CHAPTER FOURTEEN

1.4K 76 0
                                        


WACECE ITA?

PAGE 36

NA UMMU ZAYD

Bikin muqaddas da zeena, yarage saura kwana 5,duk wainar da ake toyawa mardiyya bata da labari lokacin suna jabi, gidan apartment biyu ne kasancewar komae a gyare yake yasa muqaddas beyi wani shiri va don kwata kwata ummi hanashi fada ma mardiyyar tayi don gani take zata iya ruguza auren, vangaren amarya kuwa komae yana tafiya daedae don masu gayaran jiki ummi tadauko daga sudan,  duk da ummin ba san auren takeyi ba don sam ummi nama zee tsoron kishiya, haryanzu bata daena jin zafin kin auren zee din dayayi daga farko ba, muqaddas ne yashigo parlour din mardiyya da sallamarsa, wacce kamar anmata dole ta amsa, guri yasamu yazauna tareda tattaro dauriya yafara magana:Babe kiyi hakuri kiyafemin abinda namaki, aure zanyi kifadama ni ko me kikeso zanbaki indae baefi karfina ba banyi auren nan dan bana sonki ba habibty, mardiyya wacce tayi mutuwar zaune saboda tsabar mamaki takasa motsa koda yatsanta,wani mugun kallo tajefa masa yayinda kamar an bata umurni ta tashi da sauri tadauko wani dan flower vase dake kan console dinta ta jefawa muqaddas, gocewa yayi da sauri tareda tashi tsaye ya kankameta, kasakeni muqaddas kasakeni nace!wlh uban kuturu yayi kadan ballantana na makaho ni nafi karfin zama da kishiya wlh! Cigaba da fadin maganar da duk ta fito bakin ta tayi tana yaba masa zagi kuwa ba irin wanda beji ba arayuwarsa, duk ta gama yayyaga masa fata da tsinin kumbarta kamar ta mage, sosae ranshi ya baci can kasan zuciarsa wani irin zafi yakeji gameda zagin nasa datakeyi amma sae ya sami kansa da rashin iya tabuka komae ganin zata iya masa lahani saboda yagar da take kaima sa yasa ya saketa ba shiri tareda ficewa daga gidan baki daya, sintiri ta fara yi a parlon nata tareda rashin sanin makamar dazata kama, lallae tayi sake kuma tasaki jikinta dahar zaa auro mata kishiya nasan babu wanda zasumin wannan tuggu sae uwar guzuma(sunan datake kiran maman muq din) dasauri tadauko wayarta tareda dialling numb din sholly, wanda ringing daya sholly tadauka, mardiyya tafara zayyano mata labarin abinda ke wakana, sholly data lailayo ashar tace:kan bura uban can muna ina haka ta faru ae yau wlh komae dare dole mutafi suleja wajen karkuzu yasan ma yanda zaeyi damu, ki kawo suhail yazauna wajen baaaba, mardiyya ta amsa da toh angama, tareda kashe wayar cikin minti kadan tayi shirinta ta wuce school dauko suhail ko lokacin tashinsa beyi ba amma hakanan ta rakito sa suka taho,
Shikuwa muqaddas dama yau zae wuce katsina saboda shirye shiryen biki koda yadawo bae tadda Mardi ba sanin halinta yasa ko damuwa beyi ba yahada kayansa tsaf sannan ya fita don jirgin karfe hudu zasu bi. Cikin minti 45 ya isa katsina, kaninsa hisham yakira yataho yadauke sa kodayaje gida ya cika da yanuwa da abokqn arziki sae hidindimu sukeyi hakan ba karamin faranta ransa yayi ba jin kansa yakeyi kamar wannan din shine aurensa na farko ko ina yayi washe baki kawae yakeyi kamar gonar auduga.
Mardiyya ce da sholly gaban karkuzu wanda yadago yana kyalkyalta dariaya kamar mahaukaci sabon kamu hakan dayayi ba karamin bakanta ma mardiy rae yayi ba ita yanzu bata ga abin daria anan ba ana cikin tashin hanakali yatasa su gaba yana daria, tsaki tayi a ranta tareda fadin"haba karkuzu yanzu meye na daria anan nifa zuwa kawae nayi kataymaka ka kawo min mafita....  Kallonta yayi tareda sake barkewa da wata dariar da tafi ta dazu 'mardiyya manyan dunia dariya daya nakeyi hango tsabar kishi a idanunki kada kimanta na fada maki komae daren dadewa muqaddas sae yayi aure da zeenatu ko bamuyi haka ba? Gaban mardiyya yasake faduwa kamar ansauko mata da aradu, ita saboda tashin hanakali bata ma san wa muq din zae aura ba sae yanzu,sharce zufar da take tsiyayo mata daga goshi tayi tace:to yanzu yazaayi karkuzu konawane zan biya kai ko kasheta ne wlh zan yarda ayi amma bazan iya zama da wata da sunan kishiya ba, karkuzu yakalleta dakyau yace"mardidi kenan bazae yiwu akasheta ba hakuri zakiyi nadan wani lokaci kadan da aikinmu zaefara tasiri akanta zan miki hadin dako tazo sae yanda ki kayi da ita zan daure bakin kowa duk halin data shiga bazata iya fadawa kowa ba, daga nan zuwa lokacin da zaa sami wata mafitar inafatan kin gane, sosae mardiy taji dadin magnar karkuzun, saboda tuna in zee tazo irin azabar da zAta gana mata kamin ta aikata lahira kowa ya huta. Miko mata wata kwalba yayi wanda aka yanka wata tsohuwar jaba aka tura da karfin tsiya kai kayi mamakin yanda har akayi jabar nan tashige cikin kwalbar