Jijiyoyin wuyanta babu wacce bata fito waje ba saboda tsoro, kallonshi takeyi ido cikin ido, a hankali kuma hawaye na zarya saman cheeks dinta. Ita bata taba ganin rayuwa irin wannan ba, miye laifinta dan tace tana san waya da mahifiyarta? Shi ba da tashi mahaifiyar yayi waya ba? Ko kuwa dan salon mugunta sai ta zauna ko falon da take fita tana samun sauki ya hanata kuma bazatayi waya da yan uwanta ba?
Kallonta yake cike da tsana yana tariyo maganganun Mama, this was the first time da Mama ta taba yi mashi magana cikin bacin rai. Shi baisan fushin ta ko bacin ranta ba, amma saboda wannan yar aikin gashi yau Mama shi taima furuci cikin bacin rai.
"Yanzu kenan Arhaan duk irin magiya da lallamar da nake maka ban isa ba? Dan tsabar zalunci irin naka ko iyayenta baka taba kira mata ba? Yanzu daka zaunar da ita cikin gidan ga azaba dame kakeso taji? Tunda hakane karka sake kirana har sai ka tabbatar tayi magana da iyayenta." Ko tsayawa taji me zai furta batayi ba ta kashe wayarta.
"Kayi hakuri," Sakinah ta furta cikin sanyin jiki, wasu hawayen na zarya saman cheeks dinta. Wani wawan tsaki yaja wanda saida ya kada mata yan hanji.
"Hakuri my foot! In baki daina wannan halin munafuncin naki ba wallahi tallahi sai na lahira ya fiki jin dadi na. Kinsan nasan this isn't the real you ko? Ko zaki fake ne da wannan auren kina acting haka? Ke wai ko taba tunanin how I'm your husband baki yi ba? You know so well babu compatibility tsakanin mu, I'm far more than you are. Amma dayake kwadayin abun duniya ya mike yawa? Shine saida kukayi yadda kukayi keda poor excuse of your parents kuka saka mata ta auro mani ke? What do you want to talk to her for? Kice mata a kara zuwa wajen malamin for me to be head over heels for you?!" Girgiza shoulders dinta wanda hakan ba karamin kidinar da Sakinah yayi ba, not to talk about the words he uttered to her.
"Ki fada man, wani asirin your pathetic excuse of a mother zata kara yi a kaina?!" Ko rufe baki baiyi ba hannayenshi dake saman kafadarta suka fado kasa, kallonta ya tsaya yanayi ganin zallar bacin rai da kiyayyar shi cikin ranta.
The old Sakinah made an appearance a kanta, she was looking at him infuriately with no sign of respect, sai ma hatred din dake cin zuciyarta. "Kayi kadan! Ko kadan baka kai matsayin da ni da mahaifiyata zamu aikata shirka a kanka ba. Kai nan har tunani kake ka taka wani matsayi a duniya da za'aso a bika har a saba ma ubangiji a kanka? Duka dukanka kai waye? Nasan ban kai matsayi da darajar ka ba, banyi karatu a inda kayi ba, bana living life din da kakeyi, my parents aren't rich like yours. But what's the difference? Yadda kake da hannuwa biyu nima sune a jikina, kafata biyu taka biyu, kai daya gareni kaima hala, hanci, ido, baki, kunne, duk nawa irin naka ne. Zuciyar dake bugawa a kirji na daya ce haka zalika kai ma taka daya ce rak! Idan ka isa, kana tunanin kana da wani matsayi a idon duniya da Allah, Arhaan ka chanza ma kanka halitta, ya zama na duk doron duniya kai kadai ka fita unique, that's in har ka isa.
Kuma da kake maganar munafunci, I'm acting all saint just because naga we're married ko? Kai ko kunya baka ji ba? Da ace kai din ke gabana, da tun farkon haduwar mu ban maka abunda nayi ba. Da kai ne abunda nake bibiya, da ban tunzuraka na saka maka tsanata ba, da kai din wani abune a idaniyata, da bazan tana saka Ya T ya lakada maka bugun banza ba kuma yasha lallai ba. Kuma kamar yadda ka fada, mashayin ne; amma duk shaye shayenshi ya fiye mani kai sau dubu, ya fiye mani duk wani abu daka tara ko zaka tara nan gaba, wani suna, nasaba da isar mulkinki are nothing compared to him in my life!
Inda wannan wahalallen auren ne a gabana, Arhaan da bamu kai haka muna fada ba. Kai bari fa kaji, wallahi tallahi idan naso da tun ranar da aka kawoni cikin gidan nan sai nasa ka durkusa kasan guiwowinka kana rokana, sai nasa ka zama bawa na, ka zama rakumi ina jan akalar ka a duk inda naga dama. Amma saboda baka gabana, kallon banza ma baka isheni ba, duk banyi haka. Kuma wallahi babu boka babu malam sai ma hargitsa duk wani tunani da kake takamar kana dashi, sai na kwance duk wani daurarren noti da yake kanka."
