*WACECE ITA?*💦💦
page 4*
*na ummu zayd*👌🏽 Zayd ne zaune adaki shiru shikam yarasaa dalilin dayasa yaketa tunanin zeenatu kusan kullum da tunaninta yake Kwana yake tashy, wani dan guntun tsaki yaja tareda dajin haushin zuciyarsa gameda addabarsa tunanin wacce besaniba , zumbur kamar wanda aka tsikara haka yatashy yadauki key din motarsa yafito yana kiran salele megadi, wanda ya ansa yafito dasauri ya tsugunna tareda cewa ina kwana ranka yadade, dakyar ya amsa tareda danyin jim sannan yace"salele kasan daga wani waje maman bawan Allah takeda zama? Salele yayidan Jim sannan yace" wlh yallabae bansani ba tana zuwane amma Allah besa nataba tambaya ba.. ..zaid ne yayi saurin dakatar dashy tareda da fadin ok kana iyatafiya yayinda yashige motarsa cike da bakin cikin rashin sanin inda zenemo wannan baiwa Allah.
A haka rayuwa tacigaba da garama zeenatu Tun tana tsoron dawowar alhajin Nan hardae ta dena tunda gashy yau wata uku kenan besake dawowa ba haka tasaki ranta kuma ikon Allah bata sake zuwa gidansu zaid ba tunda yanzu Allah yarufa mata asiri tasamu wanke wanke awani restaurant kobanza tana samyn Na kashewa kuma dan abincun dayarage takan hada tacinye wani zubin harda dan guzurinta musammn ranarda ma da baasiye abinci ba, yauma kamar kullum zenatu tanacikin wanke wanke ogar gurin tayi kiranta, zeenatu kizo kihada sauran wanke wanken nan daakaci abinci!", toh! ta ansa tareda tashy domin bin umarnin megidarta, ta shigo tana hada kayan kenan Idonta yahadu dana lubabatu aekuwa batasan sanda taje dasauri tarungumetaba har jikinta na kyarma lubabatu bata ma lura da ita b taji anrungumeta gawani masifar karni daga jikin matar cikin masifa luby tahanakdeta tareda fadin wat d fuck!? are u out of ur senses kuwa? Ido jajir zeena ta dago takalli luby wanda se asannan luby ta kalli fuskar tabbas ZEENA ce, cikeda mamaki takefadin"dan Allah maman bawan Allah kiyimin afuwa wlh banganeke bace kinsan duniar ce daban tsoro, zeena tadanyi dan guntun murmushinta tace bakomae luby suka gaysa sannan kowatayi dan Jim Sannan lubyn takada Baki tace ina bawan Allah zeena tabata amsa da yana Nan lpy gashy can yana barci itada duk jikinta yayi sanyi dan ganin canzawa luby din, luby tasake cewa kekuwa zeenatu haka zumunci yake kosau daya vakizo gidana ba nashama baban ilham maganarki harnagaji...... Zeena takada baki zatayi magana taji muryar hajia zuwaera nafadin wannan wane irin iskancine kihado kayan kiwanke kintsaya tunanin naki na banza harda customer sunzo kina shirme gaskia kinkusa kaini bango!", zeena jiKi narawa batama tsaya sallama da lubyn ba ta kwashe kwanukan tabar wajen, lubabatu tabita da kallo cike da tausayi takira hajiya ashe yayar maman luby ce tace haba inna (sunan dasuke kiran hajiyar kenan) hakuri akeda jamaa kinga wlh Nina tsaidata sbd tare muka kwanta a asibiti da danta lokacin dana hayfi abdulshakur wlh inna matarnan tana cikin damuwa....... Hajiya tayi saurin katseta tareda fadin"dallah tafican sokuwa uwar jajibe jajibe kekam bansan irin halinki ba luba, kinga ina rabaki da Sharrin mutane! hka dae luby tayi shiru batasake maganaba dantasan innar tasu akwaea sababi.Haka luby dae tayi shiru tana sauraren inna, can tafaki idon inna taje wajen zeena datake fama da wanke plates tace sannu maman bawan Allah zeenat ce tadago fuskarta cike da murmushi tace Yauwa, luby tajnyo kujera tare da cewa zeena inata Kira naji kinxo gidana najiki shiru haka kuwa zumunci yake? Zeenatu taja dogon numfashi tace wlh bahaka bane maman Abdul aenaje Gidannaku aka ce kinyi tafiya, luby ta nisa tace haka kuwa akayi, ya bayan rabuwa da hidima, zee tace alhamdulilah kowa