WACECE ITA?💦.
*Page 3*
Na ummuzayd👌* Akwana a tashy ba wuya , ranan dazaa sallameta kuwa tashiga tashyn hankali dan tana tunanin inda rayuwarsu zata cigaba ita da danta, ga bawan Allah yayi kyau yayi bulbul kamar bashy ba ko ta ina alumar annabi taymaka musu suke da sutura da abinci ranan cike take da tashin hankali, tana zaune tana tinani wata attendant tashigo tace ina maman bawan Allah? Zeenatu dasauri tace gani gabanta nata faduwa, matar tace kije inji doc zaidd, amsawa tayi da toh ta tashi dasauri tatabi bayan matar, taje office dinsa tashiga tareda sallama, kallonta yayi sama da kasa ya kauda kai tareda fadin zauna, jikinta asanyaye tazauna tareda gayshesa ya amsa ciki ciki tace naggode da dawainiyar dakai damu Allah saka da alheri" ya amsa da ameen" yadanyi shiru can yace hope kinsan yau zaa sallameku ko?" ta amsa da eh jiki asanyaye" yayi dan nazarinta kadan tareda fadin inane gidanku?hankalin zeena nan da nan yatashy tafara hawaye "oh my God" yafada dan shifa ba abinda ya tsana irin atasa shi gaba ayita kuka irin haka"malama ban tambayeki dan kimin kuka bafa sonake nataymaka namaida ki gidanku tunda danki yasami lapiya!" ahankali takada baki tare da fadin "nima bansan gidanmu ba" dasauri yakalleta yace " wat!" baze tabaya yiwuwa ace bakisan gidanku ba sedae idan cikin shege kikayo aka koroki kokuma ki aikata wani mummunan laifi" kuka tasaka masa tareda fadin wlh doctor bansan waceceniba nidae nawaye garine naganni da cikin Abdallah har zuwa hayhuwarsa tacigaba da kuka kamar ranta ze fita, shidae zaid kasa cewa komae yayi yanata kallon zeenatu dataketa wani irin gunjin kuka kamar ranta zefita, yayi shiru yanata tunanin tokodae tayi loosing memory dinta ne? Abinda ya raya kenan ya kuma gasgata abinda ransa ya raya masa gameda ita, cewa yayi" kimin shiru yanzu bazan kara takura mki da tambaya ba, kije kidauko danki muje gidanmu kodan aiki kya dinga yi ana biyanki kamin kituna gidanku, tace toh taje ta hada kayanta akabata danta tareda magungunan sa tas sannan tayima yan dakin sallama suka tafi, bawan Allah ko nata barcinsa peacefully bemasan ya rayuwar take cikiba, haka ta sabashy abaya tadauke kayansu tabi baya doc zaid, yamata alama datashiga gidan baya tabude tatura musu kayansu sannan tashiga, ba wanda yacema wani komae har suka isa gidansu zaid dake g.r.a bayajidda road, yayi horn megadi yazo dasauri yabude yana masa sannu da zuwa shiko zaed ko kallonsa beyi ba yashigo da motarsa yayi parking, baba salele na ganin zeenatu yazo dasauri tareda fadin zeenatu kece haka Allah sarki yajikin na bawan Allah? Ta amsa" da sauki" tared mika masa dan ya amsa yana kallonsa, shikam gaskia zeenatu nabashy tausayi yaso zuwa dubata amma bayanda zeyi yabar vakin aikinsa, zaid ne yayi gyaran mirya tareda fadin"kijrani anan bari nama hajia bayanin aikin naki" ta amsa d toh doc" yana wucewa baba salele yace "anya zeenatu vana tsammanin hajia zata barki kizauna agidan nan inamik fatan alhery amma matar nan batada tausayi da kirki ko kadan haka yangidannan kaf suke, nima wani zubin senayi kamar nafasa aikin nan senayo tunanin iyalina dake kauye haka na nake hakuri balantana gaki ga da, abinda