Hawayen ma kwata kwata sun daina zuba, bakin cikin data kunsha tun lokacin data shigo gidan ta sauke mashi san ranta kafin tayi hanyar toilet din. "Idan ka gama tsayuwar ka fita ka rufe mani kofa. Kuma karka siyo wayar kaga idan zan mutu dan banyi magana dasu ba." Tana fadin haka ta shige toilet din ta rufo kofa hade da danna mata lock, kuka ne ya kufce mata dan haka ta zube kasan toilet din tana dizgar kukanta. Bata damu da cewar yana cikin dakin ba, ita dai kunci da bakin cikin da yake cin ranta ya mata yawan da bata iya jurewa.
Arhaan ya kusan 30 minutes a tsaye cikin dakin yana jin fitar sautin kukanta, yadda yake fita da wani amo mai dauke da karsashi da tarin bakin cikin dake cin zuciyarta. Gaba daya sai yaji ya rasa abunda yake mashi dadi, wani irin guiltiness ne ya fara seeping into his soul. Zai iya cewa yafi kowa sanin dadin mahaifiya, why would he accuse her mother with that? Me zaisa yace ma mahaifiyarta haka?
Jiki a sabule haka ya fita part din nata gaba daya, ga abun Mama ga kuma maganganun Sakinah that are making him more guilty. Barin gidan yayi gaba daya, saida ya kusan hour yana yawo cikin garin Abuja without no precise location to go kafin ya dawo gida. Direct part dinshi ya shiga yayi wanka kafin ya tura ma Mama goodnight text.
Sakinah kuwa saida ta share fin hour zaune cikin toilet din tana sharbar kuka, saida ta gaji dan kanta kafin ta watsa ruwa ta fito, wankin ma batajin zata iya yinshi. Dan haka koda ta fito ta chanza kaya zuwa na bacci gado kawai ta nufa, a hankali bacci barawo ya sace ta amma still tana sauke ajiyar zuciya.
●
Da safe Arhaan yana tashi yayi wanka, haka kwai ya tsinci kanshi da zuwa part din Sakinah, yasan bai zama lallai wannan masifaffiyar ba ta mishi breakfast yau, amma to his surprise, yana zuwa ya iske daga dining table din har gidan gaba daya ko ina kyalli yake ga abinci na zube lafiya lau.
Sai yaji ta bashi tausayi. Maze fuska yayi ya wuce ya zauna yaci abincin shi, yau ko arzikin serving din bai samu ba. Amma he could remember shi da kanshi yace kar ta kara barin su hadu da ita. Yana gama cin abincin ya fita yabar gidan, direct shagon saida wayoyi yayi, da har yace a bashi wata infinix sai idanunshi suka fada kan iPhone6 rose gold, yasan bai zama lallai ta iya amfani da ita ba, amma still yace a bashi.
Wani ice cream parlour yaje ya zauna kafin ya kira wayar Safiyya ya fada mata ta sameshi inda take, amma kar ta fadawa Mama ko Mommy cewar shi ya kirata, tace school zata. Baifi 40 minutes sai ga driver ya aje Safiyya, saida ya siya mata ice cream kafin ya wuce da ita gidanshi, so yake ta debe ma Sakinah kewa yau, amma main aim din shine ta koya mata yadda zatayi amfami da wayarta.
Saida yayi parking kafin suka fito a tare, har sunzo zasu shiga gidan suka hango Sakinah area din garden tana shanya kayanta, Safiyya dayake magana bata mata wahala, har wajen ta taka, kafin ta isa Arhaan ya tsayar da ita.
"Yaya wanki naga tayi, dama baka kai mata kayanta wajen laundry ne?" Tambayar data mashi kenan, ji yayi yama rasa me zaice mata, shi tsoronshi daya karta fada ma Mama.
"Kinga Safiyya, banma san tayi wankin ba. Karki fadawa Mama dan Allah kinji?..." bai ida magana ba Sakinah ta dauko bucket dinta taci karo dasu, dan dole ta tsaya tana kallonsu, at the same time idanunta suka fada cikin na Arhaan. Ji yayi kamar an dakar mashi zuciya ganin yadda eyes dinga sukayi luhu luhu alamar taci kuka har ya mata yawa.
"Karbi wannan Safiyya, I'll text you yanzu." Yana furta haka bai kara kallon inda Sakinah take ba ya wuce part dinshi. Kafin daya daga cikinsu ya motsa text ya shigo wayar Safiyya.
~Safiyya give her the phone and show her how to use it please. Don't tell Mama anything kuma, please.~
"Aunty Sakinah, ina wuni?" Safiyya ta furta with a full smile tana taking dinta into an embrace.
"Lafiya lau Safiyya, ya su Mama?" She asked, while they make way to her part.
"Su Mama lafiya lau duk suna gaidaki." Yadda tayi da fuskarta haka kawai Sakinah ta tsinci kanta da dariya, she looks so much like Arhaan, ta raya a ranta.
YOU ARE READING
THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅
General FictionLittafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa. Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso. Shin wannan hanya...