💦💦WACECE ITA? 💦💦
*page 32* *na ummu zaid*👌🏽👌🏽
Miss Zeena ure among the best student in these in dis faculty, how comes ure not concentrating anymore? Malamin dake daukar su zee wani course na management of fashion and creativity ne yakira zeena don duk test din dazasuyi no matter what zee setaci duka iya kauron mark seya so yi amma babu yanda zae yi yarinyar is genius, kallonsa tayi tareda fadin am sorry sire, cigaba yayi tunda kika zo school dinnan baki taba cin mark a test dina kasa da wannan ba 5/10 miss zeena, shiru tayi yayinda sire gaius ketamata nasiha,sallamarta yayi ta tafi aranshi yana kudurta"there is something disturbing dis gal this is unlike her,
*Please roommy for how many times zance kirabu da wannan mutumin, shi yana can yayi aure da matarsa ke kina nan kina grieving saboda shi please kiyi hakuri, kalli fa har sir gaius seda yamaki mgna, wlh baki ma su ummi adalci ba for there own sake please concentrate on ur studies mana zee! Zee tayi shiru tasan gaskia intisar kefada mata amma yata iya da ranta, zuciarta taki barin tunanin nan sam,"insha Allah zan yi kokari namaida hankali akan karatuna i promise u roomy, rungumeta intisar tayi tacigaba da lallashinta itama tagaji da shirun zee don zee akwae ban daria sosae tanada dadin zama yanzu data maida kanta kamar moron(doluwa) abin nadamunta kullum se tajata suntafi shaqatawa amma duk abanza
.
.
Amarya mardiyya ta tare a gidanta dake NNPC quarters a abuja,komae na gidan yayi kyau fadin haduwarsa ma bata baki ne, daedae zaman mace daya kunsan yanda quarters yake amma kayan gidan ne yafito da tsarin gidan sosae. Kallon mardiyya muqaddas yayi yace"babe yakamata muje katsina gaida su abbuh cikin satin nan kigansu, mardiyya tabata rai itafa ta tsani zuwa gidan iyayen miji balle da bikin bakaramin tsiya a ka kwasa dasu ba, dangin mardiyya iya bariki sun nuna hakan yasa ran ummi baci ita dama kwata kwata batason auren, yaken dole tayi saboda duk irin mallake muq din datayi da anzo maganar iyayensa yake taka mata burki, "kinyi shiru babe"kakalo murmushi tayi cikeda kissa "Allah ya kaimu sae muje friday inyaso ma dawo ranar sunday, ahaka sukayi ta fira sannan mardiyya tafara shafa sa aransa yace hmmm anfara kuma.
Ranar friday da wuri muq yadawo aiki suka kama hanyar katsina ,flight suka bi don haka 40 minute yasada su da garin kt, driver din su ummi muq yakira batareda bata lokaci ba akazo akai picking dinsu, mardiyya se cika take tana batsewa, dakin ummi suka shiga,lokacin ummi na kwance kasan carpet din dakinta tana firfita, saboda zafi, sallama muqaddas yayi ummi ta tashi da fararta tana fadin "oyoyo mutan abuja, zama yayi akasa yayinda mardiyya tazauna kan sofa din dakin ummi tadaura kafa daya kan daya,kafar tasha zobe da anklet, daurin nan takafa na ture kaga tsiya kasancewarta macece me gashi yasaka gashinta fitowa data tufke shi agadon bayanta, ummi ce tagama kare mata kallo aranta tana karajin tsanar mardiyyar, dakyar mardiyya takalli ummi tareda fadin "good afternoon",ummi daranta yabaci tadae daure ta amsa kunya kamar ta hadiye muqaddas,kallon mardiyya yakeyi ta gefen ido yana mata signaling cewa tasauko kasa, lura datayi yana kallonta yasa tayi shuumin murmushi don