*💦💦WACECE ITA?💦*
Na ummu zayd
*Page 16*
Dan Allah hajia kitaymakeni da folder din abdulshakur ishaq please, ok sire amma meye hospital number dinsa? Dan Allah nidae kinemo min I nid it urgently please! Zaid ne yake fadi fuskar shi cikeda damuwa, zama yayi a reception din wajen record office din tareda dafe kai, dis gal is really playing with my intelligence how can she just leave without saying goodbye, fada yakeyi da karfi batareda laakari da mutanen dake wajen suna kallonsa ba, tsaki yaja tareda komawa record office din, madam how fa? Haryanzu baki duba bane? Hakuri tabashi tareda fadin" am sorry sir yanzu nake shirin miko maka folder din, karba yayi tareda fadin thank u madam, office dinsa yashige tareda duba address din gidan su luby daukar wayarsa yayi yadauki number din daaka bayar yayi saving sannan ya tashi yamaida folder din Abdul record office, fitowa yayi yashiga motarsa har layout zuwa gidan su luby, dayake gidan su ba wuyar ganewa ne dashy ba tuni yagane, kofar gidan yayi parking tareda fito dakafarsa guda daya waje yana sake saken meze cewa mutan gidan, fitowa yayi gaba daya daga cikin mortar yanufi bakin gate yana knocking, megadine ya leko tareda fadin barka da rana yallabai, amsawa yayi da barka kadae, Dan Allah danyimin sallama da zeenatu maman bawan Allah, baba megadine ya washe baki ae yallabai hajia zeenatu tayi tafia yau kwananta biyar kenan what! Zaid yafada tareda share zufar datake keto masa donshi duk zatonsa kotagane iyayenta, shidae baba megade shiru yayi yana kallon ikon Allah, zaid yace" Dan Allah Shiga ciki kace doctor zaid na magana, baba ya amsa da toh tareda shiga cikin gidan, Jim kadan yadawo tareda fadin ance kashigo, zaid yabi bayansa megadi yanuna masa dakin baki yashiga yazauna, can se ga luby hannunta rike dana abdulshakur dake koyon tafia, zama tayi tareda gayshesa Wanda dkayar zaid ya amsa, sannan yadan dauki abdul," lallae jiki yayi sauki Abdul, kallon luby yayi Dan Allah maman Abdul kitaymakeni da number zee, jinjina lamarin tayi sannan tace doc, zee har yau batada waya Dan munyi munyi ta amsa taki "INA take toh?" Yatamvayeta ,murmushi tayi Dan tasan meke tsakaninsu da zeenatun, zee tana Kaduna wajen amsan magani, shiru yayi sannan yakalli luby, maman Abdul please kitaymakeni kimin kwatancen inda take wlh kawarki tana vani wahala, aminci bece haka ba, Dan Allah akwae laipi don nace inasonta? Murmushi luby takuma yi tareda fadin" babu laifi doc kawae dae zeenatu Nada emotional problems ne kabita a hankali kajira har tasamu iyayenta am damn sure itama tana raayinka, kawae wanan tunani kehanata nuna maka soyayyya, shawara daya zanbaka kabita ahankali zaid don't force her zee ba yarinya bace kayi hakuri kaji? Godia yayimata sannan yace : maman Abdul Dan Allah kimin kwatancen inda zee take, I can't take it any longer sonta na azabtar dani please! Yafada tareda hade hannuwansa waje guda harda wani rufe ido, daria ma yabata sannan tamasa kwatancen, godia yashiga yimata sannan yamata sallama ya tafi................. **Assalamu alaikum, wai ana sallama da maman bawan Allah, inna ce tafito rike da hannun bawan Allah tace, ikon Allah lawandi, wanene, bata amsa yayi da Nima bansanshy ba inna, topa agarin nan waye yasan zeenatu dahar zeyi kiranta, jeka kace wanene kajiko, yaron ya amsa da toh sannan yafita, inna ce ta kwala ma zee kira, zeenatu, fito wae ana sallama, zee tafito daga parlourn inna tareda tsugunawa tace, inna anya nikuwa gani nai bana zuwa ko ina inna sannan kum...... To ai seki leka kiji wanene mutum baya haka, lawandi ne yashigo tareda fadin inna wae yace zaidu ne, kwalalo idanu zee tayi tareda fadin zaid kuma tomeya kawosa nan garin, inna takaleta tace: kinjini da gulmar taku ko? Ashe ma kinsanshi, zee tace inna likitan daya taba taimakon mune nida bawan Allah, inna tace: Allah sarki aiseki bude masa dakin kofar gida tunda daga nesa yake shedan ne kawae ke mance alhery Allahu Akbar vawan Allah kenan, itadae zee jikinta duk yayi sanyi saboda tasan zuwan zaid ba abinda ze kareta dashi sedae yadaura mata rigimarshy dayasaba, tashi tayi tashiga ciki ta dauko hijab dinta, tana fitowa bawan Allah yasaka rigima seya bita Kasancewar akwaeshy dason yawo sosae, haka nan ta rike masa hannu tafita..... Zaid ta tarar tsaye a soron gidan, tsayawa tayi Dan nesa dashy kadan tace: sannu dazuwa tareda umurtarshy shiga dakin zauren gidan, hey boy come