CHAPTER FOUR

3.2K 151 3
                                        

*💦💦WACECE ITA?*💦

*Page 7
        Alhaji shazali ne zaune a tamfatsetsen parlour dinsa wanda yasha kayan alatu na rayuwa kamar parlourn sarauniyar ingila😉iya tsaruwa y tsaru anyi aiki da boko sosae wajen shirya parlourn, abin dunia ne yataru yamasa yawa shikam yarasa yanda zeyi ya daina tunanin yarinyar ko rufe ido yayi gizo takemasa ga wasu irin mafarkai dayakeyi da ita yanzu ma zaman dayake a parloun nasa tunani yake barkatai gameda ita yasha zuwa wannan kangon gida saboda yaga yarinyar dayake tunani Allah ya jarabesa dawani masifar sonta dabaiko taba jin labari makamanci hakan ba, hajiya zulfa ce tafito daga daki tasami hannun kujerar da alhajin yake kai ta zauna, dan nazarinsa tayi nawasu sakanni sanan taja numfashy tareda dafa kafadarsa, firgigit yabude idanunsa tareda zuba mata mitsimitsin idannunsa a fuskarta, hajia zulfa aranta tagama kare masa kallo ikon Allah takefadi azuciarta inbanda kudi ni zulfau mezanyi da alhaji shazali, mutum ne murjejen kato baki sidik ga masifar muni, ke kyace wani yanki ne daga  launin mutan boye 🤣, kara kallonsa tayi tareda fadin"Alhajina nifa kwata kwata Kwana biyun nan narasa gane kanka baka walwala Sam gashy baka sakarmin dan Allah alhaji inwani laifi namaka kafada min sena gyara insha Allah nikam bazan kuma ba" takarashe maganar Kamar Zata fashe da kuka, kallonta yayi akaro nabiyo tareda buso iskar bakinsa ya firzar yawani bude rangajejen hancinsa kamar vijimin saniya na hamma yace, ba abinda kikamin hajia nikaina kwana biyu narasa abinda yake damuna wlh kedai kawae kitayani da addua Kawae, Hajia zulfa ta amsa da insha Allah tareda cigaba da kwantar masa d hankali shiyasa yake son hajiar duk iya aure aurensa yakasa rabuwa da hajiar macece wacce tasan kissa da kisisina mace kyakyawa dabazata gaza shekaru talatin da takwas ba yar duma duma, batada Makusa daga jikinta har fuskarta farace tas kamar balarabiya, alhajin ne yatashi tsaye da hanzari kamar wanda aka tsikara, hajiar zulfa takallesa, alhaji lafia ko wani abin ne dan tashyn dayayi bakaramin tsoro yabata ba, kamar yaga wani abin, murmushi yamata wanda kekara ma fuskarshy muni yace"zandan fita ne wlh akwae abinda yakamata nayi namanta" adawo lpy tamasa tareda mikewa tarakashy wajen motarsa sannan takoma, driver dinsa yama magana latif kakaini Eka kadai san inda kake kaini dinnan, eh ya amsa masa tareda yin reverse sukabar haraba gidan,shitunda wannan abu yafaru dashy shaf yamanta da mallam nakan tudu, sedayama lateef kwatance suka biya ta kangon gidan da zeenatu take kamar kullum se s hirginsu bakowa sannan suka Kama hanyar Eka, l...
