CHAPTER ELEVEN

2.2K 90 5
                                        

💦WACECE ITA? 💦💦    
*PAGE 28*                                
*NA UMMU ZAID*


/TUNA BAYA/

Alhaji ahmad muhammad al'ansar,haifaffen garin katsina ne, yataso cikin gata sosae kasancewar da ne kwaya daya tilo ga hajia zeenatu da alhaji muhammad, dangin alhaji muhammad ba irin godon dabasuyi ba akan alhajin yakara aure kasancewar tunda hajia zeenatu tahayfi ahmad bata kuma koda bari ba, alhaji muhammad yashafama idonsa toka yaki yarda dan shi bega amfanin auren ba alhalin matarsa tana faranta ransa, tun alhaji ahmad na primary yake balain son sojoji ko a Hanya suke tafia da iyayensa inyaga sojoji yadinga ihun mama see soldiers"          Hajia sakeena cousin sister din muqaddas ce kanwar hajia zeenatu nafeesa, duk hutu sakeena na gidansu alhaji ahmad badan kowa ba sedan alhaji ahmad Allah yasaka ma junansu kaunar juna wanda asannu a hankali tarikide tazama soyayya tun lokacin da ahmad yafara girma ya lura da haka, bayan yagama secondary school ne alhaji muhammad yamasa cuku cukun samun Nigerian defence academy a kaduna, lokacin sakeena na primary 6, bayan wasu shekaru ahmad ya graduating a Nda da hons bsc physics, lokacin hajia sakeena nashirin zana waec, yayi proposing dinta batareda bata time ba ta amince don itama tana raayinsa, iyayensu suka shiga maganar aka saka rana sakeena nagama waec zaayi aure, lokacin akayi posting alhaji ahmad garin osun, Bayan aurensu cigaba da dama suka samu alahaji ahmad gameda aikinsa,yayinda yabar hajia sakee gida don tacigaba da karatunta,shekarar su daya da aure hajia sakeena ta haifi danta abubakar suna cemasa haseen saboda sunan babanta yaci, rayuwarsu suke cikeda kwanciar hankali, seda haseen yashiga shekara takwas lokacin yana primary 5 sannan hajia sakeena tasamu cikin zeenatu, sosae haseen keson kanwarsa kullum yana jikin umminsu saboda zeena, bayan wasu shekaru hajia sakeena tasamu cikin nafeesa, zeenatu yarinyace me baseera sosae  takasance me wayau sosae ga surutun tsiya, hajia sakeena ce zaune cikin yaranta lokacin nafeesa na rarrafe, rankwashin zeenatu tayi tareda fadin" baby watau bazakiji maganata bako? Kalli duk yanda kika bata books dinki da unnecessary drawings kuka tafara yi tareda fadin"mummy nabari, haseen dasauri ya rungume kanwarsa dake ta gunjin kuka shima kukan yafara hajia sakeena ranta yasake baci"don ubanku kushige jikin juna saboda kauna!, alhaji ahmad yashigo gidan yace haba habibty, me yarana suka maki zaki dinga cin zalinsu, ran hajia sakee yabaci, watau zalunsu ma nakeci ko? Fuu ta tashi ranta a matukar bace, itafa babu abinda yake kona mata rae da abban haseen irin mugun son yaransa kullum abinda ke hadasu fada kenan, alhaji ahmad ne yazo ya rarrashe matar sa wanda dakyar hajia sakeena ta sauko
*