here, shiko bawan Allah da Dan saurin sa yatafi yana Dan tafia Dan tafiar batayi kwari ba, daria zaid yayi tareda daukanshi ya cilla sama, Abdul yakake? Kissing dinsa yayi a kumatu tareda bin bayan zee wajen Dakin baki, zama yayi a kasan carpet din dakin tareda kallon zee" zee kin kyauta wae menayi miki kika tsaneni haka, u even have the gout to travel without even alerting me" zee takalllesa cikeda mamaki ita ba abinda yake bata haushy a alamarin zaid irin rudeness dinsa, kauda kai gefe daya tayi tace: wae zaid yakake so inyine da rayuwata, nafada maka kabari inyi settling problems dina and I promise to get back to u wit positive results, amma yanda kake maltreating dina shike sakani nakeji I can't give my love to u koda nan gaba please! " bude baki zaid yayi tareda kallon zee" shifa ba abinda yake bashy mamaki irin yanda take turanci kamar baturiya yanayin ascent dinta, shiduk tunaninshi she was not literate type, gyaran murya yayi tareda sassautawa daga masifar dayake tayi, am sorry wlh ba laifina bane yanda kike treating dina ne is very painful, tunda nake bantava jin soyayyyar kowace mace ba irin yanda nake sonki zee am sorry, ki amince da tayin soyayyya ta please before I go insane my dear, yafada tareda saka gwiwoyinsa biyu akasa, zee tace" katashy zaid bawae banasonka vane kawae inajin tsoron abinda ze iya faruwa gabane banaso yakansance kuma inada aure kuma yanzu ina soyayyya kayi hakuri please...... Katseta yayi" naji zee nidae insha Allah ma bakida miji, kallonsa tayi dasauri tace" yanzu zaid kafiso ace bada aure na hayfi bawan Allah ba akan ace da mijina? Shiru zaid yayi tareda girgiza kanshi " no zee please kada ki daukeni me son kaina dayawa wlh ba haka nake nufi ba am sorry, zanyi hakuri har zuwa randa kikaga yan uwanki amma idan har bakida miji, promise me that bazaki taba auren wani bayan ni ba?" Zee tace " namaka alkawari zaid adduarka da support dinka sunake bukata ayanzu, insha Allah inhar haka takasance zaka sameni me cika alkawarin dana dauka, Nima ina sonka zaid kawae akwae abubuwam danake over looking ne, ahaka dae ta lallaba zaid suka fara hira sannan tashiga gida takawo masa pure water da abinci, kin cin abincin yayi danshikam baya iyacin abincin talaka( hali zanen dutse), se bayan sallar asr yayimata sallama yatafi dan ranar zekoma KT, waya yadauko yabata wanda dakyar zee ta amsa tareda sayayyar kayan sawa masu kyau na bawan Allah, har bakin mota tamasa rakia sannan yaja yatafi tana daga masa hannu shima yana daga mata........... **** alhaji Ahmad ya nisa yace: umma ki kwantar da hankalinki Dan Allah, godia ga ubangiji yakamata kiyi dahar yasa kika iya tuna zeenatu kiyi hakuri umma, komae yakusa zuwa karshe insha Allah, kallonsa tayida runannen idonta daya zama ja tace: kullum cikin addua nake Abba Allah ya sa diyata tana hannu nagari, yanzu yakamata musanar da su haseen da nafeesa abinda ake ciki tunda suma duk cikinsu babu me maganarta, sannan shima muqaddas bazuba mashi ido zaayi ba watakila yanada masaniya a batan zee" alhaji Ahmad yanisa sannan yace" hakane gaskia ni tsavar tashin hankali besani nama tuna da wannan ba, amma kada musaka nafeesa cikin wannan maganar ita datake karatu sam bekamata ace ansata ba Abba haseen din dae, umma tace" to shikenan abba Allah yasa mudace", cigaba da kwantar mata da hankali yayi dan shima daurewa kawae yakeyi...... ********* hello inama magana da muqaddas ne? Daga dayan bangaren aka amsa" eh nine, Dan Allah wake magana? Ran alhaji Ahmad ne yabaci watau yaron nan ma yana nufin bashi da number ta azuciar sa yake ta magana, firgigit yadawo tunaninsa jin muqaddas din nata fading" hello, hello, gyaran murya alhaji Ahmad yayi sanan yace," kana magana da general Ahmad Muhammad al' ansar, gaban muqaddas ne ya buga, ranka yadade INA yini, amsawa alhaji Ahmad yayi tareda cewa" inbazaka damu ba muqaddas inaso naganka a gidana dake olusegun obasanjo I nid to talk to u, muqaddas ya amsa da insha Allah zanzo amma banan kusaba saboda bana kasar sire, alhaji Ahmad yace" no problem anytime just take ur time but make sure that u come OK? Amsawa yayi da OK tank u sire tareda kashe wayar yayi saving number din general....... Shiru yayi aransa yana mamakin hadinsa da general din sojoji, may be there is something tunda daddy na hurda da irin wadannan mutanen, gyara kwanciya yayi yacigaba da sake sake tareda rufe ido, mardiyya ta kima masa duka a