't mistaking da nake kiranka dan gayu, you surely live in luxury. Gidan nan yaman kyau sosai!" Ta furta ta wani exquisite murmushi tana kara kallon gidan har suka karasa cikin gidan.
"Yar baka luxury suits you kema, zakiyi kyau a nan. Infact ke zakima gidan kyau bawai gidan zai maki ba. It's a matter of time kafin ya zama naki gaba daya." Hakan daya furta har kasan zuciyarshi ya fito, amma ko kadan Beeba bata dauki maganarshi da wata manufa ba, illa kawai she laughed it off_a haka suka shiga cikin falon da almost made Habiba drooled.
"Muje na nuna maki dakinki ko? Then sai na hada mana lunch kafin Maama ta tashi daga bacci. She always take a nap in the afternoon." Nodding kanta ta mashi, dan kuwa kyawun gidan ma ya hana ko kallon fuskarshi tayi, she was so carried away.
Few feets ne dakinta away from Maama's, saida suka shiga ya ajiye mata jakarta on the sofa kafin ya nuna mata wardrobe da toilet sannan yayi excusing kanshi akan zaiyi sallah shima sai ya shiga kitchen.
Habiba tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, bazata iya tuna daga inda take ba, amma she knew she wasn't from an affluent background; dan ko suturarta ta nuna hakan. Amma yau itace zata kwana in a luxurious room kamar wannan, and he was even saying it belongs to her. Life indeed is ironic, indai kana raye karka fidda rai da rahamar ubangiji.
Yan kayanta ta hada cikin wardrobe din, ghana must go din kuma ta jefata can sama yadda babu wanda zai hangota. Toilet din ta nufa tayi wanka kafin ta fito ta sama mayukan data gani a saman mirror da body sprays. Kaya ta chanza kafin ta gabatar da sallah, har ta zauna sai kuma ta tashi da nufi sauka kasa dan kuwa if she isn't mistaking taji Saheer na magana akan zai shiga kitchen ya hada masu lunch.
Tana sauka ta tsaya tana kalle kalle, can idanta ya hango mata wani spacious and utterly gorgeous kitchen. Dan sauti taji yana tasowa daga kitchen din, with halting steps ta nufi hanyar; dukda bata da tabbacin wa yake cikin kitchen din.
Kumin afuwar rashin jina da kukayi, yanzu haka ban ida warkewa daga ciwon danake ba.
Ina kike kawar Halima Amiru? Dan Allah kiyi magana ko nasan wacece😀
Nagode.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
Ficción GeneralLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...