CHAPTER TWENTY

1.5K 113 6
                                        

  WACECE ITA?

NA UMMU ZAYD

Masha Allah Bari mudan taba alkalamin hope wannan chapter zae zama d best among the rest.show your love by voting and commenting.

Haseen ne yake fadawa ummi" ummi Niko zee nada cikine?" "Ciki kuma? Gaskia banda labari dama ina jiran ka kashigo,shekaran jiya abokin babanku Nan Alhaji sani yakira babanku akan maganar ita zee din,zayyane masa duk abinda baba sani yafada masu tayi sannan tacigaba" wlh ni bansan meke faruwa ba Kona kira ta akan naji ko da wani abin Bata iya fadamin"haseen yace" ummi kinji kinji yanda mukayi, ummi ce ta nisa "wlh gaskia munyi sakaci vama sa Ido akan alamarin yarinyar Nan saboda kowa yasan wannan kishiya ta zeenatu va mutuniyar arziki bace,shikenan tunda takasa fada maka kamata yayi mu samu lokaci ko nidakae ne muje mugani wani hali take ciki yakamta ma hayhuwar fari tazo gida wanka, zamuyi mgana da abbanku tukuna yanda ake ciki zakaji"haseen yace" shikenan ummi ni in sonane ma mutafi jibi asabar sae mudawo lahadi hankali na Sam yakasa kwanciya, nakira shi muqaddas dinma bawata takamaimar magana da ya ban amsa da ita" sallama sukayi sannan ya tafi.

Hayaniya ce kawae ke tashi a dakin masu Hira nayi masu cin abinci nayi ko wa kagani ta ci uwar kwalliya kamar zaa je zaben sarauniyar kyau,kallo daya zaka ma yan dakin kasan cewa suna facaka da naira kuma gayu ya zauna,saedae Kash kallo daya zaka masu kasan cewa mugayen yan bariki ne.

gefe mardiyya ce zaune tareda wasu kawayenta,hira kawae dakin akeyi na duniyan ci da batsa, sholly ta tabo mardiyya "mardiy lafiya dae ko? duk kinyi wani iri, saekace bake ba iyayen son biki, mardiyya ce ta saki ajiyar zucia" hmmmmm vazaki gane ba sholly,wae kinsan wannan Yar iskar yarinyar Ashe cikin nan Yana Nan be zube ba?  Bantaba tunanin haka ba sae yau Dana ganta da cikin kusan wata 8" sholly ta lailayo wata irin ashar dayasa yan dakin suka waewayo dubinta.

wata daga cikin matan me suna charas tace"kefa sholly matsalar ki kenan zagi yanzu muna cikin nishadin karuwar damuka samu kina wannan ashar haka meyayi zafi!"
Sholly tace ae dakunsan lusarancin da mardiy tayi ku kanku sae kunji kamar ku rufeta da duka Sam kwakwalwar ta Bata ja....mardiyya ta katseta "a'a fa sholly basaekin ci min mutumci ba fa, ko kula ta shollyn batayi ba ta zayyanewa yan dakin abinda ke faruwa, salati suka saka baki daya kamar wani mummunan abin ne yafaru,.

mejego datake hakimce kan gado ta taso daga kishingiden datake "wlh mardiyya kin ban haushi yanzu wa gariya waya?duk cikinmu ke ce kadae ke da kishiya tunda aka aurota muka baki shawarar a sheka shegiya lahira Kika ki yarda wae ke me burbushin imani,yanzu wa gari ya waya kina ganin zata Fara Tara zuria a cikin gidanki ke kina Nan da da daya wayasani ma ko yan biyu ne, wani irin huci ta fitar da bakin ta kamar bakin kumarci tareda tuge dankwalin kanta "Gosh! Dan Allah kudena kara hada min zafi mafita nake nema yanzu ko kasheta akace nayi a yanda nake ji wlh zan iya kasheta, ina mafita?

Dayadaga cikin kawar su me suna zakiyya tace wlh kigode min nayi wani arnen teacher aekinsa Sha yanzu magani yanzu, da sauri mardiyya tace please ki hada ni dashi Mana,  zakiyya ta barke da wata dariya,mekike ci na baka nazuba ae kwantar da hankalinki saedae shifa baya amsan kudi a matsayin ladan aiki.... mardiyya ta kuma katseta zakiyya ni yanzu indae bukata ta zata biya Koma menene zan Bashi, number din teacher zakiyya ta latsa Wanda ringing biyu yadauka.

hello zakiyya manyan dunia,batareda Bata wani lokaci ba ta shiga Koro masa jawabi, be katseta ba harta gama, dayake wayar a handsfree take,ok yanzu me kuke so ayi mata?haukatata ko a batar da ita a duniya? Mardiyya ta amshe"wlh malam zanfison a batar da ita kada wani ya Kara jin labarin ta kada mijnmu yakara tunawa da ITA harta danginta banson kowa ya Kara taso min da maganr ta balle a tada min hankali,dariya ya saki sannan "kada ki damu mardiyya sae dae aikin be yiwuwa yau saaedae zuwa gobe saboda akwae wani  aiki daya taso mani, Amma kamin Nan gobe yakamaata kishigo kibiya ladan aikin ki, dasauri mardiyya ta amsa da toh ngd teacher,zan amsa number Dinka saeka jini.