nake tsoro kenan, jikin zeenat yayi sanyi kalau tareda shiga tashin hankali, wannan shi ake cewa ga koshi ga kwanan yunwa dinfa kenan, suna cikin magana da megadi sega zaid yafito daga gidan ranshy a tsananin bace yace " zeenatu kiyi hakur ki koma inda kika fito dan hajiata taki yarda da aikinki a gidan nan" zeenatu tayi shiru hawaye nabin kumatunta tace" bakomae doc nagode d taymakon ka gareni Allah saka da alhery tajuya dasauri tadauki dan kayanta tasaba danta zta bar gidan, cike da tausayawa zaid yakirata " zeenatu" dasauri ta waigo tareda tsayawa a inda take kuka nason cin karfinta, karasowa yayi gabanta yamiko mata kudi yace gashy kisayi abinci, be saurari godiarta ba yajuya da sauri yabar gurin jikinta a sanyaye tabar gidan tafara tafiya zuwa inda tafito watau dan kongonta datake ganinsa kamar shine gidansu itada bawan Allah, ajiye kayanta tayi ta zauna dirshan a kasa tareda fara rera wani irin kuka mara sauti, dataga kukan baze mata rana ba ta tashy tafita tasiya masu ledar pure water tar da yar ashana da magani sauron rambo dan tasan danta dabe dade da farfadowa daga ciwo ba tavari sauro yamasa lahani kuma shikenan tadawo ta daura alwala tagabatar da sallolinta taja danta tazauna tafara gyangyadi, haka batasan sanda barci barawo yadauketa ba sejin kira sallar maribvtayi, dasaurimta ta tashy ta dauki pure water daya tadanyi alwala ta shimfide danta a yar zani tayi sallah tana idarwa kuwa ta tashy tabude kayansu tadauki magani tabama bawan Allah haka ta zuba masa ido yanata kallonta, kara jawo ledarsu tayi tadauko dan ragowar abincinsu na asibiti tasoma ci tarage na safiya dare yadan fara shiga tayi ishai takunnan masu maganin sauro tareda tofesu da addua ta kwanta nan tasoma barci, garina wayewa tayi sallah sannan tajawo ledarta ta kirga dan kudinta taga naira dubu arvain gareta tayi hamdala takara godema zaid tareda kara adana yan kudinta, tashi tayi ta fita tasamu napep tace malam dan Allah kasuwa zaka kaini, yace wacce tasamu kanta da cewa central yace tashiga haka tashiga taje kasuwa tamusu siyayyar bokiti dadan jarka taruwa harda pant tadawo, tasauka kenan aka napep tasamu motar wani alhaji akofar kongonta, gabantane yayi mugun faduwa tareda fadin hasbunallah waniimal wakeel!", kardae wanan shine megidan indae hakane ko tasan korarta zeyi "yanzu ina zanje?" Abimda tafadi kenan ntareda yin shahadar fadawa ciki kongon, shiko alhaji binta yayi da kallo tareda kara gasgata aikin bokansa megani har hanji, jindatayi shiru baa zo ankorota bane yasata watsar da tunanin ko me gidan ne, shiko alhaji bayan yaga shigarta yatada motarsa yabar wajen tareda tunanin yanda zeyi yazo d dare batareda kowa yagansa ba, ***Tunda magrib yagabato zeenatu takejin wani tashin hankali d faduwar gaba datarasa kona menene kara matse danta tayi a jikinta kamar wani zezo yarabasu, haka tayi ta addua a har wajen ishai dakyar tasamu barci me nauyi yadauketa wajen tsakiyar dare tafara jin ana shafa mata jiki firgigt ta farka tareda shirin kwalla ihu, akai maza aka rufe mata baki dole tayi shiru, mutumin yadaka mata tsawa tareda fadin kinamin n ihu wlh zan kasheki bawani abu nake nema awajenki va