Sama sama cikin bacci taji saukar bulala, ko ba'a fada mata ba tasan cewar Inna ce ta fara gana mata daya daga cikin azabobinta. Wani kukan zucci ta saki kafin idanuwanta suka fafa budewa a hankali, tabbas kuwa Innar ce tsaye kanta tana ta faman huci, kallon window Sakina tayi, and the sun that already peeked through the window of their room.
She jerked awake and blocked her eyes from the direct rays of sun that were threatening to block her eye sight. "Inna dan Allah ba sai kin tashe ni da ruwa ba, ko magana kika man zan tashi fah. Haba Inna yanzubin mura ta kamani fah?" Kuka ne yake san fito mata amma duk yadda zatayi sai datayi domin mayar da kukan ciki. Tasan kukanta a yanzu daya yake da karin azaba wajen Inna.
Daka mata duka Inna on the bare floor of her back, fuming with rage. "Dan ubanki inzo in tadaki kiyi sallar asuba Aa ashe ni kika maida sakara kika cigaba da baccinki ko? Zaki gane kurenki na rantse da Allah. Wannan kafircin naki na rashin san tashi sallah bansan inda kika samoshi ba, har can haka kike masu ko?" Inna ce ke surfa masifa, ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
Mikewa kawai Sakinah tayi tsaye ta nufi hanyar inda ta aje ghana must go dinta. "Kuma wallahi na baki minti biyar kiyi ki fito, sharar tsakar gidan nan kaf nake bukatar kiyi da kuma wanke wanke har nasu marainan wayon naki!" Inna thundered and made her way out of the room.
"Inna kinsan dai bazan wanke ma su Maman Iliya ba wallahi, wannan matar ba karamar yar rainin wayau bace, yanzu kuma rainani zatayi ai." She grumbled and began stripping off her drenched clothes.
"To dan ubanki sai kinyi, gara ma kiyi cikin arziki ba cikin masifa ba. Kuma wallahi ki gama zagaye zagayen naki ugubar da zaki tsinta cikin gidannan sai ta fiye maki cin mutuncin mijin matar nan. Ke daga yau ma awara zaki fara saida man kofar gida, inga uban da zai hanaki ko shi wancan tambadadden." Inna na furta haka cike da masifa ta fita daga dakin, making way for the hot tears burning Sakina's eyes down her cheeks.
Share hawayenta tayi amma she became stiffed. Wai yanzu ace mahaifiyarka ce haka, ita fa ya kamata ta tsaya taji menene damuwarta, amma how ironic ita tana fadin zata gana mata azaba, shin dama akwai iyaye haka? Kawai dan taki zama inda za'a wulakanta ta aci mata mutunci? Ko kuwa dan yanzu tana ganin bata aikin da zata samo mata wani abun duniya? Ko gani take dan ta daina aikatau to yanzu bata da damar yin kayan kitchen da kanta in aurenta ya taso? Hakan na nufin ta kara masu hidima akan tasu?
Wasu kam sunyi dacen uwa, amma banda Sakinah.
Share hawayenta tayi, jin wani zaginda Inna ta kundo mata daga tsakar gidan. Swiftly ta ida zare kayan ta saka new ones kafin ta fita daga dakin. In less than 10 mins ta gama sallah amma sai tayi zaune ta kasa tashi, har ga Allah bata saba rayuwar gidan nan ita kadai ba, ko wannan jarababben aikin safen ai ya isheta ukuba, inama ace Habibah na nan? Tasan da yanzu ta kusan gama rabin aikin.
Fita tayi sluggishly, amma still; wannan tunanin na kasan zuciyarta has never left her heart, ita kam yanzu in tayi maganar rashin lafiya ma Inna sai taji kamar ta yankata. A hankali ta fara sharar tsakar gidan, tanajin kamar zuciyarta ta fito daga kirjinta, duk ta rasa sukuni ta rasa abunda yake mata dadi.
Tun kafin ta karasa sharar tsakar gidan Inna ta fito ta fara mata masifa, ta inda take shiga bata nan take fita ba, ita ala dole Sakinah tazo tayi sauri ta gama tayi wanke wanke, dan ko maganar abincin da zataci batayi ba. Kuka ne kawai ya kufce wa Sakinah, a daidai lokacin da Baba ya fito daga dakin domin zuwa wajen aikinshi.
Yana ganinta yaji tausayinta ya kama shi, dan dama tun jiya da daddare Inna ta isheshi da masifa akan Sakinah ta dawo, dan ko a jiyan baiga Sakina ba inba yanzu ba. Baba karasowa yayi wajenta ya dagata da hannunshi, Inna na kallonsu baki sangale haka har ya karasa da Sakinah saman tabarmar dake shimfide cikin inuwa.
"Ke kasance mai sanyin rai da tausayawa akan ya'yanki Atika, ina guje maki ranar da wannan masifar take zata zama silar jefa rashin tausayinki a cikin zukatansu." Baba na furta hakan ya koma dakinsu ya dauko kuka da kosan da Inna ta bada aka siyo masu da safe. Kasantuwar yau monday yasa yake azumi, amma gudun masifar Inna yasa bai futar cewar yana azumi ba, dan kuwa daya fadi haka to tabbas zatace dan bayasan ya bada kudin abun kari sau yasa sai wani labe da azumi.