Alhaji shazali ne dukufe gaban malam nakan tudu wanda ke kyace sujada zaya masa saboda tsabar yarda da shirka, malam nakan tudu yakalli alhjin tareda tambayarsa yau kuma d wacce akazo? Watau tunda bukata tabiya bankara jin labarinka ba" alhaji ya karkace kai kamar basamude yace watau laananne, boka ya kyalkyake da daria tareda fadin tunda kafadi sunan nan kozanyi yawo tsirara dole nabiya maka bukata, kaki Allah alhaji nima nakisa, fadi matsalarka"alhj yasake karkace kai yace"watau gameda aikin dakamin kwanaki ne nawannan diya danama fyade yakai tsinanne tofa yanzu jinake Allah yajarabeni dasonta........ Boka nakan tudu yabarke dawata arniyar daria can yatamke fuska yakalli alhaji shazali, watau yau ja'iri kafada soyayyar wacce bazae yiwu aikinmu yayi wani tasiri akanta ba abu daya ne zan baka shawara shine ayi aikin dazaka manta da ita inbahakaba gaskia sedae kamutu dasonta kuma kadaena nemanta dan inkasake kuka hadu kai mgna taji muryarka asirinka zaya tonu kuma tabbas zakai nadama jai'ri, alhaji jiki narawa ya amsa"toh toh Aida asirina yatonu gwanda kawae namanta da ita nima nahuta tababbe, boka yakuma kyalkyala dariarsa yace ja'iri ae sae katafi angama, baka kara tunaninta daga yau, alhaji shazali yaciro damin kudi ya ajiye gaban boka nakan tudu yace kakiyaye dokarmu duk randa kuka hadu Kada kasake kayi magana dan tabbas aikinmu ze karye,...... Godia yashiga yima boka nakan tudu tareda mikewa da baya baya ya bar dakin wanda shine dokar nakan tudu...                    💦💦WACECE ITA?💦          *PAGE 8*  Na ummu zaid👌🏽                            Lubabatu ce takalli mijinta bayan sungama cin abinci tace abban abdul munje asibitin, katseta yayi da ya akayi ne? Kunko dace? Bashy amsa tayida"to kamar yanda kace ko zeenatu nada amnesia haka likitan yafada amma yace zamuyi EEG kafin afara bada magani, amma dayake machine dinsu ya lalace sedae sukayi referring dinmu zuwa kaduna, abban abdul yakalli luby yace tofa abin yayi tsawo fatan mu Allah yasa baiwar Allah dinan tawarke tagano yanuwanta, insha Allah semubari next week kinga time din nadauki hutu na nashekara daganan kuma semuwuce wajen hajia muyi mata Kwana biyu, jikin  lubabatu  yayi sanyi saboda tunawa dasurukarta datayi data rasa dalilin da gwaggon ta tsaneta, kirkiro murmushi tayi tareda fadin Allah nuna mana ameen ya amsa dashy tareda bata umarnin dauko masa laptop dinsa dake cikin daki.
Washegari dasafe bayan abban abdul yafita zee tashigo dan taya luba wanke wanke, gaysawa sukayi luba natambayarta ya kwanan bawan Allah?  Amsawa tayi d lafiya lau tareda shiga kitchen tadauko break fast tafara karyawa suna dan taba hira jefi jefi, sedata kammala tayi wanke wanke sannan tadawo tazauna akasa tace "nikuwa lubabatu inataso natambayeki gameda abdul tunda naxo banganshy ba gashy nasan sa'an bawan Allah ne balantana nace ko ankaisa yaye?  Ran luban ne yabaci tareda fadin hmmm zeenatu kedae bari kullum da yarana nake kwana nake tashy araena gashy nahayfa amma kamar ban hayfa ba zee takalleta tareda fadin"kamarya?Luby takara kaurara murya dagani tanajin dacin abinda takeso tafada tace"wlh maman bawan Allah watau Allah yajarabeni da uwar miji dabata kaunata ko kadan duk sanda muka hadu zagi dacin kashy kehadani da ita, hartakai ga daukemin min ilham wae kada na koyamata munafunci, haka inaji inagani aka rabamu da diyata yanzu kuma saboda tsabar rashin adalci tazo tadauke abdul da ishaq yayi magana tasaka kuka wae ze nunamata iyaka da alamaryn yaransa haka inaji ina gani baiwar Allahn nan ta rabani da dana dayake shan nono yau watansa biyu dakomawa can kuma abin bakin cikin ma ba arabi b boko dan gwaggo kauyen kaduna takeda zama, haka yarana zasu tashy cikin jahilci ba ilimin lahira Dana zamani😭 zeenatu ta tausayawa luby sosae tace bakomae lubaabatu addua d hakuri shiya kamata kiyi tayi Allah nasane dasu, hakadae suka cigaba da tattauna matsalolinsu tareda yan nasihu.
