CHAPTER TWENTY THREE

3.1K 151 19
                                        

WACECE ITA?

NA UMMUZAYD



Koda yan katsina sukaji sakin da muqaddas yayi ma mardiyya bakaramin murna sukayi ba ,tareda Allah ya wadarae da hali irin na mardiyya,

munje katsina mun zagaya yanuwa da dangi, inda na sauka gidan lubabatu, labari kamar bazae Kare ba, Nan take fadamin cewar Shima baban Abdulshakur yagaji yacire kunya ya dauko diyarsa don ganin Fara lalaceawr datayi, baa Mata fada ko kadan sae tasaka kuka,fitsara iri iri,muna cikin hirar saega shi an dauko su daga school yarinyar ta yi fes ta canza kamar ba ita ba.

Satinmu daya muka Koma gida, inda na dinga bin site din companies din Dana ke ma aiki, cikin ikon Allah suka Kara retaining Dina a matsayin online worker dinsu,sosae nake maeda hankalina kan aikina dayake zamanin yakara canzawa yasaka dole naje nayi wani course a America kan fashion and art design,cikin ikon Allah 2month na Kare nadawo gida nacigaba da aikina ina gida Amma kudin danake samu ko wata maaikaciyar govt din albarka.

Bayan wata biyu Allah ya albarkace ni da samun ciki,Wanda sosae cikin ke wahalar dani kullum muqaddas kan yafita office shiyake min wanka nanny's Dina ke abinci da gyaran gidan gaba daya , iya wahala nasha, bani nasamu kaina ba saeda nakai three month.

Sis nafeesa tagama karatun ta na mbbs(medicine) inda zamuje Oxford don Grad dinsu, sosae na saka rae da tafiyar Amma fir my yaki Bari na tafi acewarsa lafia Bata isheni ba haka inaji ina gani na zauna a gida, da Abdallah aka tafi don juyin duniya yaron ya ki dawowa gida da ance zaa kawo shi ranar da zazzabi zae kwana, haka muqaddas ya tattara shi yabar ma su ummi, sae yazamana hutu kawae yake zuwa wajen mu.

Wata na Tara cif Allah ya saukeni lafiya nasamu karuwar Diya mace,inda na roki muqaddas alfarmar asaka Mata sunan lubabatu,dakyar ya yarda acewarsa sunan tsofaffine, (lols) Amma sanin muhummancin sunan a wajena yasa yasanya Mata inda muke cemata hibba, sosae luby taji dadi,tun ana suna sauran kwana biyu ta iso garin Abuja da kayan barka akwati biyu.

Anyi suna cikin koshin lafiya jamaa sunyi min Kara sosae, nafeesa ce tazo ta zauna wajena kasancewar tagama karatun ta Bata Fara house manship dinta ba tukuna.

Cikin ikon Allah take fada Mani haduwarsu da wani doctor don yanzu magna a tsakaninsu tayi nisa,hotonshi ta dauko phone dinta ta nuna min cikeda da farincikin ganin Wanda ke kan screen din nafeesa nace, what! Zayd, alhamdulilah, itako da mamaki take tambayata ko na sanshi nake Bata amsa da" sosae ma shine zaid din Dana Baki lbr ae, nafeesa dasauri tayi dialling number dinsa ringing biyu ta dauka, " Ashe man kasan sister na zeenat maman abdallah, shikanshi maganr ta matukar bashi mamaki,ikon Allah Kenan shikam dama nafeesa na Masa Kama da fuskar da ya sani, bayan sun Dan taba Hira tabani wayar muka gaysa a mutumce kamar ba abinda yataba hadamu dashi, komae na dunia Ashe kaddararre ne daga Allah,.
Tambayarta nayi inda tasanshi taban amsa "zuwa wani course dinsa yayi Oxford can muka hadu"har dare hirar zaid din muke tayi in Kara jaddada Mata cewar tayidace da Miji na nuna ma saa.

A national hospital dake Abuja nafeesa tasamu house manship dinta, Dan haka wani zubin ni nake zuwa daukota in call din safe takeyi,kasantuwar ita sam Bata iya driving ba,babu yanda banyi ba lokacin kan inyi aure takoya Amma taki, yauma kamar kullum naje daukota ina mota ina dialling number dinta, idanuna suka hangomin wata mace, tana tahowa wajen parking space din, fuskar ta kumbure suntum, kasantuwar Rabin fuskarta ya rube cancer ta cinyeshi, iya tausayi baiwar Allahr taban tausayi hakan yasa na Dan Kara kallonta tareda fadin"Alhamdulilahi lazi afaani min mabtalaka bihi,wafaddalani ala kaseerin min man kalaqa tabdeela"(adduar dayakamata mutum yayi Kenan idan ya ga wani mummunan ciwo insha Allah ubangiji bazae taba jarabtarka da wannan ciwo ba).

