BABI NA SITTIN DA BIYAR

1.7K 259 44
                                    

Tsayawa yayi yana kallon kofar da Sakina ta kulle, mamaki ne ya kamashi, gashi kuma he couldn't move an inch. Shi fa ganinta kawai yakeso yayi, baice dole sai tace har yanzu tana sanshi ba, ta tsaya ma ta saurari cewar yana santan kadai ya isheshi. Wai shin dama haka soyayyar take? Dama haka taji time din data fada mashi tana sanshi amma ko kallon arziki bai mata ba? Ashe dama soyayyar haka take da ciwo?

Shi idan ya zauna yayi tunani bai iya tuna ranar da zaice yau soyayyar Sakina ta shigeshi. Shidai yasan tun ranar da ya kusanci Sakina kuma yaga ba virgin bace daga ranar komai na rayuwarshi ya tsaya mashi cak, wani irin kuna da bakin ciki yakeji har kasan bargon zuciyarshi.

A tunaninshi idan ya maidata gida ya daina ganinta komai zai dawo mashi kamar yadda yake da, sai ya lura rashin ganin nata ma shine azaba mafi muni daya taba yiwa kansa. A haka ya daure ya hakura, kuka ne kawai baya iyayi, baisan da wata matsala zaiji ba, komai ya hadu ya cakude mashi waje daya.

First ganin daya mata bayan wata biyu ji yayi kaman an sauke mashi wani dutse a zuciyarshi, a lokacin ya tabbatar ma kanshi tabbas yana san Sakinah, kuma bawai zaman da sukayi bane yasa ya fara santa, Aa tun zaman da sukayi gidan Aunty Halima. Bai tabajin dukan zuciya ba kamar yanda yaji a time din da ya karanta takardar asibitin nan, he felt that he couldn't just accept the pregnancy like that.

Baisan abunda yayi holding dinshi back ba lokacin da Ya T yake dukanta, yana alakanta shi da kalmar raping din data furta an mata. Shikam kanshi duk ya daure. Yanzu gashi wata daya kenan amma Sakina ko kallonshi batayi, ko waje daya ma bata yarda su zauna. He needs her more than anyone a rayuwarshi.

A hankali ya taka yaje bakin kofar dakin, softly yayi knocking kofan, yafi five minutes yana knocking kofar nan amma ko kadan Sakina bata nuna cewar taji knocking dinshi ba. Dama time din la'asar yayi, har ya gaji yaje yayi sallah ya dawo. Ya gaji da wannan zaman enemies din da sukeyi, shikam he loves her with all his being, koma me zata mashi saidai ta mashi amma yau dole zasuyi magana, kuma dole zata kulashi, kuma dole zai nuna mata yana santa kuma dolenta ta yarda. Inma ta kama ya balla kofar to fa babu makawa zai balla kofar nan.

Wanka yaje yayi, dama kusan week kenan baya wanka sai after asr, ashe dama haka damuwa take? Shi tunda yake baisan mecece damuwa ba sai yanzu da soyayya ta sakashi cikinta tsundum.

Abinci ya fita waje ya samu yaci kadan kafin ya dawo gidan sai bayan Maghrib, gidan Mama yaje ya kwanta dakinta ya samu ya danyi bacci. Haka yakeyi kusan kullum, dan indai a gidanshi ne tofa lallai daya kwanta Sakina yake fara tunani, in kuwa a dakin Mama ne yakan samu ya danyi baccin.

Knocking ya fara yi mata, wannan karon da karfin gaske, "Sakina kizo ki bude mun kofa idan ba haka ba wallahi zan balla kofar nan. Sakina wai ya kikeso nayi da raina? Sanki nakeyi kamar rai na ya fito, to wallahi kina matata bazan wahalar da kaina ba, kizo ki bude man kofar nan Sakina!" Yayi threats din, yayi ban hakurin, yayi magiyar amma duk a banza.

Sallar isha'i yaje yayi kafin ya shiga kitchen, custard din nata ya hado kafin ya koma dakinshi ya fara laluben extra keys dinshi, dukansu ya kwaso yadda ma bazai rasa wanne ne na dakinta ba. Custard din ya aje gefe kafin ya fara trying. Duk wanda yayi trying baiyi ba sai yayi banging kofar akan ta bude amma Sakina taki bude kofar nan.

Saura key daya, tsayawa yayi yana kallon key din yana kuma kallon kofar dakin, "Sakina it's either ki bude kofar nan ko kuma wallahi tallahi na balla ta, kuma na ballata ni dake duka bazamu ji dadin daren yau ba. Wai me kika mayar dani?" Yana murza key din sai ga dakin ya bude, a zuciye yayi banging kofar ta bude, itama daidai da time din datazo zata bude mashi kofar, dan kuwa da tausayi da tsoro duka ya bata.

Turo kafar da yayi shine ya tunkuda ta baya tayi luu zata fadi yayi hanzari rikota hade da ajiye cup din custard din saman console din dake wajen kofa. Bai damu da masifar da zata mashi ba yayi hugging dinta very tight.