tasan ta kunno ummi dama burinta ta bakan tamata rae kuma ta bakanta mata, girgiza kafa takeyi irin yanda yan dunia keyi,ummi ta ce muqaddas kaita dakin ammi tagaidata, su nuwaera ne suka shigo gidan lokacin suna jss3 gayda mardiyyar sukayi suna murnar ganin amarya dakyar ta amsa tana cin magani atake sukaji suma tafita ransu barin ma ganin yanda take kada kafa gakuma ummi a kasa, ko yayansu basu gayda ba suka shige ciki don haushi shima yake basu da anty zee ya auro aida baayi haka ba, dakyar yatashi ya kalli mardiyya kitashi muje mugaida ammi, binsa tayi abaya har tana ruko masa hannu cikeda kunya yafisge hannunsa, dakin ammi suka shiga yanda tayi ma ummi haka tayimata kasancewar ammi nada saukin kai ba kamar ummi bane yasata yin murmushi amarya an wuni lafia? Dakyar mardiyya tace lpy, sanan ammi tasa murjana kawo musu abinci dire masu kawae tayi tayi gaba duk kunya tacika shi, ammi ta tashi tabasu wuri ta nufi kitchen kasancewar itace keda girki, da daddare ummi takira muq, ta inda take shiga bata nan take fita ba, yanzu kai fisabilillahi Muqadas irin matar daka zaba ma rayuwarka kenan? Ita kanta tana bukatar amata tarbiyya balle tama yaranka irin surukar daka zaba mana kenan, in kyanta ne ya rude ka gani nakeyi ita kanta zee din daka ki aure kyakyawace, shiru yayi yarasa bakin magna hakuri kawae yake b ma ummi, "ae sae ka tashi ka kwasa gayyarka kuje dakinka don bazae yiwu takwana cikin yarana tabata masu tarbiyya ba, kunma je gayda abbunku? Aa yabata amsa sannan ta umurcesa dasuje sugayda abbu, duk rashin kunyar mardiyya kasa ma abbun tayi don sosae yamata Kwarjini, nasiha yamasu sosae sanan ya sallamesu.
muqaddas ne yayi banza da mardiyya sosae tabata masa rai,be hada komae da iyayensa ba, magna take masa tafara shishigemasa kamar zaa rabasu "ya isa haka babe! Meyasa kikama su ummi haka gaskia inkinaso mu shirya ki dinga mutunta iyayena, cikeda mamakin yanda muq yake ta gasa mata magana tasaki baki, tabdijam lallae tanada babban aiki ta lura su ummin nan sunfara shigan mata hanci da kudundune wlh bazata lamunta ba, dole inyi maganinsu aranta take fadin haka, cikeda iya kissa tafara shafasa tana kuka tana bashi hakuri, nan da nan ya hakura dan dama baya iya nisan fushi da eta.
Har suka tafi mardiyya tana yima su ummi ladabi da biyayya,ummi aranta bata yarda ba ganin take na munafunci ne kawae, bayan komawarsu abuja mardiyya taje wajen bokanta yabata magani yace tazuba masa a ruwan wanka yanda ruwa ke kwaranya daga jikinsa haka zae manta da iyayensa, haka kuwa kayi tundaga nan muq be kara tuna su ummi ba sam ko kira sukayi baya picking seyaji kamar ana kona sa, karshe ma se yasaka su a black list, yazama vawan mardiyya sosae sae yanda taga dama takeyi dashi shine girkinta wanke underwear dinta wanke wanke komae shiyake mata kudinsa kuwa tasan komae saedae ta dauki atm dinsa tayi withdrawing abinda takeso bashi da ikon magana ko kadan.

YOU ARE READING
WACECE ITA??
Spiritualta wayi gari ne da hayhuwar yaron daba tasan wanene ubanshi ba, kwatakwata kwatakwata bata iya tuna ryuwar da tayi abaya, tirkashi littafin wacece ita littafine daya kunshi soyayya, rudani, tashin hankali dakuma tausayi, kubiyoni dan jin wannan kaya...