Yau ce lahadi ranar da zeenatu zasuje asibitin psychiatry dake barnawa, kamar kullum tun karfe 9 suka bargida tareda hada kayansu suka saka a boot bawan Allah na hannun baban abdul shikam son yaronyake kamar dansa kodan rashin yayansa ne oho, luby ce gaba rike da bawan Allah yayinda zeenatu nagidan baya, tafiya suke luby da Ishaq n tattaunawa gameda alamaryn rayuwa itadae kosun sakota da ga eh ko aa batasake cewa komae, cikin awa uku yasada su dagarin kaduna garin gwamna, inda daganan suka yanke hanyar hayin danbushiya, parking sukayi a kofar wani gida dayaji sumunti malale a zaure sumul gidan yasha fenti peach colour kusan duk yankin garin gidan yafi kowanne kyau, wanda aikin ishaq dinne yagyara tunda bayanda beba gwaggo tadawo gari takiya, shiga sukayi tareda sallama assalamu alaikum, waalaika salaam aka amsa tareda fadin kushigo mutan katsina lale lale, shimfida musu tabarma matar tayi tace bismillah suka zauna aka soma gaysawa, Ishaq ne yayi gyaran murya tareda fadin, "baba hala gwaggo batanan? Inna tagyara zama adan kujerar datayi tsuguno tace"hmm kai dae bari isyaku wallahi audu(abdulshakur) shidinne jiki ba dadi ance wae aljana yar macukule ce ta kamashi yanzu haka maganar danake gwaggo taje kaishi Wajen tasalla me magani, yanzu ma kaga tadawo, tunda baaba kemagana ran Ishaq ya gama baci wannan wace irin rayuwace tabbas dole yasan nayi dan yasan ana zaluntar luba dan ma Allah yabashy mata me hakuri dawata ce da yanzu anyi tsiya, lubabatu dae kanta naduke saboda tsabar bacin rae tama rasa bakin magana, se wani hawaye dataji yana zubo mata lokaci lokaci tana sharewa, ita kanta zeenatu tana tausayawa luby gaskia dan zaman dasukayi talura macece me kawaeci inbadan ma ta tambayeta ba bagaya mata zatayi b, Ishaq ne yakara Kada baki yace ilham kumafa? ita tana ina? Kafin baba tayi magana Sega yarinyar tarugo cikin gidan a guje, yar karamar yarinya dabata wuce 3years ba amma saboda tsabar futu futu datayi kafar nan bako takalmi duk yasha kaushi ga wani bakin lalle anmata, fuskar nan duk majina, zuwa tayi tafada kan jikin baaba tana fadin, baba ki foyeni su murtala ne suka biyo mu zasu bigemu..... Baabar tawashe baki tareda fadin ilham bakiga su mamanki bane, lubabatu takai duba ga kyayawar diyata wacce ayanzu bata da maraba da kauye futuk, wani hawaye yakuma silmiyo mata gaskia tabbas an cuceta, ganin datayi intazauna awajen zata ita fashewa da kuka yasata tashy tareda shigewa dakin dasukan sauka wanda Ishaq dinne yagina musu, baaba tarike baki"oh ni ashalle Allah yakawo mu zamanin da dan yau baida kunya bare kara"Ishaq ne yakatseta baaba zaki Fara kema ko? Jan bakinta tayi ta tsuke Kada tama kanta bukulun kudin da Ishaq din inyazo yake bata, zeenatu dae jikinta duk ya mutu lalle kowa datashy salon jarabawar tana zaune tana sake sake sukaji sallama, assalamu alaikum, daga can aka kuma amsawa waalaiki salaam, gwaggo ce tashigo goye da abdul abaya kafar nan tayi futu futu kallon Ishaq tayi tace "aa ha saukar kuma yaushe, kallon innar yayi yagaysheta cikin washe baki ta amsa tareda da sauko