cinya, dasauri yatashi yana me sosa wajen tareda zuba mata idanu aransa yanaso ya mata magana amma kwata kwata yakasa, hararsa tayi tace" muq wannan wane irin iskanci ne wai banacemaka kaje kayimin shopping bane tundazu zaka nemi waje kazauna watau ga yar iska kenan ban isa namaka magna ba oya tashimin, sum sum yatashi tareda dukar dakai kamar wata munafukar tsohuwa yadauki mukulinsa yafice..... Daria tayi tareda fara ma kanta kirari," seni diyar hajia zulai murucin kan dutse ban fito ba seda nashirya, namiji a tafin hannunmu yake se yanda muayi dashi karyar maza wlh, magana take ita kadae kamar wata ma haukacia, Dan tun bayan rasuwar suhail da sati biyu mardiyya tamanta komae tacigaba da cin duniayrta da tsinke, shedan kam yagama yimata fitsari a kunne............................ Haseen ba wani abu yasaka mukace kazo ba illa akan maganar yar uwarka zeena, haseen yadago yakalli iyayensa dasauri yace, Abba meyasami zee? Kullum inna tunata senayi kamar naje gidanta ko nakira sena manta, alhaji Ahmad ne yayi murmushi yace: alhamdulilah haseen kai nalura alamarynka dasauki bakamar nida ummanka ba, tiryan tiryan alhaji Ahmad ya zayyanowa haseen abinda Yafaru, haseen ne yafara share zufa ba kakkautawa , yana fadin Abba wae kuna nufin ba asan inda lil sis takeba, tabata? Abba ne ya gyada kai tareda fadin haseen hakuri duk zamuyi mu rungumi kaddara har Allah yasa musan Inda zee take haseen ne yafara kuka wiwi kamar karamin yaro, kallon Abba yayi kamar karamin yaro, daddy ina muqaddas yana nufin yacemin besan da batan zee ba? Abba yace" kwantar da hankalinka haseen munyi magna da muqaddas din shima ko ganeni beyi ba, kayi masa uzuri nalura shima kamar an mantar dashi alamaryn matarsa, haseen yagoge hawaye yace" wlh duk wanda kedasa hannu a bacewar sis senayi sanadin salwantar da rayuwarsa kowanene umma kiyi hakuri kidaena kuka Neman sis zamu fara kowane gidan radio dadukwani gidan tv na Nigeria duk wani social media zamu baza hotunanta........ 💦💦WACECE ITA?💦💦. *Page 17* Na ummu zaid👌🏽👌🏽 *kuyi hakuri da jina shiru dakukayi, kunsan shaanin me iyali se a slow, nagode kwarae da kulawarku Allah bar kauna* **Yanzu watan zee 5 a Kaduna ana magani amma shiru babu wani ci gaba,inna ce ke cewa" anya zeenatu bazako mu canza wani wajen me maganin ba tunda gashi yau wata biyar amma babu alamun nasara, zee tayi ajiyar zucia tace: inna nima lamarin nan kwata kwata yafara siremin dukda ance dae baa cire rai da rahamar Allah, bazan mance alherynku agareni ba ngd ngd , inna takatseta" zaki fara ko? Ae da na kowane, sedae kuma inhar yanzu baki daukeni uwaba, zee tace" ba haka bane inna, " au maza magrib tayi zeenatu kije waje kinemo bawan Allah Sam ban lura da fitarsa ba wlh, wannan megida akwae son yawo,zee ta tashi dasauri ta dauki hijab tafita nemn bawan Allah a waje,don tuni ta Dade da yayesa kasancewar akwaeshy da girma yaron yayi wayau kamar ba Dan shekara da rabi ba, ..................... Alhaji Ahmad ne zaune a office dinsa yau wata biyu kenan dasukayi magana da muqaddas akan yazo amma shiru kamar an shuka dusa, daukar wayarsa yayi tareda kara dialling sunan muqaddas din, seda tayi ringing har takusa tsinkewa sannan aka dauka, assalamu alaikum, ahaji yafada, daga daya bangaren aka amsa sannan alhaji yayi gyaran murya, muqaddas nayi matukar mamaki da har nakiraka nace inason ganinka amma shiru har yanzu bansami reply daga wajenka ba, fatan dae lpy, muqaddas ya amsa da lapia lau sire wlh abubuwane suka min yawa mundawo ma kasar ina abuja insha Allah cikin satin nan zanzo ayi hakuri, alhaji Ahmad yayi ajiyar zucia tareda fadin ina sauraronka Dan Allah kada kabari nakara nemanka, muqaddas ya amsa da insha Allah tareda ma alhajin sallama ya katse Kiran,,,, dogon nazari yayi na dalilin dayasa alhajin kenemansa danshi shaf yamanta dasunyi magana dashi akan yana nemansa kwanaki , tashi yayi kamar wani marayan muzuru yashiga dakin mardiyya wacce take fama da laulayin ciki, kullum tana kwance adaki kamar kayan wanki ita a dole game juna biyu, zama yayi Dan nesa da ita kadan tareda sunkuyar dakai dan ba karamin tsoronta yakeji ba, harara ta watsa masa tareda Jan dogon tsaki " mtswwwww lapia malm? Kazo kawani tsareni kamar wacce tayi maka laifi lpy? Kallonta yayi tareda sunkuyar dakai aransa yana tsoron fada mata tafiayar dayakeso yayi danyasan tabbas inhar yafada mata gaskia bazata barshi ba, tunda suka dawo wata biyu