Bayan ya katse wayar ne mardiyya tasaki ajiyar zucia,"wlh sae yanzu zuciata tamin sanyi sanyi ngd zakiyya nawa zaa Bashi?zakiyya ta barke da dariya saboda dazu kanki Yana tukunya bakiji me nace vane? Baya amsan kudi a matsayin ladansa, mardiyya ta amshe ok me zaa Bashi don ITA har ga Allah Bata kawo komae ba, zakiyya tace saduwa kuma ta baya(wa iya zubillah) mardiyya  tayi shiru hankalinta ya tashi ita duk barinkinta Bata zina balle Kuma luwadi, "vazan iya ba zakiyya gunda nakoma wajen tsohon malamina yayimin nashi bajintar,"wata a dakin ta katseta "yo meye a ciki abinda sau dayane kawae zakiyi bukatar ki Kuma ta biya, ke haryau Baki waye ba komae akace sae kice a'a"a haka suka dinga mata huduba dae har ta amunce akan washegari zata je wajen teacher.

Bayan nagama sallar asuba, nayi azkar Dina nadan Koma barci kasancewar sae 6 nake tashi nasoma ayyukan gidan, cikin barci na ne nasoma Jin wani irin kauri na tashi kamr mafarki bandamu ba na gyara kwanciya na cigaba da barcina,hayakin ne ke Kara turnike dakin sosae Wanda har ya sani Fara tari sosae, a firgice na tashi tare da soma ambaton Allah SWA, bude idona gabana ya buga fast,kasancewar mugun ganin danayi na wuta tanacin wardrobe din dakina, da sauri na mike nafara neman hanyar fita daga dakin dama jikina akwae hijab Dina danayi salla bancire ba, bude kofar nayi don neman agajin mutan gidan Amma ga mamakina wutar Nan ni take hararowa sosae na fice daga dakin, duk dahaka wutar Nan na bina ganin tana niyyar cimin ne yasanyani na Fara gudu ko lura da cikin jikina ban ba, ficewa daga gidan nayi nacigaba da gudu dasauri kasancewar safiya ne sosae baaka ganin gilmawar kowa abinka da unguwa me shiru tafiya nacigaba dayi sosae har na bar unguwar ko takalmi babu a kafata.

Bandaena ganin wutar Nan na bina ba har sae da nayi kusan tafiyar 3 km, wajen wani Dan shago na ga benchi na zauna a galabaice ina hutawa,ga mamakina wutar Nan nakuma gani tana kusanto gareni dasauri na tashi na cigaba da sassarfa kwata kwata ji nake bana iya Kara minti 3 a garin Abuja yamin zafi kwarae dagaske, ahaka na karkata akalar tafiyata zuwa ga central motor pack, motoci ne suke ta Lodi inda na ga ana fadin katsina mutum biyu dasauri na fada cikin mota, akacigaba da Lodi haki kawae nakeyi numfashi na na fita sama sama wacce muke tare a baya takalleni sannu kinji baiwar Allah ya raba lpy,ameen na Bata amsa tareda kosawa mota tacika mutashi,saeda aka Fara amsar kudin mota sannan idona ya raena fata Don nida na fito ko takalma babu kafata ina Naga kudin mota,kallon dan Union din nayi "Dan Allah malam ka taymaka Mani wlh ko sisi banisdashi ......kan in sake bayani cikeda maseefa Dan union ya amshe(ae hajia Nan ba gidan taymako bane in bazaki iya biyan 3500 dallah malama sauka musaka wani kinbata Mana lokaci,a cikin motar wani mutumi da tunda nashigo yake kallona yayi mgna, malama kada ki damu Kai malam ga kudin na biya mata,godia nayita yima mutunin kamr zan Ari Baki don yanda nakejin wani zafi na taso min inhar ban bar garinnan ba watakila mutuwa zanyi, ko minti talatin bamu Kara ba motar mu ta tashi saeda Naga munfara barin gari hankali na ya kwanta, yanda muka bar Abuja haka takasance van Kuma tuna wani alamarin daya jibance ni ba,komae na manta van iya tuna kowa iyayena mijina da yanuwana.

ABUJA
Jirgi su ummee su ka hau dirrect daga Lagos zuwa Abuja ita da bro haseen, gidan Alhaji sani abokin abokin Abbun mu suka soma zuwa saeda sukayi sallah tukun sannan yaron Alhaji sanin mujahid yakaisu gidana kasancewar yasan gidan,don ina amarya yakai mamanshi.

Knocking sukayi a kofar dazata sadasu zuwa main parlor din gidan, mardiyya ce ta bude masu, duk iya rashin mutumcinta sae da taji gabanta ya buga dasuka hada ido da ummin,(inji bahaushe yace ko mutuwa na kunyar da da uwa), tamvayarta sukayi bayan sun gaysa ina zeenatun, don tunda suka iso sukaita Kiran wayarta basa samu don sun fada mata zuwan su yau din,kut mardiyya ta hadiye wani Abu me nauyi a kirjinta,itada teacher yace bawanda zae Kara neman zeenat Amma gashi ko kwana baayi ba yanuwanta sunzo nemanta, cikeda duniyan ci ta kallesu, Amma dae kunyi kuren gidane ko saboda Nan babu zeenatu, Kamar alamara sae taga duk sunyi shiru sun diririce, ummi tafara fadin kiyi hkr baiwar Allah, munyi kurene,Kai haseen inaga mukoma mu neme gidan ko, toh kawae yace yayinda wani labule me nauyi ya rufe idonsu zuciarsu daga tuanin zeena, hakanan suka koma gidan Alahji sani Wanda ba Wanda yasake maganar zeena din asalima mamakin dalilin zuwan su Abuja din sukayi tayi a haka washegari suka koma gida Wanda ko Abbu shikansa bae Kara maganar ba,tarihin diyarsu ya goge a memory dinsu Baki daya.

WACECE ITA?? Where stories live. Discover now