abdul abaya, kallo daya Ishaq yayi masa yasaki salati gwaggo menene nake gani  haka? Gwaggo ce ta kara rike abdul din tareda fadin kaidae bari isyaku wallahi aljana ce takamashi garin nan yanzu ma daga gun tasalla me magani nake to ita batada makarin seda muka sada dazuwa can cikin kauyen tunburku, Ishaq yakalli dansa cikin bacin rai wanda yasan tabbas malnutrition(cutar yunwa) ke dawainiya dashy yarame daga fata se kashi gawani katon ciki him se kananan kafafu, tabbas dabadan uwarshy bace dase anmusu sharia, daure fuska yayi tareda fadin"haba gwaggo yanzu fisabillahi har yaro yazama haka baki kaishi asibiti ba haba gwaggo, kai da Allah rufa min baki kuda anyi magana sekuce wani asibiti mango park ma yaci kaniyarsa to ba inda zaakai yaron nan ehe!, seda tayi fadanta ma'ishi bece komae va kana takai duba ga zeenatu, wannan fa daga ina? Kada baki yayi yabata amsa da yayar zeenatu ce, gwaggo tadaure fuska yau kuma da kwashe kwashen daka zo kenan banda matarka kuma harda wata yaya wallahi isyaku ka kiyayeni saunawa zancemaka kadinga barin shirginka gida wae inama take, amsawa yayi da tana daki, au yanzuma kuma rashin daar hartakai da ban isa azo a gaydaniba Ashe, duk abinda akeyi luba na daki tanajinsu, dan haka tafito ta tsugunna tana gayda inna, ina yini, inna ta ansa dakyar tareda fadin watau rashin arzikin naki haryakai ki ki gaydani oh hi SAUDE na boni, anya isyaku haka wannan tabarka kuwa, itadae luba duke kai tayi tareda fakin ido takalli abdul, gabanta ne yawani buga, tareda jin wani bakin ciki na tasomata. Inna ce takuma cewa to isashiya ae se atashy abamu waje ko? Mikewa tayi dasauri tareda shigewa daki, yayinda zeenatu tabita abaya, luby tafada kan kujera tareda rushewa da kuka wannan wane irin daukar alhakine maman abdallah kiga yanda dannan yakoma gaskia hakuri na yakare tabbas bazan jure ba, dan yaranan amana ce Allah yabani, zeenatu tadafa ta tareda fadin maman abdul komae yayi zafi maganinshi Allah kuma tabbas ke jarumace, yanzu davara daya zaayi ahankali a kwace yaron nan........ Ina mafita?                             💦💦WACECE ITA?💦💦        *page 9*     na ummu zayd👌🏽                                   Zee tabata amsa da bari abban abdul yashigo seku tattauna kiyi hakuri kinji? Allah yamana maganin wannan masifa, ahaka sukaita tattauna matsalolinsu har azahar amma ko ruwa baa kawo masu ba.... Ishaq ne yashigo dakin rike da Leda aciki luby ta tashi ta amsa ledar tareda fadin sannu da zuwa, cikin Dari Dari ya amsa yace ina zuwa sake fita yayi yadauko wata ledar tareda jakar pure water, luby tatashy zata FItA yariko hannunta cikin sauri, zeenatu naganin haka ta tasshy takoma barandar wajen dakin Nasu tabasu waje, kallonta Yakuma yi tareda kasa da murya yace"haba habibty, bansan ki da fushi har haka ba nikaina nasan anbata miki luby dan girman Allah kiyi hakuri, saurin dakatar dashy tayi tace,baban ilham wallahi tallahi hakurina yakare ba uwar dazata yarda tanaji tana gani a amshe mata yara har Dana goye tayi shiru kasan Allah wlh da dana zan tafi kullum INA cikin zullumi akan yaron