kenan beje katsina yagayda iyayensa ba, kakalo magana yayi kamar me koyon magana" dama a a a... Wajen aekinmu ne aka ce zamu tafi wani course na kwana uku a Lagos shine nace bari nafada miki, gaban mardiyya ne yafadi jin ambaton sunan Lagos din dayayi dan tasan nan ne gidan su zee yake, kallonsa tayi na wasu sakanni tareda fadin "zanbarka kaje amma ka tabbatar aikin da aka kai ka shi zekai ka, kanajina?" Girgiza kai yayi kamar wani jaririn kadangare, sannan yatashi zetafi aransa yana farinciki da barinsa datayi, kallonsa ta cigaba dayi aranta tana raya kyau da cikar zati irin na mijin nata,qut! ta hadiye yawu tareda kiransa" my dear?" Dasauri muqaddas yajuyo Dan yasan irin wannan kiran batayinsa se inta na neman wani abu a wajensa, tashi tayi tabiyo shi Inda yake tsaye kamar andasa shi, Dan mardiyya irin Matan nan ne jarababbu sosae, kafin ya dawo daga tunaninsa sejin yayi ta rungumeshi tareda hade bakunansu waje daya, shima he doesn't have any option than yabiyemata dan ayanda yake jin mardiyya ko wuta tace yashiga to tabbas ze iya Shiga.......... **** Muqaddas ne zaune a tamfatsetsen parlourn alhaji ahmad, tunda yashigo gidan abubuwa ke canza masa, yana ganin kamar bayau ne yafara zuwa gidan ba, tunani yashiga yi don tabbas gidan ba bakonsa bane, yana cikin tunani ne alhajin yafito daga bedroom dinsa, murmushi ya fadada ma fuskarsa tareda Neman guri yazauna a one seater din kujerar dakin nasa, gayshe muqaddas yayi,wayar land line din dake kan stool din tsakanin kujera da kujera yadauka tareda dialling hajia sakeena, umma kizo muqaddas din has arrived, muqaddass ne yasami Kansa da faduwar gaba, to shi meyafaru ne da har ake Kiran wata shi dabe waye da wannan bayin Allah ba, tunani yashiga yi batareda ya gano komae a lamaryn ba, wanda hakan ne yabama alhaji Ahmad damar kare masa kallo, duk yaron ya canza kamar bashi ba Dan gayu meji da kwalisa, ga wata rama da duhun dayayi, ahaka kowanne a cikinsu yake ta tunani batareda yacema danuwansa komae ba, hajia sakee CE tashigo parlourn tareda sallama" assalamu alaikum, amsawa sukayi atareda sannan hajia tanemi waje tazauna, itama aranta tana mamakin canzawar da mukaddas din yayi, daga kai yayi yakalli hajia sakeena Wanda hakan ya haddasar masa da faduwar gaba, gaysheta yayi tareda sunkuyar dakai Wanda kekara faduwar masa da gaba don besan meyayi ma wannnan bayin Allah ba suke nemansa, wayar hajia sakeena CE tafara kara alamar kira ne yashigo mata, dauka tayi tareda karawa a kunne tana fadin" kashigo yazo ina dakin Abba" sannan takatse wayar, haseen ne shima yashigo parlourn tareda gayda iyayensa yanemi waje yazauna a kusa da kafar umma, ko kallon muqaddas din beyi ba Dan gani yake shine silar bacewar lil sis dinsa, muqaddas ne yadago yakallesa Wanda yahaddasa masa karuwar faduwan gaba saboda haseen din abokin sa ne sosae ,amma meyakawoshy gidan nan? Tambayar kansa yayi danfa harga Allah shi be gane komae gameda wannan taro cikin family dinnan ba, alhaji ahmdad ne yayi gyaran murya tareda fadin: muqaddas nasan zakai mamaki kwarae akan musabbabin abinda yasa nayi kiranka, kuma observation din danayi tun shigowarka yasa nagane baka san dangantarka dake tsakaninmu dakai ba ko? Rudani muqaddas din yasake shiga dn shifa Sam maganar be gane Inda ta dosa ba, alhaji Ahmad ne yacigaba dacewa" munkiraka ne muji tabakinka gameda masaniyar bacewar diyarmu kuma matarka zeenatu" muqaddas yadago dasuri yace" sir wlh ni Sam bansanta ba banida wata matar da ta wuce mardiyya, watakila wani ne baniba.....haseen dake gefe a zuciye yadaka ma muqaddas tsawa" come on my friend! kada ka raina mana hankali, inma saida zee kayi wlh yau seka fadi gaskia dan...... Alhaji Ahmad ya daga hannu tareda dakatar da haseen" is ok haseen I didnt invite u here to create a drama, inbazaka min shiru ba then u go out!" Shiru haseen yayi tareda watsa ma muqaddas wani mugun kallo, wanda yasa muqaddas din kasa dakansa don baze iya fada da haseen agaban Wanda yake ganin iyayensa bane, amma ransa yayi matukar zafi akan abinda haseen yamasa, alhaji Ahmad ne ya nisa yace "kalleni dakyau muqaddas ni dakaina nabaka auren zeenatu diyata, shekara biyu da rabi kenan, abinda nakeso dakai shine, kafadamin INA zeenatu take, idon muqaddas ne yay ja cikeda Bacin rae, dan me wannan mutanen zasu tasashi agaba da tambayar inda diyarsu take shida Vesanta ba? Bude baki yayi yace" am sorry sire but I don't