kam lapiyansa lau alhamdulilah, haka suka cigaba d hira yayinda zee take tafaman wankewanke itakuma lubabatu natayata hira, inna tazo wucewa tagansu sunata hira takama baki tace"oh ni diyar lawandi kekam luba kinji haushi watau maganar danamiki duk bata isheki ba kenan?"luby natamata signal tayi shiru taki tacigaba tareda dayimata dakuwa🖐🏼 watau nice ma kike mawa wanan kallo yaran zamani se a barsu nidae ina jiye miki tsoron jamaa ne atoh, haka dae inna tayita mita sannan tabarsu, bayan tawucene luby kefadin dan Allah kiyi hakuri zeena kinsan halin inna akwae mita, tace LA! bakomae wallahi, lubyn bata tafiba harsae yamma likis abban Abdul yazo daukarta takada baki tace zeee zomuje ku gaysa da babban abdul nasha bashy labarinki yau dae yaga zeeanatu dinnan, zee tace to shikenan aranta tana mamakin kirki irin na luby, tare suka jera har wajen restaurant din inna dae na kallon luby yayinda take mata kallon sauna, taja tsaki mtswww, wlh wannan diya da shanshanci kike mudae addua kawae zamubiki da ita Allah ya shiryeki luba, hakadae suka wuce sum sum suka bar inna nata sababi, suna fita suka samu yayi parking a kofar restaurant din suka gaysa luby tace abban Abdul yau dae ga zeenatu ashe tareda inna suke aiki, yakara fadada fararasa yace Allah sarki seyau Allah yayi zee tayi murmushi haka dae suka gaysa sannan tayi musu sallama abban abdul Yakawo dubu biyu yace gashy zeenat asiyawa abdul biscuit ta amsa tayi godia sannan ta koma yamma kuwa nayi tahada kayanta ta tafi kongonta. 💦💦WACECE ITA?💦. Na ummu zaid👌🏽 *page 5* yauma kamar kullum zeenatu tana zaune tana faman wanke wanke dayake wajen maaikata ne birjik wannan na girki wannan na wanke wanke in wanan yahada kwanuka yayi anjima wani zeyi to yanzu zee ce turn din wanke wanke yakamata tanacikin aiki hajia inna ta Kwala mata Kira ta amsa tarada tsame Hannu tatfi don amsa kiran uwar gidan tata, tsugunawa tayi har kasa tace gani hajiya, inna ta Dan saurara da sababin datake tace yauwa aese ki shirya me nafe(napep) ze zo yakai ki gdan waccan shasha sha, kobata fadi sunanba tasan watake nufi dan haka tace toh hajiya, tareda mikewa dan ta shirya ita da bawan Allah, cikin minti kadan ta kimtsa tareda zuwa ta shayda ma hajiar tagama, hajiar tace aeseki tafi yana waje yana jira amma base kindayawo yau ba sekuma gobe zee tayi godia ta mike tadau dan buhunsu tashiga napep wanda yakaisu layout layin masallacin lugga tanan gidan lubyn yake, tunda suka sauka take kallon gidan watau wani irin kara gyaran gidan daakayi iya tsaruwa ya tsaru sedaa ace Masha Allah haka tashiga Gidan tareda knucking din kofa luby tazo tabude da gudu tarungume zee tareda fadin ga zeenatu ga zeenatu lale marhaban lallae yau inada babbar bakuwa!"zee tajanye jiki tareda neman kujera tayi matsuguni, ta gayda lubyn sannan sukadan fara taba hira tace au sakko bawan Allah din mana kisha iska, nidan zumudi ma ko ruwa vankawo miki ba😊, tashy tayi takawo mata kayan motsa baki kan kace meye wanan ancika gabanta da kayan lashe lashe zee tarike baki tace" haba maman abdul duk nikadae luby tace gashy kuwa sekin cinyeshi zee tazaro ido 😳tareda fadin wanene ni? Haka dae suke tahira zee nacin abinci, takammala lokacin bawan Allah yatashy yana kuka tadaukeshy tana bashy nono, luba tace nikuwa zeenatu Tun randa na fara ganinki nalura kina tareda damuwa kuma harga Allah naji inada burin in taymakeki Kada kiji komae inaso kifadamin abinda ke damunki, nan danan jikin zee yayi sanyi Idonta yakada yayi jajir, luby takalle ta tareda dafa cinyarta tace "kiyi hkuri in abinda nafada yabatamiki rai mubar maganar amma Allah yasan tunranda nafara ganinki