Kara matsowa tayi dab inda na Kara kureta da kallo sosae, ko mafarki ne bazan manta da wannan fuskar ba, mardiyya Yar gayu mardiyya me kyau , yau itace Allah ya jaraba da wannan ciwo, jikina har rawa yakeyi na fito daga mota nakira sunanta" "mardiyya!" aiko dasauri ta juya muka hada Ido inda cikin hanzari ta nufoni tareda durkushewa a gabana alamun neman yafiya, wani irin azababben warine ke fitowa daga jikin ta kasancewar warin cancer bashi da Dadi ko kadan, dakyar na iya dauke numfashi na, hannunta tasaka ta rike kafata kasancewar tumour din ya rinjaye barin fuskarta na hagu kota yi magana baa ganewa, dakyar na iya fahimtar abinda take fada min, ki yaafemin mardiyya kada na mutu da hakinki Dana baban suhail, kiyafemin, dasauri na Kara matsawa kasancewar warin na son yafi karfin tsayawata na Shaka, bakomae na yafe Miki kiji da lalurar dake damunki, kanwarta ce cikeda maseefa take fadin" Dallah malama kina Bata min lokaci, lokacin dakike zaluncinki kike cin dunaiyar ki da tsinke ae bakiyi tunanin akwae Rana irinta yau na zuwa ba don haka!", haka mardiyya ta tashi jikinta a matukar sanyayye ga wani mugun ruwa kamar na kurji Yana bin fuskarta Yana ta tsiyaya abin babu kyan gani.

Wunin ranar haka nayishi jikina a matukar sanyaye,Koda muqaddas yadawo aiki na bashi labari ko damunsa Naga abin beyi ba, dakyar ya iya cewa "Allah sauwaka, kadan tagani", haka dae na wuni ina jimami don ta matukar bani tausayi.

Bayan sati biyu, naje asibiti dauko nafeesa na hadu da kanwar mardiyya tana kuka awajen, dasauri na balle murfin motar na nufeta, dafa kafadarta nayi da sauri ta juyo takalleni, tabbas taganeni don haka na tambayeta" meya farune ina mardiyya" fashewa takara yi da wani gunjin kuka cikin shesheka take fadamin rasuwar mardiyyar a yau, sannan ta cigaba da fadin" maman Abdallah don Allah ki yafema mardiyya keda baban Abdallah ko Zata samu sassaucin wani azabar kabarin, don vanji mardiyya tana cikin masu rabo gobe....... Da sauri na katseta "bake Kika halicceta ba nana , tsakanin bawa da Ubangiji baa Masa shishigi, Allah ya jikanta, jaje nayi Mata sannan na karasa cikin asibitin, nafeesa nake fadawa bayan na daukota sosae ta jinjina abin don wani irin tsoron Allah ne ya shigemu, mutum baa bakin kowa yake ba, Allah ya sa mudace.

Bayan wasu shekaru....

Alhaji muqaddas ne zaune a tamfatsetsen parlournsa Yana karatun jarida yayinda Abdallah yashigo parlourn, yaro matashi me aji Dan kimanin shekara 28, ajiye jaridar yayi tareda amsa sallamar da Abdallah din yayi, cikeda nutuswa Dan matashin ya zauna akasa tareda sunkuyar da Kai kasa alamun wata maganar yakeson ya Fadi, Sosa Kai yasoma yi alamun Jin kunya, Wanda Alhaji muqaddas yace" da alamu akwae maganar dakake so ka fadi,go ahead, banason wannan kunbiya kunbiyar", hajiya zeenat ce tashigo dakin dattijuwa Yar kimanin shekara 48, Amma tsabar hutu yasa ko ka kalle ta bazaka iya kidanya Mata wadannan shekaru ba.

Gaysheta yayi ta amsa tareda fadin"me ake tattaunawa be babu mu, cikeda zolaya, Alhaji muqaddas yace kema kya tambaya, hakanan dae Abdallah cikeda jin kunya yake fadin" mammy daama..... Ehn.....aure nake so nayi, Kuma Salma Yar gidan auntyn katsina(lubabatu) nakeso..

Dasauri Alhaji muqaddas da hajiya zeenat suka hada Ido cikeda farinciki, Alhaji muqaddas" alhamdulilah am so glad to hear that man, nadade ina maka kwadayinta, saboda zumuncinmu ya dada kulluwa a tsakaninmu Amma yanzu tunda dakanka ka zabeta, saekuje ku daedaeta kanku inta amince zanma Alhaji ishaq magana...

Yarane yammata kimanin yan shekara 19 suka shigo parlourn Wanda da gudu suka tafi wajen danuwansu, suna farincikin ganinsa, alahji muqaddas ne yakallesu daya bayan daya aransa Yana tasbihi ga ubangiji na azurtashi da yara masu Tarbiyya da kyau, ayanzu yaran su shida zeenat shida, uku maza hudu Mata, hibba tayi aure shekara daya kenan sae sauran da yanzu suke gabar karatu, tashi sukayi suka fice da ga parlour cikeda da nuna tsananin shakuwa a tsakaninsu......

TAMMAT BIHAMDALLAH, ALLAH YA YAFEMANA KURA KURANMU INDA MUKAYI KUSKURE ALLAH YA YAFEMANA INDA MUKAYI DAEDAE YABAMU LADAN.......

SAIKUNJINI A LITTAFINA NAGABA ME SUNA

********A DALILIN WANI**********

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now