Kwanaki sunata tafia yanzu haseen yana ss3 haduwarsu da muqaddas da abotarsu ta samo asali ne tun suna junior secondary school, sosae suka shaku haryanzu dasuke senior school abotarsu na nan yanda take sukanje ma juna hutu lokacin su hajia sakee suna abuja, hakanan Muqadas yataso yana raayin zeena, amma yabarma ransa harsae yadan kara girma itama tagirman dan yanzu take shirin zana common Entrance na primary, tun hajia sakeena nama zeenatu fada akan zane zane  hartagaji tazuba ma sarautar Allah idanu donta lura abin na zee ajininta yake,batada sana'a se zanen riguna da shoes iriri,  *Akwana a tashi ba wuya wajen Allah su zee ana shirin shiga Uni,yayinda girma yafito mata sosae ta zama yammata, farace tas doguwa siririya ce amma tanada body structure mekyau komae nata dan daedaene, idanunta farare ne tas tareda zara zaran eyelashes, irin idanun nan daake ma lakabi da lulu eyes, babu abinda ke kara ma fuskarta kyau irin idanunta da dan pink lips dinta karami, batareda nacika ku da surutu ba zeenatu dae kyakyawace irin matan nan da se kana ganinsu kullum kara kyau suke maka,  shakuwarsu da haseen soasae take yawa kwata kwata bayason abinda ze bata ma kanwarsa rae itadae nafeesa yar kallo ce don batada hayaniya sam koda yan gidansu da wuya kaji tana magana, lokacin sukuma haseen sungama makaranta inda yayi degree dinsa a fannin industrial chemistry a Nsuka abuja yayinda muqaddas yakaranci chemical engineering, batareda sunsha wahala ba duk suka sami aiki,Muqadas  yasamu aiki a abuja refinery,shikuma haseen yana aikida yan power holding company amma bangaren marketting.
Ummi sakeena takalli zeenatu ranta a bace bayan ta karanta takardar jamb dinta data cike, "yanzu zeenatu saboda bakida hankali duk kokarinki kirasa abinda kikazaba se art and designing?, meke damunki ne please,wlh bana son wannan ambition din naki tun kina karama haba baby!" zeenatu ta turo dan karamin bakinta gaba, tace please ummi kimin addua Allah yasa haka zefi alhery kisaka min albarka wlh ni shine burina a rayuwata, ummi takatse ta "dallah yimin shiru MuMu, ae insha Allah bazaki samu course dinnan ba,! alhaji ahmad dasae yanzu yasaka masu baki yace"haba ummi meyasa kike irin hakane please, ki mata addua Allah yasa haka yafi zama alhery nikam i wont force my children suyi karatun dabasa so please ki rabu da ita",  zo ummina kinji, zee ta matso kusa da abba dama tasan daga shi se yaya haseen kawae ke goyon bayanta banda ummi da nafeesa, ummina ki kwantar da hankalinki nayanke shawarar bama a kasarnan zakiyi karatun ba ina kika zaba ko ina ne insha Allah zan nema miki kinji ko, cikeda murna tace "da gaske abba?" gyada mata kai yayi, tace ok sire tareda saramasa(haka watarana takecemasa in tana cikin nishadi) sena yi bincike which university will be best for my area of study, kallon ummi tayi wace ranta inyayi dubu ya baci tace, "haba abba yanzu akan unitellectual course dinnan ne zaka barnata kudinka........?dakatar da'eta yayi yace "kidae samana albarka kawae ran hajia sakee abace ta tashi tabarmasu parloun, idon zeena yaciko da kwalla tace abba please talk to mummy dats my ambition i have been imagining it since when i started to grew up, my lifE just depend on it please talk her, kallon diyarsa yayi yace, ki kwantar da hankalinki baby ummi zata sauko i know one day she will be very proud of u.......