face kidan bani aron jikinki nadan mintuna, gabanta ne yafadi wani tashin hankali yakara ziyartart tareda wani tsananin bakin ciki, kasa motsi tayi tayi gum tanata jero addua cikin ranta, haka tanaji tana gani mutumin nan yamata fyade waiyazubillah😢 yana gama biyan buktarsa yatashy yabarta anan tafashe da wani irin kuka nafitar hankali lallae bataga amfanin rayuwarta ba kuwa, "Allahumma ajirni fi musibaty wa aklifni kairan minha😭ya Allah kai kasan halin danake ciki ubangiji kayi gaggawar daukar raina nasamu na huta da wahalar rayuwarnan!", kuka takeyi tareda jin wani irin tsananin bakin ciki lallae rashin shelter ma wani babban tashin hankaline da a gidansu take haka bazata taba samunta ba, kara rushewa tayi da kuka da ta tuna itafa ba kowa bace tunda bata iya tuna komae gameda rayiwarta,, haka taci kuka soasae kamar ranta ze fita dataga kukan baya mata rana ne yasa ta mike dakyar tanajan kafa tayi wanka da dan bahonsu ta tada kabarar sallah wanda tadade tana kuka.ahaka barci me Nauyi yayi awon gaba da eta. 💦💦WACECE ITA?💦💦
*page 4* na ummu zayd👌🏽 ***Zayd ne zaune adaki shiru shikam yarasa dalilin dayasa yaketa tunanin zeenatu kusan kullum da tunaninta yake Kwana yake tashy, wani dan guntun tsaki yaja tareda dajin haushin zuciyarsa gameda addabarsa tunanin wacce besaniba , zumbur kamar wanda aka tsikara haka yatashy yadauki key din motarsa yafito yana kiran salele megadi, wanda ya ansa yafito dasauri ya tsugunna tareda cewa ina kwana ranka yadade, dakyar ya amsa tareda danyin jim sannan yace"salele kasan daga wani waje maman bawan Allah takeda zama? Salele yayidan Jim sannan yace" wlh yallabae bansani ba tana zuwane amma Allah besa nataba tambaya ba.. ..zaid ne yayi saurin dakatar dashy tareda da fadin ok kana iyatafiya yayinda yashige motarsa cike da bakin cikin rashin sanin inda zenemo wannan baiwa Allah.
A haka rayuwa tacigaba da garama zeenatu Tun tana tsoron dawowar alhajin Nan hardae ta dena tunda gashy yau wata uku kenan besake dawowa ba haka tasaki ranta kuma ikon Allah bata sake zuwa gidansu zaid ba tunda yanzu Allah yarufa mata asiri tasamu wanke wanke awani restaurant kobanza tana samyn Na kashewa kuma dan abincun dayarage takan hada tacinye wani zubin harda dan guzurinta musammn ranarda ma da baasiye abinci ba, yauma kamar kullum zenatu tanacikin wanke wanke ogar gurin tayi kiranta, zeenatu kizo kihada sauran wanke wanken nan daakaci abinci!", toh! ta ansa tareda tashy domin bin umarnin megidarta, ta shigo tana hada kayan kenan Idonta yahadu dana lubabatu aekuwa batasan sanda taje dasauri tarungumetaba har jikinta na kyarma lubabatu bata ma lura da ita b taji anrungumeta gawani masifar karni daga jikin matar cikin masifa luby tahanakdeta tareda fadin wat d fuck!? are u out of ur senses kuwa? Ido jajir zeena ta dago takalli luby wanda se asannan luby ta kalli fuskar tabbas ZEENA ce, cikeda mamaki takefadin"dan Allah maman bawan Allah kiyimin afuwa wlh banganeke bace kinsan duniar ce daban tsoro, zeena tadanyi dan guntun murmushinta tace bakomae luby suka gaysa sannan kowatayi dan Jim Sannan lubyn takada Baki tace ina bawan Allah zeena tabata amsa da yana Nan lpy gashy