nan sekuma nazo natardashy ahaka, agaskia nagaji Abba, tafashe da wani irin gunjin kuka, sedatayi ma'ishi be dakatar da ita because koshy yasan she has to cry her sorrow out, shiru yayi nawadansu lokuta sannan yakalleta luby, kiyi hakuri bazangaji dabaki hakuri ba kuma tabbas nima yanzu yazama dole agareni nasan yanda zanyi na karbi Abdul bazan iya ganin yaron nan yamutu saboda yunwa ba alhali inada rufin asirina kiyi hakuri, lallashinta yacigaba dayi haryasamu tasakko daga fushin nata sanna n yatashy yace, ga kayan miya nan nasiyo dakayan tea seku girka abinda yasawwaka tunda nasan munada sauran avinci a store, gyada kai tayi tareda share guntun hawayen fuskarta, kira gwqggo takuma kwalamasa,isyaku! Isyaku! A sukwane yafice daga dakin tareda amsawa, naam gwaggo!, sababi tafara yi tana fading"oh ni yarnan wallahi kaji haushy isyaku kai haka zaka tabe a gindin mace ne? wannan irin jaraba har INA,shidae shiru yayi Dan beda tacewa, washe gari tun sasafe muka tashy muka gyara dakin saboda zamu tafi asibiti a brnawa, ilham CE tashigo dakin Muna tsaka da karin kumallo, luby ta kalleta ilham zo nan, yarinyar tana rabe rave tazauna kusa da uwar luby tace vaki gaydani da aunty ba tace INA kwana duk muka amsa, can tace wae kece mamana? Luba tace eh mana nice mamanki ilham takuma fadin to nima kitafi dani katsina,luby tashare hawaye Dan har ga Allah tanasan zama tareda diyarta, tace in anyi Hutu zakizo, nidae dabawan Allah a hannuna INA ta kallonsu cike da tausayi, can ishaq yaleko yace"inkungama kutaso mutafi kada muyi latti, toh" muka amsa dashi nadauko hijab itama luby tadauko tarike ma ilham hannu, yarinyar se tsalle tsalle takeyi, tana murna,biyawa mukayi ta dakin gwaggo muka gaydata wacce dakyar ta amsa kallo ma bamu isheta ba, sim sim muka mike tareda fadin semun dawo, gwaggo taki tankawa, kallon ilham tayi tace"yakinan ameena (sunan ilham nagaskia) yarinyar tanoke kafada tareda fadin uhm uhm ni maamana zani" ran gwaggo yavaci tafara sababi" watau luba har rashin mutumcin naki yakai nan, daga zuwa kwana daya rak kinfara hure ma yarinya kunne abinda nake jiye ma sakaran nan kenan yaki ji kissa da makirci ko karuwar legas albarka" mudae dasauri muka bar dakin mukayi waje wannan cin kashi har INA haka?, muna FItA muka samu ishaq ajikin mota yana jiran mu nashiga gidan baya yayinda luby ke gaba dauke da bawan Allah, tafiaya CE mukayita takusan awa daya zuwa barnawa Wanda  harmuka iso bawanda yace ma wani kala kai kace ba yan adam cikin motar, asibitin muka shiga inda akamana bayanin yanda  zamuyi abubuwa din mukayi sannan mukabi layi, ga de jamaa nan wasu  gwanin ban tausayi wasu kuma kamar lapiya lau,ishaq yana mota yanajiranmu munbarmasa ilham,  munabin layi  wata nurse tafito takirani luby tace" tashy mushiga maman bawan Allah, jikina asalube nashiga, mukayi sallama dan da alama likitar musulmace, ansa mana tayi tareda fadin bismillah kuzauna mana,  Neman kujera mukayi dake facing matar muka zauna, yan rubutu tayi akatin tadago takallemu, tace waye me damuwar acikinku?" Nice" nabata amsa sedata