Ummi please i beg of you kibarni nayi course dinnan i promise u, u will be very proud of me, ummi sakeena tayi shiru batareda tace komae ba, ganin shirun da ummi tayi yasa zeena fashewa da kuka mummy tayi saurin jawo diyarta, "baby bawae nahanaki studying course dinnan bane kawae banga amfaninsa bane sannan duk kokarin da Allah yabaki kirasa mezakiyi se art and designing ure more than that kada kibari ki asarar iliminki , amma tunda kin nace Allah ya bada saa yasanya alhery da albarka cikin karatun naki mamana, zeena tarungume mamanta cikeda murnan jin amincewarta*                                       *Abba ne yadawo daga wajen aikin sa bayan an natsa ne zee tace abba maganar karatuna nayi deciding cewa stanford university zani  dake basing a california, ummi batace komae ba dan har ranta batasan course din da yarinyarta tazaba kawae ta yi shiru ne badan tana da yadda zatayi ba, abba ya fadada fararsa yace "ai nan california ma dan gidan kawunki isah yake da zama,nasan ze kulamin dake da sauki Allah yakaimu insha Allah i will start processing admission dinki from this week, yayanku ma yakirani akan wacce yakeso so in nagama settling issues dinsa i will get back to you, dadi kamar yakashe zeena,yayanta haseen zeyi aure zata samu aunty, dagudu ta tashi tashige daki don kiran haseen din su tsegunta, don yanda sukeyi kamar wani saanta, murmushi abba yayi yace akwae rigima inhar zee bazata samu attending bikin brother dinta haseen ba......    
💦💦Wacece ita?💦💦          *page 30*                                 *na ummu zaid👌🏽👌🏽*             *Inakike aunty umma shehu maje nagode sosae da ziyarar dakika kawomin Allah bar  kwana*                             Muqaddas ibrahim dane ga alhaji ibrahim da hajia hadiza sani tsafe, yataso cikin family masu rufin asiri sosae, alhaji ibrahim kwararren cardio thoracic surgeon ne, yasamu tarin ilimi da dama sannan yakasance abin alfahari ga alumma wanda yake amatsayin chief medical dirrector(cmd) a fmc katsina, muqaddas shine babban da a gidan kannensa tara mahayfiarsa hajia hadiza nada yara hudu muqaddas, se hisham, safeena da nuwaera,muqaddas dogo ne sosae fari sedaeba ba can ba kyakwawane meji da karfi murdaddene sosae kallo daya zaka masa yamaka kwarjini, in takaecemuku muqaddas kyakyawane sosae na nuna ma tsara, akwae kwalisa da gayu ba kadan ba,ya haddace qura'ani tun yana 22yrs duk gayunsa sosae yakeda raayin ilimin addini yanada kwakwalwa irin wadanda ake cewa gifted dinnan ne, lokacin da hajia hadiza ke da cikin safina alhaji ibrahim yakaro aure ya auri hajia sauda, sosae ummi kejin kishin mijinta babu abinda ke hadata da saudah don ko magana bata mata, yayinda muqaddas tun yana karamin sa jininsa yahadu dana saudat,kullum yana jikinta, ganin babu sarki sae Allah ne yasa ummi barin ma sauda muqaddas yaxama dan gidanta, yaran ammi hudu saleema, murjana da auta aisha, zaman lafia da kwanciar hankali ke gudana a gidan alhaji ibraheem duk yaran gidan nason hajia sauda saboda macece me saukin kai yayinda ummi batada wasa da yara sam duk gidan ita akafi jin tsoro..............
