BABI NA TALATIN DA SHIDA

1.5K 226 37
                                    

Fuskar yagani a rufe, amma duk wacce take cikin blanket din bata lafiya dan kuwa sai rawar sanyi take irin ta masu zazzabi. Yazo zai daga blanket din daga fuskarta kenan Aunty Halima ta shigo dakin, kallonshi kayi kafin ta karaso cikin dakin da murmushi kan lips dinta. She knew Arhaan, and right now he's curious to the core; amma she wouldn't let him unveil Sakinah's face, dan kuwa ita kanta Sakinar wouldn't love that.

"Ya dai, dan Mama? Ko aikin za'a tafi ne?" Ta tambayeshi tana karasowa kusa dashi. Arhaan barin wajen fuskar yayi hanyar kofa, haka kawai yakejin ranshi baya mashi dadi, something related to whoever it is laid on Aunty Halima's bed.

"Eh wallahi, gashi nama makara, I'll take my leave, sai na dawo." Yana fadin haka bai saurari amsar ta ba ya fita daga dakin, numfashi Aunty Halima ta sauke kafin ta ajiye plate din abincin data kawowa Sakinah ta koma kitchen din. Kasantuwar Baban Shaheed baijin dadi yasa tayi taking weekly leave a office dinsu.

Sai can wajen karfe 10 Sakinah ta tashi, tana farkawa bakin ciki yayi dirar mikiya cikin zuciyarta, nan take taji wani daci a makogwaronta. Ta dade da jin hausana da kiran bacci da rahama, amma bata taba yarda ba sai yau. Bazatace ga yadda baccinta yake ba, amma tabbas hours din da tayi taking while asleep were blissful, dan kuwa ko da digon bakin cikin dake ranta bata ji ba. Amma within a second of her awake, she felt the pain diving to the deepest core of her soul.

Kuka ne kawai ya kubce mata, tunawa da tayi yadda samarin nan suka keta mata haddi ba tare da sun tsaya sunji duk irin rokan da take masu ba. Duk da cewar sun kulle mata baki, hakan bai hana su karantar pleas dinta daga hawayen idanunta. Ashe dama duniya cike take da azzalumai marasa imani? Dama haka duniyar take kowa ka gani bayasan farin cikin ka? Ita yanzu ina zata sa kanta?

Kanta ta cusa cikin laps dinta ta fara kuka, kuka me cin rai mai tara da dana sani, kunci da kuma bakin ciki. Sakinah batasan ya akayi ba saidai taji an dafa ta, dagowa tayi da rinannun idanunta ta saukesu akan Mama tana kallonta cike da tausayi, ga Aunty Halima gefensu tsaye.

Mama wadda tazo gaisuwar mijin kawarta tun daren jiya, dan kuwa kusan su sukayi jinyarshi a abuja, da Allah ya dauki ranshi sai ta biyo yan kawo gawa ta kwana yau da safe tazo gidan Aunty Halima domin ta huta. Shigowarta kenan sai suka iske Sakinah tana wani gunjin kuka mai cike da tsantsar bakin ciki marar algus. She felt her soul going for her.

"Sakinah lafiya? Meya faru? Meya sameki?" She asked, looking between a profusely crying Sakinah da kuma Aunty Halima data saka ido kawai tana kallonsu.

"Mama wallahi bansan me ya faru ba, tun kafin 7 tayi ta shigo gidannan tana wani irin kuka ga zazzabi ya rufe ta. Da kyar na samu tayi shiru tadansha juice sai ta kwanta, to yanzu shine ta tashi. Sakinah dan Allah ki fada mana abunda ya faru." Aunty Halima ce ke magana, itama muryarta tayi wani irin karyewa, dan wallahi bata jin banbancin Sakina da Safiyya har cikin ranta.

Ajiyar zuciya Sakinah taita saukewa kafin a hankali ta dago fuskarta mai cike da tarin damuwa, ji tayi Mama ta janyo ta jikinta giving her the best motherly hug she had never received in her life. She felt unscathed and urge to pour out whatever it is within her heart.

"Mama, tsoro nakeji, Mama shikenan na rasa darajata da mutunci na. Mama yanzu babu wanda zai so ni ko? Haka nan zan kare ko, Mama? A wulakance har Inna ta gaji da zamana gidanta ta koreni." Har ranta takejin kuna, ita yanzu bataki Allah ya dauki ranta ba.

Patting shoulders dinta Mama tayi, "Sakinah ki saurara kinji? Babu wanda zai tsaneki, ki fada mana me yake faruwa kila akwai hanyar da zamu taimaka maki. Komai yayi zafi maganinshi Allah."