karemin kalllo nawasu sakanni sannan tace meye matsalar? Mikamata takardar referring din nayi nace daga  katsina aka mana referral, budewa tayi takaranta tareda kallona tsab tajeho min tambaya"accident kikayine ?" Bansani ba abinda nace kenan" wata takarda tabani tace ga wannan kuje kuyi hoto in anvaku result din kukawo Mani, na amsa Tareda tambaya" please where the is the side cause we re new" kwatance tamana mukayi godia muka fito, zuwa mukayi muka biya kudi a micro finance sannan mukaje wajen scan din layine mukabi nawasu awowi sannan aka kiramu,,tashy nayi nashiga akamin scan sannan mutumin yace mana segobe zamu dawo mu amsa result din, salama mukayi dashy nafito na fada ma luby tace Allah kaimu, zee fatan mu adace kisan Inda dangin ki suke " ahaka mukaje mukasami baban ilham ilham din ma tayi barci bawan Allah NATA koke koke mikomin shi yayi nace " vawan Allah abban zakama rigema"bani amsa yayi da" shaanin yarone ae yayi kokari Dan kundade, yakukayi ne?" Luby CE ta amshe dacewa result dinne ance se gone zamu amsa abban ilham yace" to Allah yakaimu amma anya bazamu kwana nan cikin gari ba saboda ayi komae agama jibi zamu koma katsina" luby tace " lapia habiby dawuri haka?" Amsa yabata dacewa" to yazanyi luba kinsman yanayin yanda muka ga Abdul sonake na lallaba na amshe sa muje asibiti Dan nasan wannan yanayi nasa nasan se anyi admitting dinsa" luby tace" hakane to kuma ita ilham fa? Shiru yayi yace luba nasan kina da fahimta kinsan shaanin iyayr se ahankali itama in sha Allah ahanakali zan amsheta kiyi ta hakuri yar aljanna nasan kinadashi kikara akan Wanda kikeyi kinji hayati?" Gyada kai kawae tayi" nidae ina bayan Mota ina vama bawan Allah nono, tafiaya mukayi Medan tazara tasadamu da unguwar tudunwada wani gida muka tsaya mukayi parking muka fito, gidane babban gida me kofuna a waje ishaq ne yabamu izini yace kushiga ganinan shigowa, shigewa mukayi mukayi sallama, wata year dattijuwa ce tsakar gidan ta amsa da faraata "ahh lake da mutan katsina tashi tayi ta shimfida mana carpet Tabamu izini muzauna ,zama mukayi aka kama gaysuwa daga ganin matar Nada kirki tashi tayi takuma kawo mana ruwa da burabusko akwano muka sake gaysawa takalli luby yace" diyata ina isyakun ne ? Yana waje luby tabata amsa, tasake cewa ae yace nan zaku kwana, ke amina zo nan, ilham tanoke kafada taki, rike baki tayi kaji yar nema to tashy zakiyi kibar min gidana tunda nizaki ki, bata amsa nayi da laa hajiya yazaki mana haka cikin wasa mukayi raha ,sannan tasa hannu ta amshi bawan Allah" kuci abincin luba "saka cokali mukayi muka ci abincin sannan bayan mun gama mukayi alwala mukayi sallah, hajia mero take cemana ai isyakun yakirani yacemin nan zaku kwana wae kina ganin likita Allah ya sawwake muka amsa" luba kiyi hakuri dda halin yayata Nina nasan bata kyautawa duk rashin fahimtace kinji ko" luby tadukar dakai tace" lah bakomae hajia " hajiayar tagyada kai munacikin magana ishaq din yashigo aka kawomasa abinci yaci bayan ishai aka nuna mana makwanci.

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now