* alhamdulilah ummina ur admission is out and u have succesfully made it, they have enroll u, zeenatu tadaka tsalle tareda rungumar abbanta, alhamdulilah thanks abba bansan irin kalmar dazan maka godia ba, Allah kara budi da arziki, hajia sakeena dake yaken dole tace ameen tana taya diyarta murna amma a zuciarta badan tanaso ba, muqaddas da haseen ne suka shigo parlourn tareda sallama, wanda dagudu zeenatu ta rungume yayanta, bros wlh nasamu admission i was enrolled dadine yakashe haseen tareda bata hannu suka kashe, muqaddas yakalleta da sexy eyes dinsa, "sis ba gaysuwane? cikeda kunya zee tagayshesa sannan ta cigaba da bama bros labari, muqaddas ya kura ma zeenatu ido a ransa son zeenatu na fisgarsa jinshi yakeyi kamar ya hadiyeta don kauna, haseen ne ya lura da yanda yake kallon zee kur ko kyaftawa bayayi,taboshi yayi tareda fadin "frnd how fa? Cikeda kunya ya sosa kai tareda fadin nothing much,
*Da daddare Muqadas yace "my inlaw i need to talk to you, haseen ya wurgamasa pillow "wane irin iskancine yaushe nazama surukinka? Daure fuska yayi tareda gyaran murya, please am serious, ganin seriousness a fuskar muqaddas ne yasaka haseen natsuwa tareda fadin "am all ears, jim yayi sannan yafara fadin"frnd am in love, kuma badakowa sae zeena, zuciata na kaunarta i really want to marry her please kazamarmin jagora, murmushi ne ya subuce ma haseen ya kalli frnd dinshi, yanzu akan kanwarka kake ta karamar murya? common just proposed to her nidae i am hundred percent in support nasanka muqaddas bansan wani aibu a tareda kai fatana Allah yasa lil sis ta amince ma, cikeda murna muqaddas yace ameen ameen ahaka sukayita ta tattaunawa gameda yanda alamarin bikin haseen ze kasance don kwata kwata 3month aka saka bikin.
Washegari bayan anyi breakfast ne abba yatafi aiki lokacin yana matsayin general na sojoji, haseen yadaga waya yakira zee,hello sis please come over inason mgna dake, daga dyan bangaren zee tace gatanan zuwa, dirrect dakin haseen fa nufa, bros how fa? Dama brother dinki keson mgna dake, samun kujerar dake dakin yaya haseen tayi tareda fadin"gani ya muqaddas Allah yasa samune"daria sosae tabashi zeena akwae abin daria, haseen ne ya zame yabar masu dakin, matsowa kusa da eta sosae yayi wanda ya haddasa mata faduwar gaba, kur ya kuramata ido, hakan dayayi bakaramin kunya yabata ba duk jikinta yayi sanyi, dakyar ya tattaro maganar dake bakinsa yace "zeena i love u ,dasauri ta dago tasauke manyan idanuwanta akan fuskarshi sannan tasaukesu kasa tana kallon tyles din tsakar dakin, cigaba yayi, "yes i mean it inasonki zeena kicire matsayin yayan dakika daukeni kimaedashi yazama masoyinki burina na aureki baby please ki amince dani, iya tsoro zee taji tsoro dan yaune karan farko da namiji yataba furta mata kalmar so, itama tadade tana adduar Allah ya bata miji kamar bro muqaddas, don sosae yake burgeta, "please baby kice wani abu i wont force u in bkyasona ki fada mani i will leave u, kina sona?cikeda kunya zeena ta gyada kai tareda rufe fskarta da tafin hannunta, da murna muqaddas ya ke fadin "yes!  Insha Allah u wont regret it zee i promise u, cigaba yayi da fallasa mata asirin zuciarsa game da yanda yakeji da ita, itadae zee tayi shiru wani irin feelings takeji davata taba jin irinsa ba, dakyar yabarta ta tafi kasancewar yanaso yakoMa abuja yau dinnan, tashi tayi tafita tana murmushi a fuskarta jin tayi anjawo hannunta da karfi ihu take kokarin yi ya rufe mata baki tareda janta dakin, zeena takallesa haba yaya haseen wlh kaban tsoro sosae, kullo kofar yayi tareda "fadin ke abin tsoro baya maki kadan wallah, kin amince da abokina zee? "Daga masa kai tayi tana kara fadada murmushin fuskarta, haseen jinsayake yafi kowa Murna yamika mata hannu "give me five, kashewa sukayi kamar wasu yara sannan yace, wlh am so happy for u sisto nasan wanene muqaddas a ganina kinyi saan miji, zee ta amshe amma aunty hibba tafini saa data sameka bros, cigaba sukayi da hirarsu sannan haseen yabar dakin, zeetayi tsalle tafada gado cikeda murna, gani tayi kwanciar bazae mata ba yasata tashi don shiga wanka tanata raera wakar "soyayya dadi idan hardakai zaniyi,inbakai wazani kalla abayan rae🎼
💦💦WACECE ITA?💦💦  *page 31*                                *na ummu zaid👌🏽👌🏽*                                    Yaune ake bikin haseen wanda yarage saura sati daya tafiar zeena school, sosae suke shirin bikin yayanta itada Muqadas sune kirjin biki hakan kuwa ba karamin kara masu shaukin son juna sukai ba kullum suna tare waya kuwa tazamar masu kullum suna manne da juna.