naji inasonki zeenatu kiyi hakuri", zee tabude baki tafara mgn muryarta na rawa tace maman abdul wlh bahaka bane nayarda dake dari bisa dari, kawae labarin rayuwata babu komae cikinsa face wasu kulle kulle da inna fadamiki bazaki taba yarda daniba kamar yanda zaid yakI yarda,..... Luby takatseta da cewa wlh maman bawan Allah fuskarki batayi Kama data makaryata ba sedae inhar baki da burin gayamani matsalarki..... Zee tace bahaka vane tareda fashewa da gunjin kuka musamman data tuna fyaden da aka mata watannin baya yanzu ciwon abin takeji kamar yanzu yafaru, seda tayi me isarta kana ta tsagyata da kukan tadubi luba tace idan nafada miki cewa ban san ni Wacece ba zaki iya yarda?Luby Takalleta akagauce tareda fadi banganeba? Zee ta nisa tace lubabatu wlh tallahi niban *san wacceni* ba kara tsinkewa dakuka tayi kana tacigaba, na wayi garine naganni a garin nan tareda cikin bawan Allah bansan gidanmu ba bansan iyayena ba bansan waye yayimin cikin bawan Allah ba da ubansa kokuwa beda uba Alahu a'alam, luba wannan shine labarina, bana iya tuna komae gameda rayuwata ta baya, jikin luba yayi matukar sanyi ita tunda take adunia bata taba jin irin wannan labari ba lallae kowane dan adam danashy kalubale, luby wacce ayanzu harshenta yayimata nauyi saboda tsabar kaduwa tace"zee to yanzu inakike dazama?" Zee tace"maman bawan Allah a uncompleted building muke dazama nida dana banida inda zanje"tasake fashewa da kuka, lubabatu natayata kukan dakyar tace "share hawanyenki zeenatu Insha Allah zanyi iya bakin kokarina wajen ganin nataymaka miki kinji? Zeenatu tagyada kai tace ngd Allah yakara arziki, ta Kada kai takalli agogon dakin, kinga har laasar tayi luba bari nayi sallah nawuce kada yamma tayi luba tace kije ina? Aedagayau kingama zaman kwango Kuma nasan halin baban abdul beda matsala koda voice quarters kizauna kan yazo zee takada kai tace gaskia kiyi hakuri amma luby baze yiwu nazauna gidannanba. 💦💦WACECE ITA?💦. *Page 6* na ummu zaid👌🏽 Zee takara shan mur tareda fadin wallahi bazan daura ma kowa nauyi ba nagode da taymakonki, ran luba yabaci tace maman bawan Allah haka ki ke da taurin kai ashe? Lallae nayarda baki yarda dani ba haka aminci yake ashe? Bakome Allah ya kiyaye hanya kitafi!, jikin zee yayi sanyi hakanan tanaji tana gani badan ranta nasoba tadawo tazauna, luby tasaki faraarta tareda fadin kokefa amma kintsaya kafiya Ina wannan abin, zee tace ayya bahaka bane kayanmu dasuke can ne wae..... Luby takatseta tareda fadin kya kwaso nakwasowa gobe mugani kodamasu dama, hakadae suketa fira har yamma zeenatu natayata girki suka kammala komae da komae suka ajiye a dinning table, wajen biyar suka ji karar motar baban abdul shakur luby tafita da sassarfa ta tarbi mijinta hannunta sakale danasa suka shigo, zeenatu kunya takamata tareda fadin sannu dazuwa, yadan kalleta kadan ya amsa da yawwa maman bawan Allah, yau kece Gidan namu sannu ta amsa da yawwa, kana suka shiga cikin daki, sebayan ishai baban abdul yadawo akasoma cin abinci, wanda ita zeenatun jinta take duk atakure takasa cin komae se cakula shi kawae take, bawan Allah ne yasa kuka wanda yabawa zeenatun damar tashy dan dakkoshy ashe fadowa yayi daga kujera har yafasa baki, dasauri tadauke shy tareda fadin sannu tana rirriga shy take amma shi yakiyin shiru baban abdul yayi magna"bashy nono mana ta amsa da toh tasamu waje tafara bashy wanda tafada duniar tunani idan yanzu yazasuyi in nan ma abban abdul din yaki yarda dazamansu? Abban abdul ne yakalli luby yace: yau kawar taki nan zasu kwana?ajiye spoon din hannunta tayi tace baby akwae maagnr dazamuyine nidakai gameda alamaryn baiwar Allah