have any idea akan diyarka, asalima bansanta bantaba ganinta ba wlh" salati hajia sakeena tasaka tareda fashewa da kuka, " wannan wane irin masifa CE ke kunno kai a alamaryn yarinyata? Kuka tacigaba dayi Wanda ya haddasa ma haseen karin bacin rai, kallon muqaddas yayi yace " this is the last warning dazanmaka kafadamin inda kuka kai sis dina wlh I will forget about all the friendship na cimaka zarafi!.." alhaji Ahmad ne ya daka ma haseen.Tsawa "get out! Tunda kai ba'a fada maka mgna kaji kaji " am sorry Abba" haseen yafada, Abba yakara kaurara muryarsa" I said just go out, bana bukatar ka anan!" haseen ne yatashy ransa abace yafita har yana banging kofar parlourn, alhaji Ahmad yakalli muqaddas Wanda ya sunkuyar dakansa amma babu abinda yakeji kamar ana huramasa wuta cikin zuciarsa saboda tsabar bacin rai, gyaran murya alhaji yakuma yacigaba" kayi hakuri da halin abokinka inafatan shi baka manta dashi ba? Shiru muqaddas yayi ba tareda yabawa alhaji Ahmad amsa ba, cigaba alhaji yayi" nasan akwae wani kulalliya a bacewar zee Wanda am sure kaima kashiga rudani kamar yanda mukashiga, umma INA pictures din bikin zee dauko min, hajia sakeena ta amsa da toh, tareda tashy tashiga bedroom din Abba dan dauko masa hotunan, Jim kadan tadawo dauke da pictures din bikin zee Wanda adakin hajiar aka gansu cikin wardrobe dinta, mikama alhaji tayi tareda Neman waje tazauna, alhaji Ahmad yamika ma muqaddas pictures din tareda" ka nutsu sosae ka duba pictures dinnan dan nasan yanzu gani kake kamar shirme mukeyi ko?" kamar bazai amsa va saboda bacin rai, da yasan wannan shirmen maganar aka kira don afada masa da babu abinda zesa yataso tundaga abuja har lagos, amsa yayi dakyar tareda duba picture din farko Wanda yasa hanjin cikinsa kadawa, shine dauke da zee ranar dinner party dinsu Wanda suke kallon juna suna daria, besan sanda ya kara cigaba da kallon pics dinba wani Wanda sukaje honeymoon ne suka dauka wasu da family lokacin bikinsu, zufa ce tafara karyo ma muqaddas jikinsa yafara rawa, gashy dae tabbas shine da zee cikin photos din amma azahiri baya tuna komae gameda ita, kuka yafashe dashy kamar karamin yaro jikinsa Yakama rawa kamar Wanda yake da epilepsy(farfadia), alhaji Ahmad ne ya rikeshi dasauri tareda fara karantomasa adduoi Wanda convulsing din dayake yasa hankalin su hajia sakeena da alhaji Ahmad tsananin tashy dashiga rudani, dakyar da tayamakon Allah dakuma addua suka samu muqaddas yadaena convulsing , jigum jigum sukayi su biyun tareda kiran haseen ya tayamaka a kai muqaddas daki dan yazama unconscious.......... 💦💦WACECE ITA?💦💦 *PAGE 18* *na ummu zaid* zee da zaid kuwa tun tana kin biyemasa, har tazo tafara biyemasa soyayya suke me shiga zucia, kusan koyaushe suna makale da juna a waya, duk weekend kuma yana hanyan zuwa kaduna sedae inyana da calls ne kawae wani satin yake skipping baya zuwa, yauma zaid ne yazo Kaduna suna tareda zeenatu adakin baki na Zaure, hira sukeyi irinta masoya, yayinda bawan Allah keta kaikawo a tsakar dakin, zaid ne yakamoshi yana daria, "me kafan yawo abdallah kai baka zamane? Bawan Allah yayi daria dan shi bamae saurin iya mgna bane, kwanciya yayi luf a jikin zaid, zaid yakalli zeena, "dear wae bakya tausayamin ne please, kamarya ta bashi amsa" zaid yace" kodan tausayamin bakyayi kullum INA zarya a hanya dear, ga abdallah shima yana bukatar uba atareda shi kodan wannan kya tausayamin, pls zeena ki amince min muyi aure harna fara zama chronic bachelor ba mata, daria yaba zee tace" bawae banasonka vane zaid kowani Abu sonake nagano family a...... katseta yayi " yaushe? after 2 year, 5 years or ten years?" please zeenatu kimanta da wannan wlh na tabbatar iyayenki koda ace anganosu zasu fi farinciki suganki da aure, agida an matsamin, wannan soyayyar damukeyi batada amfani inhar bata zama ta aure ba, zee tace" kayi hkr dear zanyi shawara pls, "kullum haka kike cewa zaki shawara amma ba respond am tired!" itadae zee tayi shiru Dan inhar tabiyema zaid yanzu zasu bata, bata San wace kalma zatai amfani da eta ya fahimceta ba............ Inna ce takalli zee dake zaune agabanta tana yankema inna kumbar hannu tace, "zeenatu, zeenatu tadago tareda cewa naam inna, inna tacigaba" zeenatu yakamata iyanzu ace kin gama kunbiya kunbiyar kinshirya munje wajen me maganin nan bansan dalilinki nakin zuwa wajen me maganin nan ba, zee ta ajiye nail cutter din dake hannunta takalli inna" wlh inna ba haka bane kawae kudin da mutumin nan yace akawo ne nake ta tunani tsakani da Allah banso na takurawa baban abdulshakur, kokarin dakukeyi akan kuga nasamu sauki bansan da wani baki zan muku godia bane, inna takatseta " watau ke haryanzu baki mana kallon yan uwanki ko? Ai munyi mgna da ishaq din yacemin jibi ze turo kudin mota da kudin maganin a account din sani( babban Dan inna) zee tayi ajiyar zucia Dan aranta batasan wasu irin zuri'a ce haka masu kirki ba, dakyar ta kakalo murmushi tace" Allah sarki Allah yasaka da alhery banida bakin muku godia inna se addua, Allah yasa kugama da dunia lapiya, inna ta amsa da ameen, tace" ae kuma banga bata lokacin daxamuyi nidake ba karshen satin nan se mushirya mutafi, zee ta amsa da Allah kaimu sannan tacigaba da yanke ma inna kumba.... . ............... Muqaddas ne yafarka daga barcinsa cikeda wani irin azababben ciwon kai, don ko idon sa dakyar yake iya budewa, dafe kai da hannuwa biyu yayi tareda ambaton " ya Allah!" Bude ido yayi yasake kallon dakin dayake ciki, kwakwalwarsa ce daena aiki na wucin gadi, cigaba yayi da ambaton ya Allah!, Wanda ahankali ciwon kai din yasauka, kallon dakin yacigaba dayi I da alama besan ina yakeba don yasan nan ba dakin hotel din daya kama bane, firgigit yafara dawowa conscious mind dinsa tareda tatriyo abinda yafaru dazu, hasbunallahu wa niimal wakeel! yasake fadi tareda tashi tsaye kamar Wanda aka cokawa allura, bakin window din dakin yaje tareda yaye labulen dakin ganin gari yayi duhu ne yahaddasa masa faduwar gaba" omg! Meyakaini yin barci a gidan nan haka, zama yayi yacigaba da tunani nan yatuno da fuskar wacce yagani a pictures din dazu da ake ikirarin shi mijin tane, fashewa yayi da kuka kamar karamin yaro, Dan har yanzu yakasa tuna komae gameda ita balantana mutanen dasuke ikirarin surukansa ne, kuka yake me sauti Wanda yasa Abba da haseen shigowa dakin dasauri Wanda dawowarsu kenan daga sallar magrib, shigowa dakin sukayi a kagauce tareda dafa muqaddas din, Abba yace lafiya kake kuwa muqaddas? Kuka yacigaba dayi sannan yabude baki dakyar yakalli haseen yace" friend am so confused, believe me bansan WACECE ITA ba bana iya tuna komae gameda ita, please can you just wake me up from these nightmare?" Jikin haseen yayi sanyi kalau, don'tun dazu daya ga convulsing dinda muqaddas yayi yasan, he doesn't know anything akan whereabout din zee, shima daga ganin Alama he was under a spell, Haseen yadafashy yace" frnd kayi hakuri yanzu kaga, kahuta I will explain everything to u kashiga toilet kayi alwala kayi sallah dan bakayi asr da magrib ba inka ci abinci then we shall talk OK? Dakyar muqaddas yatashy yashiga toilet yadauro alwala haseen ya shimfida masa darduma sannan shi da Abba suka fita bayan sunga fitowarsa daga toilet din, tada ikamar sallah yayi wanda da ace haseen ya tsaya tareda muqaddas din daya lura da canji a tareda shi, domin dungura sallar yakeyi kawae dakyar yake iya karanto fatiha kawae a sallah, Wanda ada muqaddas mutum ne me matukar ibada, mahaddacin qur'ani amma yanzu bako daya,Dan rabon dayabi sallar jam'i ma yamanta, shi kanshy abin nadamunsa, and he don't know waze ma magna akan wannan issue dinba Sam, sallar shi ya idar yar dungure sannan yatashi yafita parlour, nan ya sami haseen yayi tagumi, kallonsa yayi frnd harka gama sallar? Gyada masa kai yayi sannan haseen yasake fadin" tashi muje muci abinci ankai parlourn daddy, binsa yayi abaya sukatafi, kowa yayi serving kansa se muqaddas yasami kansa dajin kunyar wadan da suke ikirarin surukansa ne, Abba yakallesa yace" inlaw kasaki jikinka kaci abinci mana, haka nan yayi tatura lomar abinci bakinsa yunwa yakeji amma Sam abincin yafitar masa akai, wayarshi ce tayi amsa kuwwa Wanda tun adazu yabarta a parlourn alhaji Ahmad, shaf yamanta da wayarsa, dasauri ya dauko wayar tareda dubawa don kan ya isa gareta ta tsinke, fuba miss call din wayar yayi 40 miss calls daga mardiyya se wasu missed call na mutane, gabansa ne ya yanke yafadi don yasan kashinsa yagama bushewa shikam ya Shiga ukunsa, zufa ce ta karyo masa, jikinsa yafara rawa don tsoro Wanda harya fada kan kujera batareda ya shirya ma hakanba, haseen ne yakaraso garesa tareda dafa sa donshi da Abba sun zata ko ciwon ne yakeso yatashi, " frnd lafiya dae ko?" Haseen yafada Wanda bemasan haseen din na magana ba, tsam yatashi yashige bedroom din dazu tareda dialling no din mardiyya, wacce