.
.
yaune ake dinner party din haseen zeena iya kyau tayi kyau kamar itace amaryar, jira take muqaddas dinta yazo ya dauketa,"hello babyna kifito gani nan a kofar gate", ok ta cemasa sannan ta tako a hankali kamar me tausayin kasa, tunda tafito yake kallonta kamar ya lashe ta, shiga motar tayi tareda hura masa iska a ido, kallon fa?, ajiyar zucia yayi tareda fadin"anya baby zan iya bari kije wajen dinner dinnan gaskia am jealous,cant hide it, murmushi tayi dake kara ma face dinta kyau"yayana never worry kai kadaene a zuciata cigaba da kwantar masa da hankali tayi   sannan yaja motar suka tafi
* Kiran abokan ango akayi da kawayen amarya sufito sutaya amarya da ango murna, da takama da izza muqaddas yafito wanda ba karamin kyau yake kara masaba, rawa yafara yana kwaso shoki don dole yacashe yau bikin besty dinsa yanda yake ta rawa harda girgiza kamar dan daudu ba karamin bama mutane daria yayi ba, liki yake yi kamar bayason kudin harseda haseen yarike masa hannu "please friend ya isa haka, tunda yafito fili mardiyya takura masa ido yamugun tafia da imaninta, a ranta ta raya ita tasamu mijin datake nema, omg ga kyau ga kudi, lallae Allah ne yasa tanada rabo data biyo kawarta sholy bikinnan, da kamar kada taje, sholy ce ta taba mardiyya wacce ta saki wani ajiyar zucia, "yadae mardiy, nuna mata Muqadas tayi wanda yanzu yakamo hannun zeena suna rwa, "dat guy yamin sholy i was in love" sholy ta yi murmushi ai abune mesauki mardiy bari agama wannan bikin kibishi kimasa magana kinji inbe amince ba to tabbas zamusan yanda zamuyi dashi, cigaba sukayi da kallon duk wani moves nashi, taro yayi taro bikine akayi shi cikin tsary na manyan mutane don su AIT da NTA, suke nuna dinner party dinnan live, bayan angama bikin ne muqaddas yaja hannun zee suka fita dama ango da amarya daganan zasu suce gidansu dan an tsara cewa ba bu wanda ze masu rakiya.
Mardiyya ce tabiyo sa dasauri tareda fadin please jimana, juyowa yayi yace"are u talking to me? Gyada kai tayi tafara matsowa kusa dashi cikeda yanga tana karayraya, zee sarkin kishi tuni ranta yabaci tashige mota, kallonta yayi cikeda raeni, cigaba tayi"please inbazaka damu ba dan ban number wayanka inaso muyi wata magna, gaskia kamin" kallon ta yayi cikeda mamaki ashe akwae irin wadannan mata marasa aji haka? "please kimin uzuri bakowa ce kucaka nake bama number wayata ba and for ur information wannan dakike gani cikin mota matatatace ita zan aura bana bukatar kowace kazamar mace!  Sosae mardiyya ranta yabaci itada da samary suke binta kamar rakumi da akala ake ma wulakanci yau?the almighty mardiy lallae ta yarda alhakkin maza yafara kamata sabods mardiyya akwae yaudara kyakyawace ta nuna ma saa kusan zance tafi zeentun ma kyau shiyasa take abinda tagadama, samary aci kudinsu a wulakantasu shine burinta,romance kuwa tana yi amma koda wasa bata taba sex ba, bata gama tunani ba se jin motar muqaddas tayi tatashi tareda bade ta da kura, "kam bala'in nan ni wannan gayen ze wulakanta wlh seyagane cewa shayi ruwa ne, tayi kwafa tareda komawa cikin hall din dan yima sholy magana su tafi,
Tun a hanya zeenatu ke cika tana batsewa don sosae take kishin Muqadas barin ma ganin mardiyya dinnan me shegen kyau, dakkyar ya lallabeta tasauko sannan suka shiga gida.