nan yace amshi wannan ki je kisa a haka rami a daedae bakin kofar dakinta a yi ajiyar wannan kuma yasake mikomata ki tabbatar ranar da aka kawota ta ci kamin wahsegari.sosae mardiy tayi godia nan atake ta ajiye masa dubu dari biyu. Daria karkuzu yasheqe dai ita shiyasa yakeson aiki da mardiyy don bata bada kudin banza sam baya wasa da aikinta don yasan shima yanasamu. Basu isa gida ba sae kusan bayan ishai sosae sun gaji don sholy ma ko gidanta bata wuce va nan ta kwana, yayinda mijinta keta kira tana dauka tahaushi da maseefar ita ba gida zata kwana ba hakuri yabata tareda mata sallama yanason tambayarta ina taje amma tsoro bazae barshi ba. Washegari tun da farar safia sukaa nemo me aikin gini suka biyashi sosae ya fasa tiles din wajen dakin zee aka birne kwalbar, sholy tace to yanzu rabin aiki ya kammala kinsan dae yanda muakyi dake ki daure ki nuna komae ba komae bane har matsiyatan danginta su wuce sannan mufara buda babin cin uban yar shegia shewa sukayi suka tafa tareda ci gaba da kitsa tuggun su inda sholly taba mardiyya shawarar takira muq ta nuna masa tayi nadama yanda zata samu yasaki jikinsa sannan ta fanshi kudin ta datakai wajen karkuzu, haka kuwa sukayi mardiyya takirasa lokacin yana dakin ammi suna maganar yanda zasu tsara abincin daurin aure duk da general yace su barshi zaayi komae a can amma gunda suma suyi nasu iyawar ikon, dauka yayi cikeda faduwar gabar da tsoron maseefar mardiyya amma sae yasamu akasin haka inda yana dauka ta fashe da kuka cikeda iya kissa tana bashi hkr sosae yaji dadin haka yakuma aminta da tuban mardiyyar inda daga karshe tama sa zancen nata kayan fadar kishiyar dabe mata,  ba cikin jin dadi yace ta fadi ko nawane zae bata t siya tunda yanzu lokaci ya riga ya ya kure mardiyya ta karkace kai tace yabata dubu dari biyar, saeda ya jinjina a ransa amma yazaeyi bazae iya hanata ba haka yamata alkawarin transfer ita dae ammi tana jinsu inda san wannan makirci ne irin na mardiyyar amma taja bakinta ta tsuke. 
A bangaren amarya kuwa shagulgula kawae ake gudanarwa cikeda tsari irin na yan boko kuma masu kudi, inteesar tun ana saura kwana biyar dauren aure ta iso daga nijar haka ma wasu daga cikin kawayen zee din dayawa turawa ne sun mata kara wajen zuwa mata hardasu sir gaius da jamaa da dama, manyan masu kudi sun halarta hotel duk da ake ji da shi kuwa a fadin garin lagos sae da abbuh ya kama saboda manyan bakin da dayawa a hotel suka sauka, ranar thursday muq da danginsa wanda abbuh ya wakilta su zo don event din da su ummi suka shirya suka dira wanda suma bakin gwargwado muq yakama masu hotel hadda su nuwaera aka zo, sosae family get together din da ummi tahada ya kayatar anci ansha anyi karyar naira duk inda ka gilma kuwa masu video coverage ne ke daukan, bikin saedae muce sam barka don fadar tsaruwar wajen bikin ma asarar biro ne. Haseen ba karamar rwar gani yayi a bikin ba kasancewar abu nashi inji shi sosae komae ya tafi inda ranar daurin aure zaa wuce da amarya katsina saboda suma can sun shirya nasu bikin dadedae gwargwadon ikonsu. Tunda ake nuna bikin a nta live hankalin mardiyya ya masifar tashi lallae inuwar rakumi tayi nesa da kasa, don har tagama kallon bikin bata ga alamar talaka ba, sosae hankalinta ya tashi wani irin azababben kishi ke cinta, don indae bangaren kyau ne bata da kishi don tasan tafi zeenatu kyau nesa ba kusa ba amma kudi fa, masu sa aga kyanka ko bakada kyan. Sholy ce tadinga tausar mardiyya don taga kishi na neman ya sata ruguza masu shirin su.
Vayan daurin aure aka wuce da amarya tareda danginta da wasu daga cikin kwayenta zuwa katsina don abbuh jirgi guda aka bashi don jigilar kai amarya da mutane kt, bawani kuka tayi ba amaryar kasancewar boko tagama zauna mata kuma gani take kukan me zatayi ita da tadade ma rabonta da gida sosae ummi tamata nasiha tareda fada mata yanayin zamantakewar aure bata boye mata komae ba tacire kunya ta sanar da diyarta komae kunya ta kama zee hakan kuwa bakaramin taymakonta yayi ba don dayawa wasu abubuwan bata sansu ba tunda ko dacan ba shiga irin maganar takeyi ba kuma gata ba wasu kawaye ba, sae turawa.
Su ummu sunyi walima a cikin gidansu wanda aka kayatar sosae da sosae sanda sheik dr sani maihula suka gayyato yafadakar da mutane gameda zamantakewar aure. Anyi komae cikin tsari an watse inda aka ajiye zee a bangaren ammi itada mutanenta washegari kowa ya watse yarage daga intisar sae zee na don inti sae ranar _Tuesday zata tafi yayinda amarya da ango sae friday nan zata dan zauna.

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now