can yana barci itada duk jikinta yayi sanyi dan ganin canzawa luby din, luby tasake cewa kekuwa zeenatu haka zumunci yake kosau daya vakizo gidana ba nashama baban ilham maganarki harnagaji...... Zeena takada baki zatayi magana taji muryar hajia zuwaera nafadin wannan wane irin iskancine kihado kayan kiwanke kintsaya tunanin naki na banza harda customer sunzo kina shirme gaskia kinkusa kaini bango!", zeena jiKi narawa batama tsaya sallama da lubyn ba ta kwashe kwanukan tabar wajen, lubabatu tabita da kallo cike da tausayi takira hajiya ashe yayar maman luby ce tace haba inna (sunan dasuke kiran hajiyar kenan) hakuri akeda jamaa kinga wlh Nina tsaidata sbd tare muka kwanta a asibiti da danta lokacin dana hayfi abdulshakur wlh inna matarnan tana cikin damuwa....... Hajiya tayi saurin katseta tareda fadin"dallah tafican sokuwa uwar jajibe jajibe kekam bansan irin halinki ba luba, kinga ina rabaki da Sharrin mutane! hka dae luby tayi shiru batasake maganaba dantasan innar tasu akwaea sababi.Haka luby dae tayi shiru tana sauraren inna, can tafaki idon inna taje wajen zeena datake fama da wanke plates tace sannu maman bawan Allah zeenat ce tadago fuskarta cike da murmushi tace Yauwa, luby tajnyo kujera tare da cewa zeena inata Kira naji kinxo gidana najiki shiru haka kuwa zumunci yake? Zeenatu taja dogon numfashi tace wlh bahaka bane maman Abdul aenaje Gidannaku aka ce kinyi tafiya, luby ta nisa tace haka kuwa akayi, ya bayan rabuwa da hidima, zee tace alhamdulilah kowa kam lapiyansa lau alhamdulilah, haka suka cigaba d hira yayinda zee take tafaman wankewanke itakuma lubabatu natayata hira, inna tazo wucewa tagansu sunata hira takama baki tace"oh ni diyar lawandi kekam luba kinji haushi watau maganar danamiki duk bata isheki ba kenan?"luby natamata signal tayi shiru taki tacigaba tareda dayimata dakuwa🖐🏼 watau nice ma kike mawa wanan kallo yaran zamani se a barsu nidae ina jiye miki tsoron jamaa ne atoh, haka dae inna tayita mita sannan tabarsu, bayan tawucene luby kefadin dan Allah kiyi hakuri zeena kinsan halin inna akwae mita, tace LA! bakomae wallahi, lubyn bata tafiba harsae yamma likis abban Abdul yazo daukarta takada baki tace zeee zomuje ku gaysa da babban abdul nasha bashy labarinki yau dae yaga zeeanatu dinnan, zee tace to shikenan aranta tana mamakin kirki irin na luby, tare suka jera har wajen restaurant din inna dae na kallon luby yayinda take mata kallon sauna, taja tsaki mtswww, wlh wannan diya da shanshanci kike mudae addua kawae zamubiki da ita Allah ya shiryeki luba, hakadae suka wuce sum sum suka bar inna nata sababi, suna fita suka samu yayi parking a kofar restaurant din suka gaysa luby tace abban Abdul yau dae ga zeenatu ashe tareda inna suke aiki, yakara fadada fararasa yace Allah sarki seyau Allah yayi zee tayi murmushi haka dae suka gaysa sannan tayi musu sallama abban abdul Yakawo dubu biyu yace gashy zeenat asiyawa abdul biscuit ta amsa tayi godia sannan ta koma yamma kuwa nayi tahada kayanta ta tafi kongonta.
![](https://img.wattpad.com/cover/163662843-288-k743104.jpg)
YOU ARE READING
WACECE ITA??
Espiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...