.
.zeena a matsayina na mahyfiar ki kinsan daedae gwargwado duk irin arzikin da Allah yabamu baesa nayi watsi da tarbiyarku ba, shawara daya zanbaki kiji tsoron Allah bance kiji tsorona ba kituna wanda ya halicceki, ki kama mutuncinki kada kiga kina wata kasar kiyi watsi da tarbiar damuka baki,Allah yabada saa ayi ta karatu please ki abinda yakaiki kidawo kinji ko?  Zee wacce ke ta rusa kuka kamar Allah ya aiko ta ta ce insha Allah ummi kiyafemin kinji? Ummi sakeena tace" baki min komae ba nayafemiki Allah yamiki albarka yaba da saa, rungume mamnta tayi tacigaba da kuka don tun da take bata taba nisa da iyayenta ba,ummi kuwa daurewa kawae takeyi don zatayi missing yarta, don nafeesa basu cika hira da mummy ba miskilace ta nuna ma saa, nafeesa ta kalli sis dinta tareda matsowa kusa da ita ta rungume ta" sharemata hawaye takeyi da yatsanta, "shhh please yaya zee kidaena kuka, we will miss u", nafeesa nada dauriya sosae don dawuya kaga abinda yasata kuka, rakata sukayi har bakin motar dazata kaita airport dan hawa jirgi, haseen ne ya kunno motarshi kirar hyundai elentra,yana parking zee taje dagudu ta rungumeshy har ga Allah gani take kamar sun rabu kenan, "haba lil sis so kikeyi kisani kuka nima, ki kwantar da hankalinki ai akwae waya da social chats, zamudinga ganin juna"shiga gida yayi yagayda ummi yace ma hibba matarshi suje suyi rakiya, amsar makullin mota yayi daga hannun driver ya tura zee ciki,  wacce take ta kuka sannan suka shiga ,har airport din murtala muhammad suka rakata seda suka ji tashinsu sannan suka tafi cikeda kewa.
.
.
Bayan isowarsu motar school tazo ta dauki zeena, daki akabata sannan mutumin ya mata bayanin cewa gobe zasu zo daukanta saboda sabuwar zuwa ce, hostel dinsu yana
Silicon valley banisa da school din tafiar kafa ce ke kaisu su biyu ne jal a dakin, bayi tashiga tayi wanka sallah tayi sannan tafara tunanin abinci don yunwa takeji, tana cikin tunani aka kara mata knucking sannan aka miko mata abinci, white rice,stew and salad ne zama tayi taci ta koshi sannan ta dauko wayarta tafara kiran yan gidansu hira sukeyi sosae, se kusan magrib roomate dinta tashigo dakin gaysawa suakayi sanann sukayi introducing junansu, intisar sunan yarinyar amma ba yar nigeria bace yar nijar ce yarinyar vice president dinsu tana karantar law.washegari motar school dinsu taxo daukarsu haka dae intisar ta taymaka ma zee har department dinsu,yau da gobe har suka saba sosae.
.
.