seda takusa tsinkewa ta dauko bako sallama ta lailayo masa ashar, ubanme kakeyi dabaka dauki wayata ba muqaddas? Hakuri yafara bata tasake daka masa tsawa nace" ubanme kakeyi daka ki daga wayata ba hakurinka nake bukataba muq tambayar ka nayi, shiru yayi tareda fadin am sorry ba aladarsa bace karya amma seyasami Kansa da fadin" accident mukayi nida abokan aikina Amma dasauki ankaimu asibiti ne" ajiyar zucia tasaki don tunaninta kullin data masa yafara kwancewa ne, to shikenan katabatar kuma kadawo jibi din kajiko nafada maka don I nid u, kobata fada ba yagane abinda take nufi can kasan zuciarsa yafara" Allah yarabamu da jaraba, haseen yashigo dakin tareda fadin" frnd inka gama daddy nason ganinka" amsawa yayi da toh tareda tashi yabi bayan haseen din, alhaji Ahmad yakalli muqaddas din yace" muqaddas dama Kana da farfadiaya ne? Muqaddas yakalli Abba dasauri yace " farfadiya kuma? Tunda nake bantaba farfadiya ba Abba" alhaji Ahmad yayi gyaran murya tareda zayyanowa muqaddas labarin duk abinda suka sani gameda batan zee, shiru muqaddas yayi cikeda mamaki da alajabin abnda alhaji Ahmad yake fada, Alhajin ne yakarasa dacewa" muma abinda yafaru damu shiyafaru dakai sihirne ke tattareda kai dayasa ka kasa tuna komae fatanmu kacigaba da addua muma nan munayi Allah ya sawwaka, kai haseen kutashi kutafi ka kaishi Ku kwanta Allah ya sawaka , sallama sukai masa suka tashi suka tafi...... 💦💦WACECE ITA?💦💦 *PAGE 19* NA UMMU ZAID👌🏽 *kuyi hakuri masoya litrafin wacece ita kwana biyu I was carried away, sannan page din kacokan na sadaukar dashi zuwa gareku love u loads* zeena kiyi sauri kifito mana, ni narasa irin wannan sanyin jiki dakike yi gameda tafiar nan ,inna CE take fadi yayinda zee take daki tana saurin shirya kanta, tace" inna kiyi hakuri hijab zansaka two minute, inna tace" to baturia aeseki tayi tareda kara rike hannun Abdul,zee tayi daria Dan yanzu wasa suke da innar kamar kakarta Dan ta lura inna ta tsani turanci don hka take tsokansar inna wani sa'in, dauko hijab dinta tayi navy blue me hannu tsaka Wanda har kasa yake tadauko takalminta flat baki tareda Jakarta baka, tafito ta kullo kofar tareda fadin " inna muje ko?" Inna ta amsa da toh tareda Jan bawan Allah suka FItA, seda suka kusa titi inna tace yaron nan wahala ze sha zeenatu bari namika shi gidan harira kekuma ki karasa titin kitare mana me napep kinji ko?" Zee ta amsa da toh tareda cigaba da tafiya inna kuma tawuce kai bawan Allah gidan hareera wacce kawar inna dince, bakin titi takarasa tareda jiran abin hawa ta tareda tace" malam kasuwar barci zaka kaimu, mutumin yace toh sannan zee tace" don Allah kadan jira mamana yanzu Zata karaso, cewa yayi toh Allah yasa kada tadade, zee vata rufe baki bama ta hango inna tace" yauwa gata can karasowa ma don Allah mudan karasa kadauketa kasan tsohuwa,me adaedeta ya yi kwana suka dau inna daga nan yakaisu kasuwar barci inda ake shiga motar Zaria, suna zuwa suka samu saura mutum uku kawae don haka suka shiga baa dade ba motar tacika suka kama hanyar Zaria..... ................... kauyen giwa suka je sannan inna tasamu wani me rake a bakin wani rumfa tace "Dan Allah yaro INA tambayane gidan malam shuaibu me dara, mutumin yanuna musu gidan sukayi godia sannan suka shiga gidan tareda sallama, gidane ginin kasa me dakuna dakuna da yar rumfa sedae a malale yake da sumunti fes dashi da alama matan gidan Nada tsabta, wata yarinyace dake bakin rijiya tana wanke2 ta amsa, inna tace yarinya munzo wajen malam shuaibu ne yarinyar tace "ya kuwa je kasuwa amma kushiga daga daki se akira maku shi su maman basanan ma, inna ta amsa da toh sannan yarinyar tamasu jagora zuwa dakin, parloune karami dayaji Leda a tsakar dakin bangon dakin kuwa duk an saka kalandu anyi ado dasu abinka da kauye akwae san kalanda, ruwa yarinyar takawo musu a kwanan sha sannan tace bari na aika akirawo baban, inna tayi godia sannan tasha ruwan tareda mikama zeenatu, amsa tayi Tasha itama sannan tace" inna dama haka wurin keda nisa lallae agayda hareera ko INA tasamoshi oho" inna tace " toh ai in lalura tasamu koma inane komae Nisan waje haka nan ake zuwa fatan asamu lapia" cigaba sukai da hira sannan bayan mintuna sukaji sallamar malam shuaibu, shigowa dakin yayi tareda sallama, duk suka amsa sannan yazauna Dan nesa dasu yace" sannunku dazuwa, zeenatu tagayda malam shuaibun ya ansa fuska sake, sannan yayi shiru na wucin gadi, inna