Fitowa yayi ya dawo ya zauna kusa da Sakinah wanda babu abunda takeyi banda kuka, har wani ciccijewa take tana shesheka, Inna kuwa tun wani kallo da Baba yayi flashing mata yasa tayi gum da bakinta, dan duk abunda tasan yau idan ta tanka shi to dole sai tayi regretting. Yanada hakuri, amma she knew not to feed him up.
"Karbi kici Sakinah, kiyi hakuri da duk wata rayuwa da zata zo maki. Allah ya baki wata irin uwa da sai wanda yaso jarabta yake bawa ita, kiyi hakuri da duk yanzu rayuwa tazo maki kinji? Allah zai baki ladar yi mata biyyayya." Baba ne yake patting while uttering these soothing words to her earshot.
Dagowa tayi da rinannun idanunta ta saukesu akan Baba kawai ta kara fashewa da wani kukan. Riko hannunshi tayu tana wani gunjin kuka "Baba kwata kwata rayuwata bata man dadi, na rasa duk wani farin ciki da nakeji a duniya. Zuciya a koda yaushe cikin kunci take, Baba na rasa gane hanyar da zan dosa. Habiba ce maj kwantar man da hankali yanzu itama bata nan. Haka duniya zata cigaba da kasancewa kullum ina cikin kunji? Wallahi Baba duniya bata da dadi."
Duk taurin zuciya irin na Inna hakan bai hanata jin wani iri ba, ganin yadda Sakinah ke kuka har can kasan ranta tana kai hannun Baba zuwa saitin da zuciyarta take mata kuna. Hakuri ya cigaba da bata har ta samu tayi shiru ta fara cin abincin kafin ya fita daga gidan ko kallon inda Inna take baiyi ba, dan haka In a bata samu damar tambayarshu kudin cefanan ranar ba.
"Yau kau zakici ubanki na rantse da Allah. Saboda ke ai ya futa daga gidan bai bani ko sisi ba, to wallahi sai na fanshe ta. Maza tashi kiyi wanke wanken nan kiji ki ranto mana waken suya, awara zaki farayi kofar gida. Ba dani za'ayi wannan iskancin ba, in kika bani haushi ko auren naki ya tashi wallahi ko tsinke bamuyi maki ki nemi uwar da zai maki na gaya maki. Shegiyar yarinya kawai."
"Innaaa..." maganar can kasan zuciyarta ta fito, dan tasan koda tayi protesting it's of no use to Inna, yadda tace din dole haka zaayi.
"Zakiyi ki cinye ki tashi ko kuwa?!" Ta daka mata tsawa wadda batasan lokacin da ta tsaida dukkan wani tunanin da takeyi ba ta fara turo koko da kosan da har ya fara sanyi.
•
Tun daren jiya baisan me yake damunshi ba, shi rayuwarshi bai taba shiga damuwa ba, koda ya shiga to irin minor abu ne wanda dayaje wajen Mama to insha Allahu ta gama kuka da abun har karshen rayuwarshi.
Safiya tayi, ya kamata ace yanzu yana shirin zuwa wajen aiki amma kwata kwata ya kasa koda motsi, kuma shi he couldn't point out abunda yake damunshi, amma yasan he isn't well.
Karar budewar kofa yaji a dakin, kafin Aunty Halima tayi uttering faint salam tana karasa shigowa cikin dakin. Tray ne dauke a hannunta da breakfast dinshi ne sai sauri take dan she has to take the kids to school ga hidimar gida ji take kaman tayi hauka, dan kwana biyu ta dan saba da Sakinah.
"Dan Mama ya baka tashi ka shirya ba? Ko yau bazaka je ba? Ga breakfast dinka nan, wallahi hidima taman yawa Arhaan ji nake kaman nayi hauka." Tana magana ta ajiye tray din a bedside drawer kafin ta fita daga dakin, dan yadda taga yanayinshi yau tasan bawai zau tanka ta ba.
Tana fita ya kalli abincin, haka kawai zuciyarshi take raya mashi da Sakinah na nan tabbas yasan ita zata kawo mashi breakfast dinnan, kuma kafin ta fita dole sai sunyi fada, ya zageta ita kuma ta dankara mashi bakar maganar da sai yaji kamar ta kamata yaita jibga.
"Kai Shawagababbe, wai bazaka tashi ba ka wani kwanta kayi male male kaman an narka kitse?" Haka kawai yaji amon muryarta cikin kunnenshi, dan karamin tsaki yayi amma haka kawai ya tsinci kanshi da dan karamin murmushi tunawa da yayi da jaraba da masifa irin ta Sakinah, a haka demeanor dinta baka cewa zata iya bala'i.
"Kai dallah tashi!" Kamar gata gashi haka yaji sautin ta, kuma ya tsinci kanshi da mikewa-amma amsawar da kashin kafarshi yayi ya tuni mashi da karayar dake jikinshi da kuma wadda itace silar hakan. Nan take yaji tsanarta ta cike mashi zuciya.
Nagode
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...