Mardiyya ce gaban hatsabibin bokanta karkuzu, please karkuzu ka taymaka wlh wannan din da aure nakeson shi,karkuzu ya karkace kai ya sheke da daria "kwantar da hankali aure kamar anyi angama, kishafa wannan miko mata wani shuumin turare yayi tareda cigaba da fadin"kije office dinsa a take ze kamu da sonki sosae mardiyya, kara karkace kai tayi kamar tsohuwar zakara "maganar waccan fa daya cemin matarsa ce gaskia nikam banason zama da kishiya, karkuzu ya ce "ke ja'ira wanann dole zasuyi aure komae daren dadewa sedae kiyi hakuri ya auretan inyaso a san yanda zaayi da ita, murmushi ne ya kwacewa mardiyya tuna irin wulakancin da zata ma zee, godia sosae tamasa sannan tazage zif din jakarta taciro rapper din yan dubu dubu ta diremasa, tana barin wajen karkuzu dirrect NNPC tawuce bata sha wahala ba tagane office dinsa saboda akwae masu mata bincike akansa, secretary dinsa ce ta hanata shiga daka mata tsawa tayi, "ke dallah malama wallahi ko shi Muqadas din be isa yahanani shiga ba valle ke! Tureta tayi sannan tashiga office din akabar secretary tsaye galala kamar doluwa, daedaeta natsuwarta tayi tashiga da sallama lokacin yana waya da zeena, gavansa ne ya buga suna hada ido yaji wani tsananin sonta na fisgarshy jinsa yakeyi kamar sonta ne ke tafia da numfashinsa, ganin da mardiyya tayi yayi shiru yana jifanta da wani kallon soyyaya yasata shuumin murmushi, "hello my lover boy tafada cikeda duniyanci, binta yakeyi da kallo ko magana yakasa yi, zama tayi ta kallesa tunda bazaa bani izinin zama ba ni bara nazauna anan, murmushi yasakanmata sannan yace"na isa nama gimbiyata haka bismillah, sanann mardiyya tafara masa wasu maganganun dake kara jefa soyayyarrta cikin ransa, bata bar office dinsa ba harsaeda yamata alkawarin zae aureta kuma wata uku tabashi dasauri ya amince har yana rokonta tarage watannin don sun masa nisa, sallama tamasa sannan tabar office din tundaga nan muqaddas yarasa natsuwarsa, ko sallah yakeyi tunanin mardiyya yake zee kuwa yadaena kiranta kwata kwata se itace me kiransa kuma kullum intamasa korafi da irin excuse din dayake bata.....
.
.muqaddas ne zaune a gaban ammi yana mata bayanin yanaso atura gidansu budurwarsa, ammi ta washe baki"haka ake so ae haseen yaron kirki ne inafatan zeena din ma haka take amma bakacemin tana makaranta bane wae? Muqaddas ya sosa kai tareda fadin"ae ammi ba ita bace wacce zaa tura gidansu mardiyya ce,"ammi takada baki"zeenatun fa kuma muq? Shiru yayi sanann yacigaba ammi gaskia ni yanzu mardiyya nakeson aure kinga ita tana karatu kuma ina bukatar mata"ammi ta fara salati lallae yaran zamani watau ko kunyar fadin magana bakwaji,ina fatan hakan bazae kawo maku matsala da friend dinka bako? Murmushi yayi sannan ya ce ba matsala ammi, cigaba tayi amma banki taka ba muq vansan uzurin ka ba kuma amma zee bazataji dadin aurenka ba beside ma ure too young kafara yin mata biyu tun yanzu,Allah yasa alhery zanfada ma umminka sannan ama abba magana.
Tunda aka fada ma ummi maganar auren Muqadas take ta surfa fada"wannan ai zancen banza ne yasan bazae iya jiran yarinyar mutane ba ya furta mata kalmar so?  Ae ko kunyan haseen yajima wallahi"Alhaji ibrajim yayi saurin dakatar daeta"haba hadiza ku matsalar mata kenan yanzu Muqadas ko mata hudu yace zae aura a rana naga ba laefi bane tunda yanada abin rufin asirin dazae ciyar dasu, balle ma bakisan uzirinsa nayin auren ba dan Allah kiyi hakuri", ummi tayi shiru ranta a bace don sam gani take vaa kyauta a wannan alamary ba, batamasan dalilin dayasa bata san auren nan ba tun kan ma tasan wacece matar da muqaddas din zaya auro.