"Mama tunda nabar gidan nan na fara suyar awara a bakin layinmu, I hate what I do with passion, amma Inna wouldn't hear a word of it. Sai ya zaman mani dole nayi, because that's the only way I get to eat, Inna ta daina bani abincinta. There's this guy we got acquaintance with, ashe cutata zaiyi Mama. Jiya da daddare he told me nazo muje ya siya min ice cream, he promised me dama. Sai na bishi, saboda kullum I make sure I do something bad wanda za'a fadawa Inna ko dan tace in daina soyar awarar tunda iskanci nake, I thought it would help. Ashe ni nake saka kaina ciki. He was with three friends of his, and they raped me, they raped me of my chastity, Mama. Suka yarda ni a cikin wani layi suka gudu, it was late at night..." she couldn't continue, it felt more painful now that she was reminiscing it with both her mind and her lips.

Mama soothed her shoulders and urged her to continue, "Zazzabi ya rufeni, Mama, ga heartbreak din dake ci na. So I slept off a bakin wani shago, dan wallahi ko hauka nake ban isa na koma gidanmu ba; kasheni zasuyi. Ya T will make sure I rot to hell, Inna kuwa dama tsineman ne kawai bata taba yi ba, nasan yau sai nasha ta kwando kwando, tun jiyan ma. I'm tired of living anymore, I want to die...." Mama had to use her palms to block Sakina's lips from uttering whatever it is she wanted to utter.

"Kul, kar na sakejin kin fadi haka. Ba Allah bane ya halicce ki? Shin da baisan akwai amfani a rayuwar ki Sakinah da tuni ya dauki ranka. Suicide thought should never come to your heart, believe in Allah, he hears, he sees. About you being raped kuma, that's your destiny, sh ake kira da kaddara Sakina. Allah ya kadarto ga abunda zai faru da rayuwarki dole kuma ya faru dake. Even though I hate to say this, but you have your own share on this. Me zaisa dan mahaifiyarki bata kyautata maki kice sai kin rama? Me zaisa dan tana muzguna maki kice dole kiyi inventing ways din da zaki bata mata itama? Kinsan had it been revenge wasn't on your mind, saurayin nanbazaki bishi ba balle har haka ta faru dake. I'm not judging, amma kin tafka babban laifi, but that's what makes part in your destiny. Wannan shine Kaddarar Sakinah. Amma hakuri zakiyi, ki barwa Allah komai, zai miki magani kinji? Ci abinci ki kara hutawa sai musan yanda zaayi."

Dagowa Sakinah tayi daga jikin Mama tana share hawayenta, "Yanzu Mama ai ko wajen Allah banda zunubi ko? Wallahi Mama banaso, na rokesu suka ki dainawa, dan Allah banda zunubin zina ko?" Sai kuma kukan ya dawo mata sabo, duk iskancin Sakinah tana tsoron haduwarta da Allah, sai yasa sometimes takeyiwa Inna duk abunda takeso bawi dan tanaso ba, sai dan kawai ta fita hakkin Allah.

"Baki dashi Sakinah, kwantar da hankali, amma dukda haka kiyita istigfari kuma ki roki mahaifiyar ki yafiya, kila hada hakkinta yake bibiyarki. Ki daina fushi da ita, kome zatayi maki kiyi hakuri kinji?" Sai yanzu Aunty Halima ta samu bakin magana, when she was able to stop the down pour coming from her eyes.

"Auntynmu wallahi Inna da Ya T kasheni zasuyi, wallahi ni nasani."

Sai ta kara bawa Mama tausayi, lallashinta ta farayi kafin ta samu dakyar Sakinah ta mike domin tayi wankan tsarki ta samu tayi sallah. Tare suka shiga Mama ta dan gyara mata jikinta ta fito ta barta dan ta kintsa taci abinci. Parlor ta koma ta kira Aunty Halima, jugum jugum sukayi su duka biyun, amma kowannen su babu abunda zuciyarshi take saka mashi face halin da Sakinah take ciki.

"Mama yanzu ya zaayi? Nidai wallahi ta bala'in bani tausayi, kuma yayan nan nata dan daba ne wallahi, babu abunda bazasuyi mata ba." Aunty Halima ce ta fara magana, gaba daya abun ya damesu kamar akan Safiyya ko su Muhibbah abun ya faru.

"Halima yadda na lura yarinyar na kwata kwata ina iya cewa batayi sa'ar uwa ba, ace kanada diya budurwa amma wai ka daina bata abinci dan mugun abu? To how would you expect ta fada maka damuwar da take ciki?"

"Wallahi kuwa Mama, kuma kinsan cikin gari; yanzu abun nan na shiga unguwarsu shikenan ta rasa mijin aure sai dai wata ba ita ba. Kuma worst thing din shine, iyayen sun turasu aikatau ne fa saboda idan aurensu ya tashi wai suyi ma kansu kayan kitchen, could you imagine? Ina tausayin Sakinah wallahi, amma for sure zata dawwama a bakin ciki kenan babu ranar fita."

"Ba za'ayi haka ba Halima, zata fita da izinin Allah. Ni zan maidata da kai na yau, zan kuma san abunda zan fada masu a rufe wannan maganar; amma indai Sakinah lives in the area dole a san abunda ya faru da ita. For that, zan nema ma Arhaan aurenta a yau dinnan insha Allah, that's the least I could do to save her life."

Anzo wajen😁

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now