tace" malam mune wadan da dama mukayi waya zamu zo daga Kaduna, ga diyar TWA wacce namaka magana akan zamu zo tare, malm yace" ae naganeku sannunku" sannan yacema zeenatu ina ruwan rijiyar danace kizo dashi? Zee ta dauko jaka sannan Tamika ma malam ruwa a gorar robar faro, amsa yayi sannan yatashi yadauko Kofi yajuye ya kalli ruwan, yarinya gaskia kamar yanda nafada aikinki nada matukar wahala sosae, saboda mugayen aljanu aka hadaki dasu Wanda rabuwa dasu se ansha matukar wahala, kiyita addua kinjiko? Zee ta amsa da insha Allah" sannan yadauki ruwan yayi addua aciki yabama zeenatu ya umurceta data shanye, kafa kai tayi tashanye sannan yace zaa fara saukar alqurani Wanda zaayi sauka bakwai, sannan zaa dinga bada sadakar abinci tsawon adadin kwanakin saukar, kuma ke zeenatu, zanbaki maganin da kullum zaki dinga jikawa a gida kisha Dana wanna da hayaki har tsawon kwanaki bakwae din, se rubutun dazaa baki zaa rubuta alqurani ne kinga kenan randa aka cika sati zaki dawo ki amsa rubutun, daganan zaayi yanka, zeenatu takalli malam shuaibu" malam yankan yazama dolene? Saboda naga kamar anacewa haramun ne ko?" malam shuaibu yayi murmushi yace" harga Allah yankan nan dazamuyi saboda Allah zamuyishi kuma sadaka zamuyi da naman bawae wani Abu ba ki kwantar da hankalinki nima banayin irin wannan aikin dakuke tunani" zee ta amsa da toh( hattara masu zuwa amsan magani wajen malamai ba haramun bane Neman magani, amma mudinga lura da wadanda yakamata mudinga zuwa wajensu, sannan musan koda ance zaayi yanka saboda me zaayi sa saboda gudun fadawa halaka, Allah sa mudace) malam yacigaba, inkin dawo zaki kuma amsar wani maganin, agida kuma kidinga sadaka kinji ko? Godia inna tama malam shuaibu, sannan yatashi yakuma FItA yadauko maganin yama zeenatu bayani, abinda yasa kukaji nace abada wannan kudin saboda yara dazansa suyi saukar alquranine dakuma abincin sadaka safe rana dare na kwanakin ne dakuma ragon sadakar dazaayi, inna tace" bakomae ai mu fatanmu adace malam, sannan tasaka hannu tadauko kudin dubu sittin cif tabama malam, ya amsa sannan yacigaba damasu Karin bayani, sallama suka masa, yace" ae bazaku tafi Baku ci abinciba, umurtar wannan yarinyar yayi takawo masu abinci sukaci lokacin har azahar tayi sukayi sallah sannan suka kama hanyar Kaduna. Alhaji Ahmad yayi gyaran murya, " inlaw yanzu abinda nakeso dakai shine kabiya ta katsina kafada ma alhaji hisham yanda ake ciki kajiko? Sannan kadage da ibada adduar nan kada afasa Allah yasa katino da matarka, zanma kawu isah magana kaima as lan yanda zaayi naka aikin" muqaddas ya amsa da insha Allah, kansa a sunkuye, haseen ne yace" yanzu frnd kaiko bazaka bari se gobe ba katafi, kaga se mutafi tare, kayi abuja nikuma nayi port Harcourt, muqaddas ya girgiza kai "kada kadamu zan sake zuwa kuma Kasan nabar mardiyya ita kadae gashi batada lafiya, kallon kallo hajiya sakee da haseen suka soma, don kwata2 sunmanta dacewa zeenatu Nada kishiya, wata sarkakiyar kenan? Tashi muqaddas yayi tareda ma su alhaji Ahmad sallama yadauki yar jakarsa don tun randa yazo suka hanashi komawa hotel sedae da safe suka fita shida haseen suka dauko jakarsa, haseen ne yabishi abaya, yayinda su hajia suka biyosa har wajen mota Inda wani soja ke tsaye yanda jiransu, Sara ma alhaji Ahmad yayi tareda cewa" good morning sir!" Good morning kawae alhaji Ahmad yace yana me mika ma muqadds hannu sukayi musabaha, umnma kuwa se share hawaye takeyi dan yarta CE kemata yawo a kwakwalwa gidan baya dukkansu suka shiga sannan driver yaja suka fice, yayinda hajia sakeena tafashe da kuka, alhaji Ahmad yariko hannunta yana share mata hawaye da dayan hannun, why habibty? Please kiyi hakuri insha Allah akwae alamun nasara zamu ga daughter rungumota yayi suka shiga cikin gida daganan yashirya drivernsa yafita dashi office..... Haseen ya kalli muqaddas, frnd amma naga kamar booking KT kayi ai, muqaddas yabashi amsa" so nakeyi naje wajensu hajiya inyaso gobe se na wuce insha Allah, haseen yace Allen yasa, shiko muqadass yasan inhar yakoma abuja beje KT ba kuwa bazae taba zuwa ba don mardiyya hanashi zuwa takeyi, shikanshi yayi missing gidansu don rabonshi da gidan wata 11 kenan, Allah sarki mammy I will get back to u yafadi a zuciyarsa tareda lumshe ido yana Dada kewar iyayensa...

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Spiritualeta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...