.
.
Haseen ne cikeda bacin rae yake ta zagaye a parlournsa matarsa hibba dake fama da laulayin ciki na ta bashi hakuri "please honey kayi hakuri kada ka fada ma zee maganar nan nasan zeena na son muqaddas bata iya boye soyayarsa kayi hakuri dan kyautawa bai yiba, kwantar da hankalinka" kallonta yayi "baby babu abinda yafi kona min rai irin ataba min kannena banason ganin bacin ransu especially zeena she owe me her happiness meyasa muqaddas ze yaudareta bayan irin amincin dake tsakaninmu? Yarda dashine yasani amincewa da soyayyarsu ashe he was a monster.. Hibba ta taso ta rungume mijinta tana kwantar masa da hankali wanda dakyar tasamu ta lallashe sa kan kada ya nuna ma muqaddas yama san da maganar aurensa tunda shima be neme sa va.....
Abin dunia yataru yama zee yawa, kwata kwata tarasa gane kan muqaddas dinta yadaena kula da ita sam yadaena kiranta ko a chat tamasa magana wani zubin baya amsawa, meke faruwa da soyayyata? Ta tambaye kanta don gaskia bazata iya hakurin jure rashin sa, ko karatun kirki bata iyawa saboda tinani dake ranta. Intisar takalleta "zee pleaese kiyi concentrating akan abinda ya kawoki ki cire zancen muqaddas dinnnan aranki he doesnt deserve it shiyasa fa bana soyayya gudun yaudarar maza kiyi hakuri, ajiyar zucia tayi tareda kallon intisar, "inti inason muqaddas i am trying my possible best naga na rage tunanin sa nakasa kitayani addua, kuma yaya haseen inna kira na tambayesa ko lafia muqaddas yake cemin yakeyi lpy lau am confused,dafata intisar tayi cikeda tausayin rommy dinta, come on addua yakamata kiyi jst be strong komae zae zo dasauki kinjiko, oya ga abincin ki cimin kidaena damuwa please.
.
.
Innalilahi wa'inna ilaihi rajiun zee tafada da karfi tareda saurin tashi daga kan gadonta, intisar da tashiga bathroom tana shirin watsa ruwa ne tafito dasauri tareda fadin lafia sis jin salatin da zee ta ke ta nanatawa, idanunta suka kada sukayi ja jawur haba no wonder ashe muqaddas yaudarenta yayi intisar tace sis lpynki wae?, mikamata wayan tayi tareda fadin sis kalli ashe Muqadas dina aure zaeyi,wae shine ya posting pre wedding pictures dinsa a facebook, fashewa tayi da kuka cikeda bakin ciki da nadamar amincemasa ya yaudareta, yayi wasa da hankalinta yaci amanar aminci da kauna, intisar da ranta yabaci tazauna kusa da zee "ehen zee she i told u maza duk mayaudarane munafukaine kinki yarda, kiyi hakuri kishare hawayenki kinjiko Allah zae saka miki kada ki kara zubar da hawayenki dan bae cancanci haka ba, hakuri tacigaba da bama zeenatu wanda dakyar tasamu tayi shiru tsanar maza na kwaranyowa da ga zuciarta, insha Allah narabu da muqaddas intisar, kiran wayar Brother haseen tayi yana dauka tafashe masa da kuka, kobe tambayeta ba yasan kukan metakeyi itama tagani, yaya haseen ya muqaddas ya yaudareni ,he betrays me, hakuri yayi tabata yana lallashinta wanda yasamu dakyar tayi shiru sukayi sallama, ranar barci sae barawone ya dauke zee.
..💦

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now