nan, dariya yayi yace ho matar aljanna hala ma yau ceton ne zaayi, itadae batace komae b shiko a ransa yana jinjina alamaryn matar tasa, tun ya na fada akan halayyarta ta jajibe jajibe harya hakura yazuba mata ido danshikam yasan lubynsa wajen tausayi ba baya ba, ahaka suka kammala luby ta tattare wajen, shidae abban abdul yayi kasake yanajiran matarsa yaji yau kuma da wacce akazo, fitowa tayi daga kitchen bayan tagama kintsa wajen takallesa tace abban abdul muje daga parlour muyi maganar, hkanan yatashy yabi bayan matarsa, suka zauna a kujera daya yayinda zeenatu ta rusunar dakanta tareda saukowa kasa, luby tace haba maman bawan allah kizauna mana, zee tace nan ma ya isa, luby ta Kada baki tareda fadin zeenatu ki kwantar da hankalinki ki nutsu kifada ma honey abinda kika fadamin, jikin zeenatu yayi sanyi dan ita ba abinda ta tsana irin bada labarinta da bakomae cikinsa face bakinciki , bata da zabin daya wuce ta kara rattaba musu labarinnata, shidae abban Abdul yayi kasake yana saurare hartakai aya, shikanshy ya tausaya ma rayuwarta, shiru yayi seda tagama kana yace"maman bawan Allah naji labarinki kuma ke diya macece be kamata rayuwarki takasance babu ginshiki ba tabbas hadari ne babba zamu taymakama miki zeena, niduba danayi da matsalarki gani nayi kamar loosing memory dinki kikayi zeenatu, Insha Allah zamuje asibiti adubaki ko Allah yasa ki gano yanuwanki, godia zee tashigayi har da hawaye baban abdul yace daina kuka maman bawan Allah duk wanda yataymaki wani Allah zaya taymaka masa, ke luby tashy kikaita dakin dazata dinga kwana, sannan yatashy yashige dakinsu, dukkansu sukayi shiru sannan luba tace zEena ba kuka yakamata Kiyi ba addua zaki dinga yi tareda kara gode ma Allah dan nasan yana sane dake, tashy muje narakaki dakin naki mikewa tayi tareda saba danta akafada, luby takaita VQ tareda cewa akawae bargo cikin wardrobe din koda kinji sanyi, ta amsa da toh tareda godia luby taja musu kofa, kara fadada faraa tayi ta kalli danta dake kwance tace"bawan Allah yau zamuyi barcin dabamu taba yiba nidakai, tofeshy da addua tayi sannan ta tashy ta dauro alwala tareda gabatar da salar nafila tanagodema Allah daya rufa masu asiri.
Washe gari da sassafe ta tashy tama danta wanka ta kara zura masa Kayan jikinsa najiya, itama tayi wanka, tanaso taje taya luby aiki amma tana ganin kamar abin yayi wuri hakanan tazauna tana lazimi tareda dazuba ma danta idanu dayake ta wasansa, sea wurin 8 taji anmata knucking tareda sallama luby ce tashiggo"maman bawan Allah ina kwana, ta amsa da lapiya lau ummyn abdul ya iyali ya akaji da hidima damu? Luby ta amsa da lpy lau amma wace irin hidima kinga bawannan ne yakawo ni ba dama cweety keson ganinki kan ya fita inkin gama kizo, zee tace ae ba abinda nakeyi inama taso nazo nataya ki aiki naga baban abdul na nan, luby tace bakomae seki zo muje kada musashy yin latti, tare suka mike yayinda zee tajanyo hijab dinta tadauki danta suka fice, taraddashy sukayi zaune kan kujera luby taje kusa dashy tazauna yayinda zee tasamu matsuguni can nesa dasu tazauna tareda fadin ina kwana alhaji, amsawa yayi da lapiya lau, ya kwanan abdul tace alhamdulilah h