Mutsu mutsu ta fara akan tanasan kwatar kanta daga rikonshi, amma abunda ya bata tsoro shine kanshi dake resting saman neck dinta sai taji digar hawaye saman wuyanta. Hankalinta bai kara tashi ba saida taji yana shashekar kuka yana mata magiya.

"Sakina nasan nayi maki laifi mafi muni, nasan nayi maki promises din da ban cika maki su ba. Ki yarda dani, it's all because I love you. Babu namijin da zai tsinci kanshi a halin dana tsinci kai na kuma yayi acting less than I did. Nasan it was uncalled for, koma menene I should've listened to you amma banyi ba. Ki yafe mun Sakina, yanzu I'm ready to listen to all you'll say, I promise you zan yarda dake basai Mama ta fada man komai ba.

Sakina bansan ina sanki ba saida bakya tare dani, ki yafe man dan Allah, ki dauki duk abunda ya faru a matsayin kaddarar mu. Can you love and trust me again?" Kuka yake cancan karfinshi, muryarshi cike take da dana sani da kuma tarin nadama.

Tunda ya fara magana take kuka itama, a nan tsaye while hugged to each other sun kusa five minutes suna kukan, sai a hankali Sakina ce ta raba jikinsu ta riko hannunshi ta jashi har saida ta kaishi kan gadon suka zauna suna facing juna. Still basu daina kukan ba, itace ma tayi karfin halin goge nata hawayen kafin shima ta fara share mashi nashi.

"It's okay mana ka daina kuka, duk kukan na miye? Ba dan Anina ta yafe maka bane? Na fada maka tun ranar fa, nasan zakayi regretting amma zan yafe maka kuma zan fahimce ka. What again? Nasan for sure koda ace ni namiji ce nake in your shoes zan aikata abunda yafi naka ma, amma what hurt me was da kaki tsayawa ka saurareni, karshe ma fa Arhaan gida ka maida ni. Shin dama haka zaman aure yake? Ko kuwa haka soyayyar take?" Hawayenta ta tsaya ta share kafin ta kirkiro murmushin dole dan ta kwantar mashi da hankali, dan kuwa da alama kuka zai kwana yanayi yau.

"Ban taba sanin soyyaya ba sai a kanka, kasan yaushe na fara sanka? A asibiti, lokacin da nayi jinyar ka. Koda soyayyar ka ta shigeni ba shiga mai sauki ko tausayi tamun ba, inata denying but I couldn't hold it anymore saida na fada maka, I was hoping saboda girman soyayyar danake maka zaka tausaya man, amma what? Sai ka nuna daga ni har soyayyar tawa basa gabanka. But as I said, na yafe maka kuma I understand you.

Duk abubuwan dana maka bayan dawowata gidan nan ba asan raina nake maka ba, amma what? I want you to know what love pain feels like. Inaso kasan yadda kuna da radadin soyayyar yake, inaso kayi feeling koda kadan daga cikin abunda nayi feeling ne. So ka daina kuka kaji Dan Mama? Anina ta yafe maka." Hugging dinshi tayi a hankali tana kuka mai ratsa zuciya. Saida sukasha kukansu suka gode Allah kafin ya sakata dole sukaje ya hada mata wani sabon custard din tasha sannan suka dawo daki.

A hankali ta fara bashi labarin rayuwarta tun yarinta har zuwa sadda sukazo aikatau da kuma bayan ta koma gida da ranar da akayi raping dinta. Tana kuka yana kuka, kuka yake saboda dana sanin dayayi, ashe duk wannan pain din datayi going through bai isa ba saida ya kara mata wani? Duk inda regretting yake to Arhaan yakai. Ita kuwa kuka take akan wounds dinta da tayi uncovering, da kuma wanda dama they're still afresh.

"Sakina babyna! You gave me one amma nasa mun rasashi, bazan taba iya yafema kaina akan rashin shi ba." Yasan haka Allah ya rubuta, wannan duk yana daga cikin kaddarar su, amma kuma shine sila.

Hawayenshi ta kara share mashi tana girgiza kai alamar ya daina kukan hakanan, "Kaga fa shi a rayuwa komai da kaga ya faru da dan Adam to Arhaan haka Allah yaso kuma haka ya rubuta, bawa bai guje ma kaddarshi. Koda wannan abun bai faru ba tsakaninmu Allah ya riga ya rubuta dana da danka dole sai ya fita babu yadda zamuyi. Besides, na boye maka ne kawai dan ka kara feeling pain din abun kuma kayi regretting sosai, but babyn bai fita ba, ni na hana doctor din ya fada maka because time din I wanted to hate you kuma I was afraid tunda ka fara denying cikin you won't accept it koda nan gaba."

Wani irin ihu Arhaan yayi, Sakina batayi aune ba taji ya dagata sama kacokan yana zagaya dakin da ita. Hawaye yakeyi amma na farin ciki. Cike da dariya ta fara magana, still yana juyata tsakar dakin "Arhaan doctor yace banda girgiza mai yawa, still babyn sai ana lallaba shi." Ko second daya bai kara ba ya ajeta kasa and started showering her with kisses while telling her how she means to him and how happy she has made him in life.

THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH✅Where stories live. Discover now