Yace mikosa mana mugaysa tashy tayi tamika masa shy takoma tazauna yayi jim kadan tareda cewa, zeenatu nakira ki nasanar dake magnar zuwan ki asibiti yau dan aduba ki ko kinsamu lost of memory dinne kamar yanda nake tunani, danhaka ke luba anjima kina iya rakata kuje adubata zanbarmiki kudi duk yanda ake ciki inna dawo kwa sanar dani, godia tashiga yimasa ba kakkautawa tareda fadin nagode alhaji Allah yakara budi yajikan iyaye...... Katseta yayi tareda fadin bakomae ai yiwa kaine. Yatashy luby tabi bayan sa dan masa rakiya zuwa wajen motarsa, dawowa daga rakiyar tayi tace maman bawan Allah seki ci abinci kishirya mutafi saboda kada muyi latti, to ta amsa dashy yayinda luby tace abincin na kitchen kizuba bari naje nayi wanka ta amsa mata taje tadauko abincin tea ne tahada me kauri tazuba chips da kwae tareda plantain tadawo parlour taci, bayan tagamata kwashe kwanunkan wajen tayi wanke wanke tadawo parlor tanadan. Kallo tanajiran luby, lubyn ce tafito dawasu kaya ahannunta tace maman bawan Allah ga wannan kisaka ma sa kema ki canza kafin nadawo nadan tsinto muku wasu kayan, rasa bakin godia ma tayi dan zumudi tace kai wannan dawaeniya luby Allah barki da babn abdul yakareki da Sharin makiya luby ta amsa da ameen, mikewa tayi tanufi sashensu domin camza kaya bayan tafito tone ta Tatar da lubyn na kokarin rufe kofa tace yanzu dama zan biyo miki mutafi, kallon zee tayi tace kinga yanda kikayi kyau kuwa ikon Alah zee tayi murmushy tareda fadin ngd nikam ba abinda zanyi se godia, luby tace"uhm mutafi dan nasan halinki inkik soma godiar nan taki, amotar luby suka tafi kirar Pontiac maroon 2012 wanda suna tafe suna hirar alamaryn rayuwane,lubyn tace zee matsalar damuke tunanin kina daita tashafi kai ne danhaka psychiatry zamuje amma fa"zee tace nidae fatana nasamu lpy bakomae ae" cikin minti kadan suka isa psychiatric unit dake general hospital katsinan, tundaga Bakin gate suka soma ganin ana kawo patient wasu adaure wasu na maganganu barkatae zee dae se tasbihi takema Allah aranta tana kara godema ubangiji, tambaya sukai inda ake siyarda card aka nuna masu suka siya suka bi layi, zee tadubi luby tace"duk tunanina ya na ga hajiya inna zatay ta tunanin Meya hanani zuwa aiki" luby ta amshe ai dama kingama zuwa wannan aiki zeenatu rufamin asiri da inna idan tasan kindawo wajena akwae tsiya jikin zee yadanyi sanyi, hakadae sukai ta hira har layi yazo kansu suka shiga wajen doctor din, kujeru biyu ne agabn table dinsa hakan yabasu damar zama tareda gayshe sa, bedago daga rubutun dayake ba ya Amsa, can yadago kai tareda tambaya"who Is the patient among you?" Luby ta amsa masa da" she is the one" kasancewar likitan bayajin hausa duk da turanci ake maganar, lubyn ce take gayamasa complain dinsu yayinda zeenatu ta samu kanta dajin duk abinda Suke fadi da turancin tambayar kanta tashiga yi toni ya akai nasan wannan yaren? Sam hankalinta baya tareda su sejin doc din datayi ya kira ta da gurbatacciyar hausar sa, seenatu! Firgigit ta dago kai tareda kallonsa yes sir, cemata yayi"u re not with us wat are u thinking of?"nothing sire tabashy amsa itako luby tsayawa tai kallon zeenatu tana mamakin ashe ta iya turanci, kara tambayarta yayi da turancin, ya akai kikejin turanci seenatu, tunani tashiga yi a ashema English sunan yaren bashy amsa tayi da I cant say sire, likitan yakara nutsuwa tareda mata wasu tambayoyi datakasa bada amsar ko guda acikinsu, rubutu yacigaba dayi tareda dago kansa yakalli luby, madam i think ur sister has amnesia(lost of memory) but before we confirm the diganosis, yakamta tayi wani test daakecema EEG(electro encephalography) kan musan ya matsalar tata take,sannan musan abinyi,luby ce ta kada baki tareda fadin mungode doc yanzu ina zamuyi wannan test, basu ansa yayida"wani hanzari machine din damuke aiki dashy yasamu matsala kuma her case is a special case zamuyi referring dinku to psychiatric hospital dake kaduna ne, godia suka masu yamika musu referral form din sannan suka FIta......

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Espiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...